← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 12 OF 43

Sashe 12

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Mommy ne zaune a bedroom d'in ta rike da waya a kunnen ta, tana fad'in
"Ki bata hakuri Hajiya Luba halin Abdurrahim sai a hankali, ko ni nan hakuri da shi nake dole sai tayi hakuri,
har zuwa san da zata shigo gidan sa bazata tab'a samin yadda take so da shi ba, dan shi wani irin mutum ne baud'ad'd'e,
san da suka kasance a tare ai ita mace ce tasan yadda zata bi ta karkato da hankalin sa gare ta."
Hajiya Luba ta ce
"Amma dai babu dad'i haka ace an bada sadakin ka ko sau d'aya saurayin bai tab'a zuwa ba,
kullum a cikin karya take wa kawayenta baya kasar ne, har wasu sun fara gane wa."
"Karki damu Hajiya Luba ke dai a saka bikin nan kawai daga zaran anyi ba shike nan ba,
bari alhaji ya dawo zan masa maganar ya turo aje a sa rana, ayi bikin nan da wuri kawai, kudai kuci gaba da shiri nima ina kai za'a kawo muku lefe satin aure."
"To yanzu naji batu Hajiya Halima ga d'iyar taki ma wai na bata ku gaisa."
Mommy ta washe baki
"Ah bawa surukar tawa mu gaisa."
Hajiya Luba ta mikawa Kuraiba da ke kwance a jikinta waya tana fad'in
"Ga Mommy'n naku kullum in muna waya kiyi ta ce nabata ku gaisa kamar baki da wayar kiran ta ku gaisa."
Mommy ta yi dariya
"Yar albarka ya kike ya shirye-shirye."
"Lafiya lau Mommy muna kai."
"Yauwa madalla kiyi ta hakuri da Abdurrahim lokaci na zuwa."
"Mommy ko na kirashi baya d'aga wayar."
"Kar ki damu Kuraiba daga zaran kunyi aure duk wannan matsalolin sun kare, kinji ko."
ta ce to.
"Yauwa to sai anjima."
Mommy ta kashe wayar.
Kuraiba ta gyara kwanciyar ta jikin uwar tata.
Hajiya Luba ta ce
"To kinji da kunnen ki Hajiya Halima ba karamin kaunarki take ba,
zaki kuma sami d'anta yadda kike so cikin ruwan sanyi."
"Momma ina son Abdurrahim burina kawai na mallake shi, nadad'e ina mafarkin samin miji kamarshi,
kyakkyawa kakkarfan namiji a tsaye mai kud'i."
Hajiya Luba ta yi dariya tana cewa
"Kud'i kam akwai shi dan kuwa su kud'i gadarsa sukayi, jinin kud'i ne a jikin su yake malala,
kwantar da hankalin ki kamar kin sami Abdurrahim kin gama."
Kuraiba tayi wani murmushi tana hasasho kasantuwar su da shi..

Nan da nan Mommy ta sunduma cikin soma shirin auren Abdurrahim da Kuraiba,
a gefe guda kuwa Umma Karima ma na nata shirin dan kuwa ta lashi takwabi sai kanwarta Siyama ta auri Abdurrahim dan tanan ne kawai zata dad'a samin cikar burin ta.
bokan ta ya bata wasu lakanin suna nan suna ta aikin shaye-shaye da shafe-shafen magani.

Feeryal da Miemie ce zaune a cikin keb'ab'b'en gurin hutawa dake gefe da sashin Ammah, wanda yake a matsayin mallakin sashin,
kamar yadda ko wani sashi na gidan yake da irin gurin.
an zagaye fulawowi kujeru na zagaye a cikin sa gurin hutawa ne na musamman da aka kawata shi da furanni.
Miemie ta bud'e baki da hanci tana kallon Siyama da ta doshi hanyar part d'in Abdurrahim.
ganin yadda tayi da baki Feeryal ta saki murmushi mai sauti tana fad'in
"Meye hakan Miemie?."

Miemie ta yamutsa fuska tare da cewa
"Dubi waccan 'yar wahalar shegiya jibeta ba gaba ba baya ba nono ba d'uwawu,
gatanan tsangargar tana tafiya tana wani karairaya jiki kamar an d'aurawa muciya zane,
me Ya Abdurrahim zaiyi da ita,
shi da ya yi rayuwa cikin turawa da larabawa,
har garama Kuraiba tana da d'an cika ita ma d'in dai ba wani fasalin kirki ne da ita ba,
Mommy ce kawai ta masa dole sai ta had'a shi da 'yar kawar ta,
shiyasa Hajiya ma ta ce yaje can Yelwan Shendam ya nimi mata akwai kyawawan mata a gurin,
Mommy ce ta ki da Yelwa zamuje mu sha biki,
da kinje garin kakanmu kin gani garin fa akwai dad'i."

Da sauri Feeryal ta waiga inda Miemie take nuna mata Siyama,
tana daf da shiga part d'in sa.
hab'a Feeryal ta rike ta ce
"Ke Miemie ki raba ni da niman magana ni dai bani da karfe idan ta jiki sai dai na gudu na barki."
"Wlh wannan had'eta zanye na kalmashe 'yar banza, ai ke kin shiga uku da shegen tsoro ina abin jin tsoro a jikin waccan shamuwar mttss."
taja dogon tsaki.
Feeryal ta girgiza kai tana fad'in
"Ni dai babu ruwa na."
"Dalla ta shi mu je ki rakani na amshi book d'i na gurin Sumayya,
banson kayan haushin nan naki."
Feeryal ta mike tana dariya.

