← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 20 OF 43

Sashe 20

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

plat ne guda biyu a cikin side d'in gefe da gefe sai
Upstairs a tsakiyan su, amma kusan a had'e suke.
shima farfajiyar side d'in lungu da sako kamar rana ko ina hasken wuta wanda ko allurar ka ne ya fad'a kasa zaka ganshi.
tsayu tayi tana tunanin ta ina zata fara.
a hankali ta soma d'aga kafarta tana nufar sakiyan wato kofar parlour'n kasan Upstairs d'in in da take hango window sa a bud'e ga kuma iska na d'aga labulen window.

Tana isa bakin kofar ta gyara rukon tea d'in hannunta, kana tayi knocking d'in kofar.
tad'an tsaya kad'an kana ta kuma yi har sau uku a jere.
a hankali ta kai hannunta kan handle ta murd'a ga mamakin ta sai taga ya bud'e.
numfashi ta sauke a hankali a sannu ta zura kafarta ciki bakin ta d'auke da siriruwar salla.
wani sasanyan kamshi ne yabi hancinta.
ta shaki iskar tare da lumshe idanunta a lokaci guda ta bud'e.

Ido ta shiga rarrabawa cikin had'ad'd'e kuma rantsastsen parlour'n da tsaruwar sa ya kai tsaruwa.
can ta hango sa kwance da baya saman doguwar kujera, ya yi pillow da hannayen sa, idanunsa a kan TV.
a sannu tashiga d'aga kafafun tana takowa cikin parlour.
sanyi da kamshi suna dukan ilahirin jikin ta,
har sikar jikin na na tashi.
yana kwance bai motsaba tamkar bai san da shihowar mutum parlour'n ba.

Ta karaso ta tsaya d'an nesa da shi, cikin siririyar muryarta mai fita da yanayi shagwab'a ta ce
"Wai gashi inji Ammie na."
kamar bazai motsa ba bare ya yi magana, tsawon mintuna biyar tana tsaye, bai kalli in da take ba.
zuwa can ya zare hannunsa guda da yayi pillow da shi, ya yi mata alama da ta miko masa.
a sannu ta d'aga kafarta ta maso inda yake.
a hankali ta kai hannunta d'aya dake rike da ganyen nan ta had'a shi da jikin Mug d'in, ya zamana da ta rike Mug d'in da duka hannayen ta, kana ta miko masa.

Bai rike ba sai zaro d'aya hannunsa da yayi, ya rike Mug d'in da d'aya hannun d'ayan kuma bazato taji ya cafko hannunta mai rike da ganyen.
wani irin waro ido tayi, kirjinta ya buga rass,
ya aje tea'n saman table d'in gabansa,
batayi aune ba taji ya fisgota, ta fad'o kansa.
wani irin d'auke numfashi tayi tare da sakin kara.
hannunta mai ganyen ya kama ya dad'a dunkule shi ya matse da karfi.
kara ta kuma sakewa tana jujjuya fuskarta cikin kirjinsa, jikin ta na b'ari.
ya saki hannun nata tare da ware tafin hannun, ganyen da yake kore ya dawo jajazir, ya ciro shi cikin hannunta ya cusashi ta d'an bakin rigarta ta saman kafad'ar ta kana ya ture ta a jikin sa, ta fad'i tim a kasa.
da sauri ta mike tana wiki-wiki da ido, tare da yarfe hannunta da take jin sa kamar ba nata ba.
ta waiga gefe da gefen ta wayam babu su Chuchu da sukace zasuzo su taimake ta.
ya mai da hannayen sa ya dad'a yin pillow da su,
yana aika mata dugun kallo.
baya ta shiga yi kana
da sauri ta juya cikin sassarfa tana fita daga parlour'n ta jingina jikin garo tana mai da numfashin tsoro.

Sai kuma da sauri ta nufi get har tana had'awa da sassarfa.
a in da ta bar su Chuchu a nan ta same su.
fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka.
"Ya dai Feeryal kin sa masa kuwa?."
suka had'a baki wajen tambayar ta.
narai-narai tayi da ido sai ga guntun hawaye ta d'ago hannunta daya matse shi tana jin sa kamar zai fita, ta ciro ganyen a hannun rigarta ta gefen kafad'ar ta.
da sauri Chulu ta karb'a tana fad'in
"Ya tabbata ke nan shugaba ya yi gaskiya koren yanye ya dawo ja."
a tare suka saki murmushi ita da Chulu.
cikin rashin fahimta take duban su suda zasu nuna damuwar su, ya b'ata musu shirin sai kuma taga suna murna.
murya na rawa ta ce
"Ya gani fa shine ya matse shi a cikin hannuna har sai da ya canza kala, kamar zai b'alla min hannu, shine ina baku zo ba."
Chuchu ta ce
"Wayo yake da shi ya yi saurin ankare wa ne da akwai abu a hannunki duk da baisan mene ne ba,
sai dai daya karanci idanun ki yaga d'aukar fansa cikin sa,
shi yasa ya miki haka,
amma kar ki damu shike nan yanzu dai tun da haka ne ya gane sai a canza tsari."
baki ta cuno ta ce
"Aa ni dai bazan sake ba karya min hannu zaiyi,
ni na barshi da Allah mugu kawai."

Har bakin kofar parlour'n Aunty suka rakata ita ta shiga,
su suka juya domin isar da sakon da suka gani.

