← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 24 OF 43

Sashe 24

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read

Da sauri duk sukayi baya har da wan da yake kasa dafe da kuncin sa, da yake jin sa kamar jini na fita sabar azabar marin da ya sha.

Da karfi ya juya yana taka kasa har ana jiyo sautin takun sa, dip-dip-dip!.
yana dad'a damke gyalenta dake hannunsa ya shige cikin hotel d'in.

Direct gurin ma'aikatan hotel d'in ya nufa masu kula da kyamarorin tsaro.
ya ce su binciko masa list d'in wad'an da suke cikin hotel d'in da time d'in da kowa ya zo.
ganin binciken nasu na yi masa nawa ya juya da sauri har yana had'awa da gudu-gudu,
yana bin kofafin room d'in kasa yana kasa kunnen sa.
sai da ya zaga kofofin kusan duka, ya d'aga kafa zai haura stairs, a hankali ya dawo da baya ya juya yana kallon wata kofa dake ta can gefe da stairs d'in.
sai kuma da sauri ya isa kofar room d'in idanunsa a kasa yana kallon abin da ke yashe a kasa dai-dai bakin kofar.
a hankali ya durkusa ya d'auko shi yana juyashi a hannunsa,
ya yin da yashiga hasko yanda ya ganta a gun shagalin bikin su tabbas d'ankwalin ta ne wannan.
bai dawo daga tunanin da yake ba yajiyo ihu cikin d'akin.

Ido ya waro da karfi tare da sakin d'ankwali da gyalen hannunsa kasa.
cikin tsananin tafasar zuciya ya yi wa kofar wani irin naushi d'aya a take ta b'alle.

A razane suka sake ta tare da d'agowa suna duban kofar.
Zazuu da ke kanta yana ta kokarin zare pant d'in ta, su kuma sun rirtike hannayenta sun bankare masa ita a haka ba tare da sun gama cire kayan jikin nata ba.
da sauri ya mike a kanta yana kallonsa, sai kuma ya ce
"Dalla ku bankare min ita kun tsaya kallon sa, idan nayi na gama sai kuyi ku bashi sauran da gani shima a hanu yake,
jira ka more kayan dad'i kaima,
bari na gama na baku sauran."
ya koma yana kokarin bin jikin ta.

Wani irin takowa ya yi tamkar walkiya mai tafiya kan iska.
ya wani kai masa naushi a hanci tare da shako makogwaron sa, da sai da idanunsa suka firfito kamar zasu fad'o kasa.
nan da nan jini yashi tsastsafowa a hancinsa gami da bakin sa.
ya wani irin janyo shi ya had'a sa da jikin garu-bango.
ji kake gomm!
ya saki wani wahalellen kara.
da gudu mutane biyun sukayiyo kansa, dukansu ya had'e su ya shako wuyan su, ya rika had'a su da jikin garu sai da ya yi musu jina-jina kafin ya sake su suka zube kasa suna numfarfashin azaba.
yakuma bin su da naushi dukan su da ogan nasu dake zube kasa yana ganin guri na juya masa.
rai b'ace ya ke fad'in
"Ku ga kunan tantiran 'yan iska ko daga kan yau bazaku sake kokarin yi wa wata fyad'e ba."
sai da yaga basa iya kyakkyawan motsi kafin ya kyale su, yana huci kamar kububuwa.

Feeryal da kyar ta mike a galabaice ta rakub'e gefe tana kankame jikin ta da kare in da suka yayyaga kayan ta, da hannunta.
tana jan shashshekar wahala.
duk fuskanta ya yi ja tsabar kuka.
jikin ta ya yi taya-taya duk in da suka karceta garin kokuwar tub'e ta duk ya yi ja, abin ka da farar mace.

Boturan rigar jikin sa ya b'alle ya zaro rigar a jikin sa ya rage daga shi sai dingilet.
ba tare da ya kalli inda take ba ya wurga mata rigar.
hannu na rawa ta d'au ka idanunta a kansa.
ya bata baya ya zaro wayarsa ya daddanna ya kara a kunnen sa.
a hankali ta saka rigar kan kayan ta da yake a yayyage,
bata saka boturan ba sai ta had'e shi ta rike da hannunta.
wayar sa ce tayi kara ya yi picking call d'in ya kai wayar kunnen sa.
"Room 13."
ya fad'a tare da sauke wayar.
ba'ayi minti uku ba wasu maza uku suka shigo.
ya ce su kwashe su su tafi da su.
suka d'ago su suka kad'aya keyar su sukayi waje da su suka turasu cikin mota sukayi gaba da su.

Ya taka zuwa bakin kofar room d'in ya d'au d'ankwali da gyalen ta ya wurga mata su batare da ya juyo ba ya ce
"Zaki cigaba da zama ne a gun?."
da sauri ta sauko a gadon ta biyo bayan sa tana saka gyalen a kanta ta ruko d'ankwalin a hannu, ka farta ba takalmi,
dan bata ma sann ta ina takalmin nata yake ba.
suna isa bakin get d'in hotel d'in.
ya bi masu gadin da mugun kallo tare da nuna musu yatsa yana girgiza shi alamun gargad'i.
ai da sauri suka sunkuyar da kawunan su.

