← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 23 OF 43

Sashe 23

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Abdurrahim ya tsaida tafiyar da yake a hankali wanda yake jin duk abin da suke fad'a.
Miemie ta juya tana shirin bin bayan Aunty ya ce
"Ke Miemie zo nan."
da sauri ta zo inda yake.
ya tsare ta da ido tare da fad'in
"Ya akayi kun tafi tare ke kika dawo ke kad'ai, wace ce 'yar'uwar amaryar da ta biyo, dama ta santa ne?."
da sauri ta girgiza kai
"Aa bata santa ba a gun bikin muka had'u."
"Baku santa ba ta biyo ta?."
ya jefa mata tambayar yana dad'a tsare ta da ido.
in'ina ta soma da tsoron kar ta karb'i tsarabar bulala ta ce
"Am..im dama...dama muna zaune ne tazo gurin zaman mu ta ce tana son Feeryal da kawa,
bayan antashi kuma mutane suka cika motar mu, shine ta ce Feeryal ta sauko ga mota can suje su shiga, itama nan gidan zatazo dama kawo amarya zasuyi."

Ido ya tsare ta dashi da kyau kamar mai son karantar wani abu.
"Uhum dama ku da wasu kuka je?."
yakuma jefa mata tambayar.
"Aa ni da ita kawai mukaje, mutanen da suka biyo motar mu kuma cewa sukayi motar da suka zo ciki ya tafi."

Kai ya jinjina bai kuma cewa ko mai ba ya nufi side d'in sa ta kofar baya.
ita kuma ta bi bayan Aunty da sauri.

Bai jima da shiga ba ya fito rike da makullin mota.
motar da ya dawo da ita d'azu ya aje ta a babban parking lot ya shige ya yi wa motar key masu gadi suka bud'e masa get ya fi.

Karfe 1 da mintuna 30 ya isa Hall d'in da akayi shagalin bikin nasa.
a wajen get ya faka motar kana ya fito ya yi yi knocking d'in get d'in.
masu gadi suka bud'e karamar kofa.
ganin shine suka ce ya shigo,
hannu suka mika masa suna yi masa ban gajiyar biki.
ba yabo ba fallasa ya amsa su.
d'aya daga cikin su ya washe baki yana cewa
"Ranka shidad'e ya muka gan ka a irin wannan lokacin ko amarya ce tayi mantuwa aka zo d'auka mata."
tsayuwar sa ya gyara ya ce
"No! kowa ya tafi an gama watsewa ko a kwai sauran mutane?."
"Ai ranka shidad'e tun karfe 1 aka gama watsewa babu ko wa a nan."
"Ina ma'aikatan CCTV camera na nan?."

Suka nuna masa da hanu suna cewa gasu ta can.
da d'an sauri ya nufi kofar da aka nuna masa.
ya bubbuga kofar aka bud'e.
mutane uku ne cikin office d'in zaune gaban computer.
ya mika musu hannu yana cewa
"I'm Dr Abdurrahim A.A FIYA."
da sauri suma suka miko masa hannu suna fad'in
"Ango mun gane ka ai daga ta cikin nan muke hango ka, muna taya ka murna."
kai ya jinjina kasa ya ce

"Yauwa d'aukar nan nake son gani a fito min da shi."
"To an gama yellab'oi."

Nan da nan suka kusa cikin na'urar suka soma zakulo duk abin da ya faru a gurin. tun daga soma decoration d'in gurin har zuwa san da aka tashi kowa ya watse.
shiru ya yi idanunsa akan Computer, da alamun nazari yake cikin kwakwalwarsa sai kuma da sauri ya ce
"D'an dawo da baya ka zuko nan."
dai-dai in da ya hango budurwar da ta zo gurin su Feeryal d'in.
ya kuma cewa a koma baya, daga in da ta taso daga gurin zaman ta.
ido ya kurawa mutanen da take tare da su.
da ganin su ba sai an fad'a ba b'ata garin samaruka ne,
sosai ya maida hankalin sa kan wanda yake busa sigari yana yi wa yarinyar nuni da hanu,
in da su Miemie suke.
da sauri ya ce
"Kunna mad'aukin magana, zuko muryar me yake gaya mata!."
"Sir mad'aukin maganar gurin ya d'an sami masala ba'a jin magana ta gurin."
tsayuwar sa ya gyara tare da kalmashe hannayen sa a kirji yana karantar lab'b'ansu tare da fassara kalmomin su cikin kwakwalwa da zuciyar sa.

Zare hannayen sa ya yi a kirji tare da shafa sumar kansa san da yaga, ta iso gurin zaman su,
a takaitaccen lokaci sun saki jiki da ita, har Feeryal tana yi mata murmushi.
ya yi musu alama da hanu suyi gaba, dai-dai san da aka tashi har suka fito gurin mota,
da in da budurwar ta tafi taje ta sami mutanen da tace suje su shiga motar su,
sannan ta wuce gurin samarukan daga nan kuma ta kuma dawowa gurin motar ta fidda
Feeryal daga cikin motar.
suka shiga wata mota, da wad'an nan maza uku da suke tare da yarinyar.
"Oh sheet!."
ya furta tare da naushin iska.
suma ma'aikatan jikin su ya yi sanyi sosai duk da basu san me ke faruwa ba amma sun fahimci shirine na kwamushe.
"Sir kalli nan."
suka fad'a suna nuna masa cikin computer.
da sauri ya sauke idanunsa kan dai-dai in da budurwar ta sauka ta shige wata mota tana yiwa Feeryal bye bye, sukayi gaba.
motar da Feeryal d'in take ciki shima yabi wata hanyar.

