← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 36 OF 43

Sashe 36

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read

"Daddy Daddy! innalillahi wa innailaihirraji'un Mommy Hajiya kushigo kuga yadda Daddy yake yi Ya Abdurrahimmmm!!.."
Ajmaal ya ke fad'i a gigice ganin yadda jikin Daddy'n ke jijjiga kamar wanda aka jona da wutan lantarki, ya had'a gumi daga kai har tafin kafafun sa.
Da karfi Daddy ya dafe kahon zuciyarsa har lokacin idanunsa a rufe ya kasa farkawa daga baccin da yake,
sai da hasken ya yi nesa da shi kafin ya juya izuwa halittar mutun, yana daf da b'acewa ganin sa sannan ya juyo garesa,
annuri shinfed'e a fuskarta tana murmushi kamar ko da yaushe a cikin rayuwarta.
tayi jifa da hannunta ya isa ga inda Daddy yake.
a take igiyar wutan dake tabaibaye da shi ya b'ab'b'alle ya zube kasa.
wani katon kasko yafashe ya tarwatse.
"FEERYAL!."
Daddy ya ambata cikin baccin amma sai da lab'b'ansa suka motsa.
Hajiya Mommy Aunty har suna rige-rigen shiga sashin Daddy jin kiran da Ajmaal ya ke.
Abdurrahim ya mike tsaye daga sunkuyon da yake rai b'ace.
ya fincikota ya mikar da ita tsaye, ya janyo ta tana tirjewa, ya yi da ita sashin Aunty.
yana zuwa bakin kofar parlour ya turata ciki.
ta zube kasa ta kuma yunkurin tashi.
rai b'ace yasa kafa cikin parlour'n tare da d'auke ta da mari ta kuma komawa tayi flat a kasa.
cikin kakkausar murya ya ce
"Idan kuka kuma fitar da ita da wad'an nan kayan na rantse sai na kashe ku!,
kar ku kawo wa mutane iskancin banza a gida."
jikinta ya sake gaba d'aya, ta ja numfashi mai d'an tsawo kana ta shiga sauke numfashi a hankali a hankali idanunta a lumshe,
sai kawai ta gyara kwanciya taci gaba da baccin ta.
tsaki yaja yana d'auke idanunsa a kanta.
ya juya har yakai bakin kofa sai ya kuma juyowa ya dawo.
hannun rigarsa ya gyara ya sunkuya ya sa hannu ya d'agota cak.
wani irin bugawa kirjinsa ya yi sanda yake had'a ta da jikin sa.
a hankali ya shiga d'aga kafarsa yana nufar bedroom d'in ta da ita.
ajiyan zuciya mai sauti ta sauke,
ta dad'a manna kanta a kirjin sa, tana kara lafewa cikin jikin sa.
hannun guda ta sakalo wuyan shi, d'aya hannun nata kuma ta tura ta bayanshi ta kankame rigarshi ta baya.
da d'an sauri ya kalli fuskarta bacci take da gaske.
yana isa bakin gado ya cirota a jikin sa ya wurgata kan gadon yana gyara zaman rigarshi
baki ta cuno har lau udanunta a lumshe.
cikin siririyar muryarta mai cike da bacci ta ce
"Ammie kaina ciwo."
sai kuma ta gyara kwanciya tayi d'ad'd'aya da kafafun ta, rigarta duk ya tattare ya koma sama gaba d'aya cikin ta yana waje.
da sauri ya yuya yafita yana mai dad'a jan tsaki.
ya janyo mata kofar.
acan wajen sakar gidan ya ga Miemie ya kirata ta karaso in da yake da sauri.
ya ce
"Je ki same ta tana."
yana fad'in haka ya juya ya nufi sashin Daddy.

Yana shiga d'akin Daddy ya ja ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Daddy dake zaune, su Hajiya suna zagaye da shi, kowa bakin sa yakasa rufuwa.
Hajiya na ganin sa ta ce
"Kai abokin turawa kai ma mamaki kake na ganin sa zaune,
yana magana tiryan-tiryan kamar bashi ne ke kwance d'azu shame-shame rai a hannun Allah ba,
har waje na fita duba ka kazo kaga halin da yake ciki amma ban ganka ba,
uban ka yana nan a kwance kai katafi taran aljanu 'yar da ta so kashe mai magani,
ina zaka iya da ita,
irin wannan jifa da tayi da shi Allah kad'ai yasan a wani hali yake ciki yanzu."
Mommy ta harare shi tare da yin kwafa wato bazaiji ya daina taimakon aljanar nan ba.
ya karaso yana cewa
"Ya jiki Daddy."
ya ce "Alhamdulillah Abdurrahim kamar an zare min ciwon haka naji, kirjin ne dai ke min zafi har yanzu."
"Insha'allahu shima zai daina."
bai bar d'akin ba sai da ya bashi wasu allurai da magunguna.

