Sashe 31
Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read
Da misalin karfe goma na dare Daddy na zaune yana dube-dube cikin computer.
Mommy na zaune a gegen sa dan yau ita ce da shi.
da sauri ya kai hannu ya dafe kansa tare da fad'in
"Innalillahi wa innailaihirraji'un."
ya rike kansa da karfe
yana jin wani irin sarawa da kan sa keyi had'e da jiri da gilmawar bakin duhu.
addu'a yarika karantowa duk wacce tazo masa baki.
Mommy ta mike tana masa fifita da fad'in
"Alhaji me ya faru?."
yakai tsawon minti goma a haka da taimakon Allah da addu'a yarikajin sassaucin abin da yake ji.
har ya iya janye hannunsa a kan da yake ji kamar an d'aura masa wani katon abu mai matukar nauyi.
kallon Mommy ya yi dake tsaye tana masa fifita, numfashi ya ja da kyar yana tuna da Fad'imatu'n sa ce da da addu'a zata taimaka masa ba fifita ba.
ido ya rumtse yana jin girman ta cikin zuciyarsa, lallai mace mai ilimi garkuwa ce cikin gida.
Da kyar ya iya mikewa ya dawo bakin gado ya zauna, yana cigaba da ambaton sunan Allah.
har yakai bayan sa ga katifa bai fasa ambaton Allah ba,
yana ji kamar ana kafa masa kusosi cikin sassar jiki musan kansa da yake jin sa kamar zai rabe gida biyu sabar nauyi.
yakai awa guda idanunsa a rumtse bawai ko dun ya yi bacci ba.
Mommy kuwa ganin ya yi suru da addu'o'in da yake a fili, tuni ta d'ale gado tashiga sauke minshari.
sai wajen karfe biyu kafin ya samu bacci marad dad'i ya d'auke shi mai cike da tarin wahala.
kamar yadda ya saba munanan mafarkai masu cike da rud'ani da firgici yanzu ma haka ya soma, sai dai na yau ya girmi na sauran lokutan.
Wasu halittu ne masu ban tsoro suke binsa zasu kamashi abaya gudu yake basa samin nasarar kamashi,
yau kam duk iya gudun sa sai da suka cimmasa.
suka d'ad'd'aure shi da igiyar wuta,
jikin wani katon itaciya wacce kasan ta, rami ce mai zurfin gaske wuta yana ci ba kakkautawa.
ga mashi gami da kifiyoyi a hannunsu suna ihu mai firgitarwa da haniniyar zasu kashe shi.
ga igiyar wutan tana shiga jikinsa tana cin namar jikin sa.
wad'annan dodannin halittun kuwa,
sun d'aga wata kifiyar wuta suna daf da caka masa.
ya zabura tare da yin salati ya mike zaune jiki na kyarma.
ya had'a zufa sharaf hatta tafin kafarsa zufa yake.
hannu ya kai ya dafe kirjin sa da yake ji kamar zasa fito.
kallon gefen sa ya yi yaga Mommy na kwance tana sharar baccin ta.
da kyar ya mike yana jin jiri na d'ibansa ya fad'a bayi ya yi al'wa ya fito.
ya shinfid'a sallaya yasoma gabatar da sallah a daddafe.
har wajen karfe hud'u ya sallame ya kwanta kan sallaya bacci na d'aukar sa yakuma yin wannan mafarkin.
kiran salla ce ta taimake shi wajen farkawa daga mummunar mafarkin nan.
ranar Daddy bai iya fita masallaci ba a gida ya yi salla.
Mommy na idar da sallar ta taja kafarta ta koma side d'in ta, babu gaisuwa bare tambayar sa ya yakwana da jikin nasa.
Daddy na zaune har wani lokaci a kan sallaya dare d'aya ya jijjiga har ya fara fita a hayyacin sa.
ya mike da kyar ya nufi sashin Aunty.
Aunty na zaune parlour tana saurarar karatun alkur'ani a TV ya shigo.
duban sa tayi tana sakar masa murmushi,
shima murmushin karfin hali ya yi mata.
ta ce "Yanzu nake shirin zuwa sashin ka naga har wannan lokacin baka shigo ba, na ce ko lafiya."
murmushin yakuma yi mata yawuce bedroom d'in ta.
ta mike ta biyo bayansa, taga ya haye gado ya kwanta.
rike baki tayi
"Daddy kazo ka kwanta kuma bafa a nan kake ba."
tayi maganar tana karasowa bakin gadon, ta zauna tana dubansa cikin kulawa.
da d'an mamaki ta ware ido a kanshi ganin yadda fuskarsa ta zabge kamar dai mara lafiya.
hannun sa ta ruko tana fad'in
"Ya ya dai Daddy me ke faruwa ne baka da lafiya ne?."
tayi maganar cikin nuna damuwa sosai.
hannunta ya kankame yana gyad'a mata kain.
gaba d'aya ta damu ta ce
"Me ya same ka Daddy ba dai ciwon ka ba, sannu kaji yanzu ina ne ke maka ciwo, Abdurrahim ya sani kuwa? bari na kirashi ya zo ya duba ka."
ido ya rumtse kana ya bud'e ya ce
"Banyi bacci ba jiya Fad'imatu ina jin kirjina da kaina kamar zasu fashe."