Suka fito daga cikin gurin Miemie tana fad'in
"Book d'in nan shi ke tayani hira da daddare idan bamuyi waya da Murad ba,
Sumayya daga aro ta rike taki bani, kullum sai tace zata kawo min gara naje na amshi kayana,
yau Murad ya yi tafiya book d'in ne zai taya ni hira."
"Wani irin book ne haka, mene ne a cikin sa?."
"Love story ne gobe zan baki ya kwana a gurin ki ko zaki shiga layi, dan naga ke sai an d'auraki a network kafin ki dawo saiti,
jiya ma da wani abokin Ya Faisal ya ganki a sashin Ammah sai da ya tambaye ni ke,
kawai na watsar da lamarin ne dan nasan ke d'in sai a hankali."
baki Feeryal ta tab'e dan tana ganin soyayya duk shirme ne da kuma b'atawa kai lokaci.

Suna shiga cikin side d'in Mommy Feeryal ta tsaya a farfajiya bata yadda ta shiga ciki ba.
ta ce wa Miemie taje ta dawo tana jiran ta dan bata mance gargad'in Mommy kan shigo mata sashin ta ba.

Da sauri Ajmal ya turo karamar kofar da ke jikin get d'in side d'in ya shigo.
Feeryal ta waiga suka had'a ido ya sakar mata murmushi.
itama takaitaccen murmushi ta mayar masa tare da sunkiyar da kanta.
ya karaso in da take yana fad'in
"A'a Feeryal ya kika tsaya a nan baki shiga ba."
"Miemie nake jira ta shiga yanzu zata fito mu tafi."
agogon hannunsa ya duba kana ya dube ta ya ce
"Yauwa dan Allah shiga ki cewa Ameerah wai taje in ji Ya Abdurrahim,
sauri nake yi ana jira na a office."
da sauri ta d'ago suka had'a ido sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta,
jiki a sanyaye ta ja kafarta, da fargabar abin da zai biyo baya idan ta shiga, tana kuma jin nauyin ta ce masa bazata iya shiga ba.

Tayi taku d'aya zuwa uku ya kira sunan ta
"Feeryal."
cak ta ja ta tsaya tare da waigawa bata bari sun had'a ido ba kanta a kasa.
numfashi ya furzar kana ya ce
"Ina so muyi wata magana yaushe kike da lokaci, nazo na same ki a side Aunty."

Shiru tayi tana wasa da bakin gyalen ta.
"Jeki sai na dawo."
ya fad'a tare da juyawa da sauri ya tafi.

Takai minti 5 tsaye a bakin kofar tana tunanin shiga daga bisani ta tura kofar ta shiga da sallama a hankali.
Mommy ce zaune ita kad'ai a parlour tana ganin Feeryal ta ware ido.
"Ke me ya kawo ki nan?."
ta fad'a tana dad'a ware ido a kanta.
Feeryal taja ta tsaya jiki na kyarma.
"Ke kutumar uban ki nace uban me ya kawo ki sashin nan, au anturo ki ki barbad'a wani barbad'en naku ne ko,
zo nan."
Mommy ta fad'a cikin tsawa.
Feeryal ta zabura ta shiga takowa in da take ta tsaya gefen ta.
tsawa takuma buga mata
"Miko min maganin da ta turo ki ki barbad'a min, ki koma ki ce mata malamin ta ya fad'i."
kai Feeryal ta girgiza cike da tsoro ta ce
"Ba.ba..babu komai dama um Ya wannan ne um Ya wannan."
gaba d'aya ta mance sunan shi da taji Ajmal ya fad'a da kuma yadda Miemie take kiran sa da shi. sai fad'in Ya wannan ta ke.
Mommy ta ce
"Da kyau mana bakuyi sammanin asirin ku zai tonu ba, dole ki rika kame-kame, hatsabibiya bakar ashana sai naci uwar ki a nan kafin naje na sami wacce ta turo kin."
"Abdurrahim."
taji an rad'a mata a kunnen ta, ido ta rumtse ta had'iye miyau da kyar, muryar Chuchu tajiyo a kunnen ta tana rad'a mata sunan nashi, kana ta bud'e ido da sauri ta ce
"Ya Abdurrahim ne ya ke kiran Ameerah."
kirji Mommy ta buga ta ce
"Waye yayan naki nashiga uku!
to bari kiji in gaya miki kar ki sake nasake jin kin dangana min d'a da yayanki dan shi ba yayun aljanu bane,
kar ki sake nasake jin kin kira min d'a da yaya shi ba yayanki bane,
kije can ki nimi yayan ki, kul nasake jin kin kira shi da yaya sai na dirza bakinki ya yi jini,
wuce ki bani guri shegiya mayyar aljana."

Su Miemie da suke d'aki da su Ameerah har suna rige-rigen fitowa suga wacce Mommy take wa bala'i.
Miemie ta tsaya sororo tagama mancewa tare suke da ita tana jiranta a waje.
jiki na b'ari Feeryal ta nufi kofa sakamakon kuma buga mata tsawa da Mommy tayi, gaba d'aya ta birkice har tana karo.
Sumayya tayi saurin cewa
"Gurin Miemie kika zo gata nan fa."
bata ko waiga ba tuni tayi waje jiki na rawa Feeryal bakaramin tsoron tsawa da fad'a take ba nan da nan yake birkitata ta fice hayyacin ta.

Ameerah ta buga dogon tsaki
"Mssttt na rantse na tsani yarinyar nan bansan me yasa Daddy yaki koran ta ba."
Chapter 12 · 0% Book details