Umma Karima ta rasa ina zata sa kanta, tarika dibi-dibi tayi nan tayi can daga karshe tasa direban ta ya jata zuwa dajin Mali.
tana shiga kogon boka Mali ta ganshi zaune yana ta aikin zuba tsafe-tsafe da surkullensa.
ya d'ago da jajayen manyan idanunsa masu muni cikin murya maraddad'i ya ke fad'in
"Wace ce ita da muka kasa ganin ta a zahiri kamar yadda muke ganin duk wanda muka kira shi cikin wannan kwaryar!?
akwai wani abu a tare da ita mene ne shi,
mene ne shi na kasa ganin shi!!."

Umma Karima ta zabura ta zube gaban sa tana fad'in
"Boka a gafarce ni, wannan yarinyar ta zame min karfen kafa na rasa ta in da zanbi na yakace ta a wannan gida,
duk wani makircin da zan gina mata sai ta sallaka,
yau ana daf da idda cin nasara tafi to tana shirin lalata nasarar,
yanzu haka boka nasashi ya tattaro duka takardun kadarorinshi,
yau nake shirin sashi ya juya sunan ya dawo nawa, da zaran ka bashi maganin cikin kwaryar nan,
shine shegiyar yarinyar nan ta fasa kwaryar,
boka a taimaka a kuma d'aukar wata kwaryar muje a bashi maganin."
boka Mali ya kece da dariya
"Hahahaha kin rigada kin tafka asara, aiki ya wargaje, je ki leka cikin tukunyar tsafi ki gani."
jiki na b'ari Umma Karima ta mike ta je ta leka tukunyar tsafin.
kirji ta buga ta waro ido cikin tukunyar, da kullum ke tafasa yau babu ko alamar d'igon abu a ciki, hasali ma tukunyar a bushe take kamas kamar tun da yake ba a ta ba'a amfani da shi ba.
ta juyo gareshi hankali a mugun ta she ta ce
"Boka babu komai cikin tukunyar ina abun ciki suke?."
"Hahahaha a gidan ki kwarya ta fashe fashewar kwarya kuma yana dai-dai da rasa abun da suke cikin tukunya,
shi kansa tukunyar a fashe yake kece bazaki gani ba,
do le sai kin kuma samo wasu a had'e guri guda masu kwari a saka cikin tukunyar, kafi aikin ki ya farfad'o a ci gaba."
jikin Umma Karima ya tsanan ta rawa murya a daburce ta ke fad'in
"Boka kasan da ya na samo wannan na karshen, shekara nawa nayi ina nema kafin na samu,
daya na samo wannan d'in ma, wannan tsinanniyar yarinyar tayi ajalin abin da na jima ina nima wlh bazan kyale ta ba,
yadda ta rushe min mafarkina sai na hanata ko da dai-dai da rumtsawa ne,
yanzu boka ai ki ya tsaya ke nan?."
"Ai ki ya tsaya da alamun faruwar wani lamari, ki gaggauta nimo lakanin ki a sake gina miki aikin ki."
Umma Karima ta mike a haukace tayi waje tana tsinewa Feeryal..

A b'angaren Dad ba karamin girgiza ya yi da ganin Daddy ya farfado ya dawo hayyacin sa ba.
shi da yake ta kan shirin yadda zaiyi ya kwashi dukiyar sa duka, ya barshi cikin latauci da jinya.
ya ciza yatsa yana buga teburin gaban sa.
"Ban so haka ba amma zamu had'u next time ni zanyi nasara, sai ka d'and'ana bakin cikin da kuka jefani ciki kai da mahaifiyar ku, sai na fanshi dukiyan mahaifina da aka yi rufarufa akace duk mallakin ka ne,
daga karshe na fanshe ran mahaifiyata da taku mahaifiyar."
ya mike ya rufe office d'in sa ya nufo gida.

Gaba d'aya gidan tun daga kan 'yan gida da ma'aikatan gidan kowa murnar samin saukin Daddy ake.
in a ka cire Umma Karima da Dad Mom.
farincikin da Aunty ta ke ciki bazai fad'u ba.
tana nan a nanike da shi.

Kwana uku da farfad'o war Daddy yana zaune a bedroom d'in sa,
gaba d'aya ya nisa cikin tunani tun ranar da ya dawo hayyacin sa, yake ta tunanin mafarke-mafarken da yarikayi abun da yafi tsayuwa masa arai shine hasken da yake zuwa ceton sa.
da maganar da ake masa kan hasken.
da kuma fuskar da ya gani daga karshe,
abun da ya d'au re masa kai.
me yasa ake cewa karya bari ta tsere daga raguwar sa, ta zauna cikin rayuwar sa.
bayan a cikin gidan sa take tamkar d'iyar da ya haifa,
yakan mance da ba shine ya haife ta ba har sai in magoratan gidan sa sun goranta.
wani irin kusanci ne ake nufi daya yawuce wannan,
gashi ana gaya masa zai kuma shiga wani tarkon nan gaba, idan baiyi gaggawar kusanto ta cikin rayuwar sa ba.
sosai kwakwalwarsa ta hargitse da tunani ire-ire.......!

Mommyn Twins ce
Chapter 36 · 0% Book details