"Subhanallahi sannu Daddy, kuma kasha maganin ka kuwa, ko dai kwana biyu baka sha ne? bari na d'auko maka na nan kasha sai na kira Abdurrahim."
ido ya rumtse yana jin yadda kai da kirjin suke masa.
ta mike da sauri taje ta d'auko maganin sa datake ajiyewa a gon ta wanda idan yana gurinta da kanta take basa yake sha.
ta had'o da gorar ruwa tazo ta bashi ya sha.
ta mike tana fad'in
"Bari na d'auko waya nakira Abdurrahim."
ya ce
"Barshi tukunna Fad'imatu idan bai lafa ba zuwa anjima sai a kirashi."
kai ta gyad'a cike da matukar tausaya masa.
ta gyara zamanta gefen sa tana ta yi masa sannu.
ta bud'e tafin hannunta tana karanto addu'o'i ta tofa ta shafa masa a kai d'in zuwa jirjin sa.
a hankali ya lumshe idanunsa yana jin nutsuwa na shigarsa, duk da yana jin ciwon amma yaji matukar jin dad'in nutsuwar da ya samu wanda jiya zuwa yau da safiya bai samu ba.
a hankali a hankali bacci ya tafi da shi.
ganin yasamu bacci Aunty ta tafi kichin domin ta shirya masa abincin da ta san yafi so idan ya tashi ya ci.
ita da Feeryal da Baba Rabi ne a kichin.
Feeryal na taimaka mata da wasu abubuwan in da Baba Rabi kuma ke ta aikin gogewa da wanke duk in da yab'aci da duk abin da akayi amfani da shi aka aje zata d'auka ta wanke ta goge sannan ta maida shi gurin zamansa.
Suna kammalawa Aunty ta d'auko lafiyayyen girkin da tayiwa Daddy,
Feeryal kuma ta d'auko nasu shima kayataccen breakfast da abinda tafi muradi wato cake d'in da ta had'a da kanta, da yoghurt mai sanyi.
ta fito ta haura da shi dinning.
Aunty na shiga ta hango Daddy jikin sa na b'ari ya had'a gumi sharkaf, idanunsa kuma a rufe.
da sauri ta dire tray'n abincin hannunta kasa, da sauri mai kama da gudu ta hayo gadon ta rirrikeshi tana jijjigashi da kiran sunan sa
"Daddy Daddy Daddy!."
da karfi ya ware idanunsa da sukayi mugun ja ya sauke wani nannauyan ajiyan zuciya.
ya kankameta numfashin sa na sama-sama ya ce
"Fad'imatu zasu kashe ni!."
a hargitse Aunty da kwalla ya fara zuba mata ta ce
"Su waye Daddy ina suke!? innalillahi wa innailaihirraji'un."
"Dan Allah Fad'imatu kar ki bari na sake yin bacci, ina kuma yin bacci nasan yanzu kam zasu kashe ni, kirjina da kai na zasu fashe Fad'imatu."
Aunty data shiga mummunar tashin hankali hawaye d'aya na bin d'aya
ta rungume shi tana fad'in
"Bazaka mutuba Daddy bazaka mutu ba."
ta mike da sauri ta fita ta d'au wayarta ta daddanna ta tura kira wa lambar Abdurrahim.
wayar tayi ta ringing bai d'aga ba, takuma mai da kiran shima sai da yakusa yankewa kafin ya d'aga.
murya a hargitse Aunty ta ce
"Abdurrahim kayi sauri kazo ciwon Daddy ya tashi!."
ta kashe wayar da sauri ta koma ciki.
Daddy na zaune dafe da dai-dai kahon zuciyarsa d'aya hannunsa na dafe da kansa sai jan numfashi yake da kyar tamkar zai fita yabar jikin sa.
Ba ayi minti 10 ba Abdurrahim ya shigo rike da jakar kayan aikin sa.
yawuce bedroom d'in Aunty kai tsaye.
ganin halin da Daddy yake ciki sai da ya firgitashi, sai dai bai nuna a zahiriba cikin gaggawa yasoma bashi taimakon gaggawa.
ganin ya had'a allura yana shirin masa, Aunty ta share kwalla cikin raunin murya ta ce
"Abdurrahim bazai sa shi bacci ba dai allurar ko, ya ce baya so ya yi bacci in dai zai sashi bacci kar kayi masa."
"Dole ne sai an masa ana bukatar ya sami bacci yanzu."
Aunty tayi shiru tana kallon Daddy daya lumshe isanunsa ya yin da bakin sa ke motsi da alama addu'a yakeyi.
sai itama ta soma karanto ayoyin Allah cikin ranta.