Ya yi waje ta bisa da sauri.
har in da ya faka motar sa, tsayuwa ya yi jikin motar yana waya.
taja ta tsaya gefe jiki a sanyaye.
wani uban ihu ta saka tayi tsalle ta matsa gefe tana yarfe hannu.
da sauri ya sauke wayar tare da juyowa yana kallon ta.
ta durkushe kasa ta rike kafarta tana fad'in
"Wayyo kafata."
torch in wayarsa ya kunna ya d'an tako gurin.
wata katuwar bakar uwar kunama ya gani,
a dai-dai in da ta d'aga kafar nata.
ya sa kafa ya take ta da takalmin sa ya murkushe.
kana ya juya ya shige mota.
Feeryal na durkushe rike da kafarta da ta ke jin tsananin zafi gami da rad'ad'i da da zugi.
nan da nan kafar ta had'a zufa shatin gurin da kunamar ya d'ane ta ya kunbura ya yi ja.

Hon ya danna yana hango ta ta jikin miron motar.
da kyar ta mike tana jan kafar ta yi kokarin bud'e murfin baya taji sa a rufe. ta dawo gaba ta bud'e ta shiga.
tana zama ya figi motar.

Sai shashshaka take ja da yarfe hannu.
duk AC da ke cikin motar, bai hana gumi tsastsafo mata ba.
ta kasa zama sai juyi take kan sit.
shiko bai ko kalli in da take ba idanunsa a kan titi.
sai da sukayi tafiya mai nisa kafin ya gyara fakin gefen titi.

Ya mika hannu sit d'in baya ya d'auko jaka ya bud'e,
kayayyakin aikin asibiti ne da yawa ciki.
ya bincika ya zaro wasu allurai guda biyu,
ya had'a su a Syringe d'aya kana ya d'an dube ta fuskarsa babu wasa
"Gyara."
ya fad'a a takaice.
sautin kukan ta ta kara, gani allura a hannun sa.
sai ta shiga girgiza kai murya na rawa take fad'in
"Dan Allah kayi hakuri kar ka min."
fuska yakuma gimtsewa ya ce
"Idan baki natsu ba sai na caka miki shi a baki, gyara na ce."
ai da sauri ta kai hannu ta toshe bakin ta, tana binshi da kallon tsoro hawaye na fita a idanunta.
kai ya kawar da ga kallon da take masa.
ya mika hanu yaja rigar sa da yake jikin ta gefe, kana ya d'an ruko gefen rigarta ta baya da zip d'in sa ke bud'e.
b'ari ta soma tana shirin cire hannunta a bakin ta.
"Idan baki tsaya ba irin su goma zan miki ta ko ina."
fuskanta ta kifa jikin glass d'in kofar motar murya na rawa ta ce
"Na tsaya Allah na tsaya."
kara ta kwalla jin ya nitsa mata allurar ta saman pant d'in ta jikin ta na b'ari.
ya zaro allurar yana jan gajeren tsaki.
ya jefar da allurar gefen titi kana ya maida jakar baya, ya gyara zaman sa yaja motar sukayi gaba.

Ta d'ago fuskarta daga jikin glass ya yi dama-dama da hawaye da zufa har da hajina.
mintuna biyar baya ta shiga sauke numfashi da ajiyan zuciya a hankali.
a sannu tarika jin zugin yana raguwa gumin da yake karyo mata ma ya daina.

A bakin get d'in wani ramb'asheshen hotel ya yi hon aka bud'e yasa hancin motar ciki.
yana gyara parking ya wurgo mata handkerchief kan kafarta.
ta d'auka a hankali ta kai shi fuskarta,
wani daddad'an kamshi ya bi hancinta ta share fuskarta.
ya bud'e motar ya fita kana ya zaga gefen da take ya bud'e ya yi mata alama da ta sauka.
a hankali ta zuro kafafunta da babu takalmi, ta fito ya mai da murfin ya rufe.
kana ya juya ya yi gaba ba tare da ya mata magana ba.
ganin haka tayi saurin bin bayan sa.
suna shiga cikin had'ad'd'en hotel d'in aka mika masa key.
ya amsa ya yi gaba takuma biyo sa da sauri, zuwa kofar da taga ya tsaya yana kokarin zura makullin ciki.
yana bud'e wa ya matsa gefe ya yi mata alamar da ta shi.
jiki a sanyaye ta shige, tana shiga ya janyo mata kofar, shi kuma ya juya.

Da sauri ta waigo tana duban kofar ganin ya rufo shi ya juya.
d'an nummafashi ta sauke hankali ta karasa ciki,
ta zauna bakin lafiyayyen gadon room d'in da yake a gyare tsaf.
sai rarraba ido take.

Fitarsa da kamar minti 20 aka turo kofar, da sauri ta d'ago.
shi ta gani rike da laida mai d'an girma a hannunsa, ta sunkiyar da kanta kasa tana wa 'yan yatsun ta.
ya tako zuwa in da take, ya aje laidar a gefen ta kana ya juya yakuma fita yana mai janyo mata kofar.
Chapter 24 · 0% Book details