Washegari ta karance ranar juma'a

Dubbanin d'arurruwan jama'a ne suka shaida d'aurin auren Abdurrahim da amaryar sa Kuraiba.
auren da ya had'a al'umma daban-daban na kasar nan da ma wajen kasar nan.
biki ya yi biki duk wan da ya ziyarci gidajen bikin nan sai ya jinjina irin bajindar da ake zubawa.
musamman gidan A.A FIYA.
nera takoka a wannan ranar.

Gaggarumin liyafa Mommy ta had'a a babban filin taro da ke cikin birnin Lagos,
inda ta gayyaci manya-manyan mawaka dan su kwankwaje basirar su dan nuna farincikin wannan aure.
da misalin karfe 8 na dare za'a fara gudanar da shagalin,
in da za aje a d'auko amarya awuce da ita can gurin liyafar,
idan aka gama gudanar da shagalin bikin a garzayo da ita gidan angonta.

'Yan uwa da abokan arziki anata shiri domin halartar filin taron.
su Mommy anata shiga da fita na kayayyaki masu tsadar gaske.
ko yanzu ma wani dokakken leshin da akayi mata odan sa daga can ketare ta saka, wan da dashi zata fantama a filin taron.

Umma Karima da kyar ta iya danne damuwar ta ta fito cikin mutane tana dariyar yake, itama ta saka kaya masu tsada, duk da kasan ranta bakin cikin zuwan wannan ranar take.
amma tayi imani da abin da bokan ta ya fad'a mata.
haka ta tausasa Siyama da kamar zatayi hauka sabar kishi, ta yi wanka ta fito.
Aunty ma tayi kwalliyar ta sosai duk wanda yagani sai ya yaba.

Tun da yamma masu kwalli da aka gayyace su suka zo.
suna ta cab'awa
kannen ango kwalliya, zuwa magriba kannen ango sun fita ras, kamar wanda za'aje gasar kyau.
ana isha'i motoci suka fara jidan mutane zuwa filin taro.
su Hajiyan Dubai da wasu 'yan'uwan su Daddy da suka zo daga Yelwan Shendam akayi da su gidan amarya idan suka d'auko ta su wuce da ita filin taron.

Dr Imran ne tsaye a kan sa, yana ta fama da shi ya tashi ya shirya su tafi,
antafi d'aukar amarya bai kamata ace amarya ta isa su basu isa ba, su yakamata su jira zuwan amarya.
ya ce bazaije ba idan yana da karfi yajashi ya kaishi.
ganin da gaske ba zaije ba, yafita yaje sashin Mommy ya sanar mata.
Mommy sun fito da kawayen ta zasu tafi, Imran yake sanar mata da abun da ya ke faruwa.
da kanta taje ta same shi,
ta ce har idan ita ta haife shi to ya tashi ya shirya,
tun bai had'u da mummunar b'acin ranta ba,
ita da tayi zaton ma har ya tafi yana tare da amaryar sa.
badun yaso ba ya tashi ya shirya cikin wasu kaya masu shegen kyau.
suka fito suka nufi filin taron da sauran abokan sa.

Ko da Miemie ta zo suje da Feeryal ai mata kwalliya,
Aunty ta ce ita bazataje gurin bikin ba, su tafi kawai.
Miemie kamar zatayi kuka tayi ta had'a Aunty Allah da annabi.
suna cikin haka Daddy ya shigo ya ce su tafi.
Miemie murna har da dariya
ta janyo Feeryal zuwa sashin Ammah bayan ta kira me kwalliya can.
Miemie sai mita take mata
"Ke wlh Feeryal gaba d'ayan ki sai a hankali,
ki duba kiga kowa ya yi kwalli tun d'azu nake ta kiran ki kizo amiki kikaki zuwa,
gashi har an fara tafi su Ameerah duk sun tafi,
da nima fa na tafi jiran ki nake tayi tun d'azu,
haba dan Allah."
"Ke Ammie na ne fa ta ce bazan je ba, dama ni ma ba wani son zuwa nake ba, ni wlh dama yanzu nayi bacci na, tun da ina off ba salla zanyi ba me zan zauna yi."
hararar ta Miemie tayi, ta ce wa me kwalliyar tayi mata da sauri dan Allah.

Simple makeup akayi mata a hakan ma da kyar ta tsaya dan cewa tayi ita bata so.
mai kwalliyar ta ce ba laifin ta bane ita kanta kwalliya ce, bata bukatar karin kwalliya.
ta saka ashoben ya zauna a jikin ta kamar dan ita aka halittasa
ta d'aura mata d'ankwalin, tare da rataya mata wani d'an siririn gyale.
kana ta bi jikin ta da turare.
Miemie da mai yin kwalliyar duk tsayuwa sukayi suna karewa Feeryal kallo
"Ya ilahi ya lillahi, zan iya rantsuwa tun da nake harkar yiwa mutane kwalliya ban tab'a yiwa wata kwalliya a 1time ta haska tamkar wacce na d'au Three hour ana mata kwalliyar ba,
ba wani fenti nayi miki ba paudar ma sama-sama na goga, ba kwalliyar ce tayi miki kyauba ke ce kikayi wa kwalliyar kyau,
sai kace ke ce amaryar."

Miemie da ta bud'e baki sai yanzu ta rufe
"Idan da amaryar ta sami kyanta ai da ta gode da bamusan in da rawan kanta zai tsaya ba,
yanzu ma yaya,
muje Feeryal nasan yanzu kam kowa ya watse ma saura mu."

Direban Ammah da Miemie ta hanashi d'aukar kowa tace ya jira su ya kaisu, shi ya d'auke su zuwa filin taron........!

Babu editing
Chapter 20 · 0% Book details