Da sauri ya ce
"Bi bayan motar ta ina sukayi!."
"Daga nan ne camera'n mu dake wannan kusurwar ta tsaya."
da sauri ya juya ya fita.
masu gadi suna yi masa sai da safe, hannu kawai ya d'aga mu ya yi waje cikin hanzari ya shige motar sa...

Feeryal na durkushe cikin toilet sai b'ari take da rusar kuka.
shiko sai bubbuga kofar ya ke yana cewa
idan bata bud'e ba idan ya b'alla kofar ya shigo sai ya yi mata kaca-kaca, ba shi kad'ai ba sai ya kira yaransa ma sun yi,
daga nan su jefar da ita a titi.
ganin zata bashi wuya ne har ta fara gajiyar da shi.
ya zaro wayarsa ya daddanna ya kai kunne
"Kuyi sauri ku shigo yarinyar nan zata bani matsala."
yana fad'in haka ya sauke wayar.

Kai ta girgiza murya na rawa kamar tana gaban sa cikin muryar kuka take fad'in
"Ka dubi girman Allah karabu da ni, kar ka cutar da ni kaji tsoron Allah wayyo Ammie na, dan Allah kayi hakuri,
ka barni na tafi kada ku cutar da ni,
na rokeka dan Allah."
ta kuma fashewa da kuka tana dad'a rab'ewa jikin murfin kofar toilet d'in.
bata rufa baki ba mazan nan biyu suka shigo.
ya ce
"Ku b'alla kofar nan ku fito min da ita,
ku baje min ita anan, idan na gama na baku ku karasa."

Wani karfe suka d'auka suka rika dukan kofar da shi..
Wani kyakkyawan bugu sukayi wa kofar sai da ta b'alle.
kara ta saka tana ja da baya cikin matukar tashin hankali.
suka shige toilet d'in suka ciccib'o ta suka fito da ita.
a kan gado suka wurgata.
suka shiga jan kayan jikinta suna yagashi.
wani irin kuka take kamar ranta zai fita.
da sauri ya shiga tub'e kayan jikin sa yana fad'in
"Wannan yarinyar akwai masifar taurin kai, duk yadda za'ayi ku tub'e min ita gaba d'aya ku baje min ita, na nuna mata taurin kai."

Wani irin zabura waziri Kutup ya yi ya zube gaban sarki Matip, ya murza gashin bakin sa fuskar sa tayi tsananin baki sabar b'acin rai.
"Tuba nake ya shugaba na, nakasa jure ganin halin da take ciki ne,
ka gafarce ni akan maganar da zan kuma duk da ka hane ni,
da zaka bani dama da na umurci runduna, mun cinmusu,
ta firgita kwarai da gaske da lamarin su."

Chuchu da Chulu da suke durkushe bisa gwuiwowin su, suna haki cikin sananin tafasar zuciya.
suka ce
"Ba sai an je da runduna ba mu d'in nan kad'ai zamu iya da su ko da sun kai runduna guda ne."
sarki Matip ya girgiza kai yana cewa
"Tabbaci da yakini kariyar da yafi namu yana gare sa,
kafin tabbaci akan koren ganye izuwa ja,
idan ya bari wani abu ya faru da ita to tabbas ya tabbata an sami rud'anin bincike, da kuwa ba zamu yafewa kanmu ba sai mun binciko shi a fad'in duniyar nan,
ku da kanku kuka zo min da amsar koren ganye izuwa ja,
ku d'ora yakini da tabbaci a kansa yana d'aure da nauyin da shi kansa bai san da shi a kansa ba,
shi d'in garkuwa ne a gare ta."
duk sukayi kasa da kawunan su suna d'aukar tabbaci...

Da karfi yaja burki a dai-dai kwanar da yaga motar ta shiga ya kurawa hanyar ido, kana da karfi ya kuma figar motar ya kusa cikin layin.
har ya yi nisa ya kuma juyowa ya rage gudun motar yana son tabbatar wa kansa rubutun da ke jikin sainbot d'in da ya wuce.
Shanawa Hotel.
sunan da ke rubuce a jikin sainbot d'in ke nan.
da sauri ya kashe motar ya fito ya nufi get d'in ya shige cikin hanzari....!

*Naso na baku yafi haka amma ban samu dama ba, sai kuyi maneji da shi, idan bacci bai d'auke ni ba zan iya kara muku abin da ya sauwaka zuwa da safe na baku,
ba alkawari bane idan Allah ya nufe ni banyi bacci ba na ce zan yi* 😂

16
Da karfi ya tura kofar get d'in masu gadin suka mike, suna kokarin dakatar da shi.
idanun sa ya sauka a kan lambar motar da a ka d'auke ta.
cikin karaji ya ce
"Ina suke ta ina sukayi masu wancan motar."
yana maganar yana nufa gurin motar.
masu gadin suka biyo shi suna cewa
"Babu wan da sukazo a motar nan wannan motar kamma tun jiya take nan, ba'a fita da ita ko ina ba."
a zafafe ya bud'e murfin motar tare da zaro wayar sa cikin aljuhu ya kunna torch d'in wayar, yana haska cikin motar.
da sauri
ya mika hanu ya janyo gyalenta da yagani kasan sit ya d'ago yana kare masa kallo.
"An ce maka wannan motar tun jiya take nan, me kake nima cikin sa."
wani irin juyawa ya yi tare da d'auke shi da wani irin gigitaccen marin da sai da ya yi tangad'i ya zube kasa.
da sauri d'ayan ya ja baya jiki na rawa.
cikin fusatacciyar murya mai had'e da tafasar zuciya ya ce
"Idan kuka kuma da katar da ni sai na yanke harshenan ku!."
Chapter 23 · 0% Book details