← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 21 OF 43

Sashe 21

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read

14
Tun da suka doso gurun baka jin ko mai sai sautin tashin kid'a.
motarsu na fakawa Miemie ta fito da sauri tana fad'in
"Feeryal yi sauri ana kan yi ban da mu."
ta zaga ta gefen da take ta ruko hannunta suka nufi cikin Hall d'in.
Feeryal ta rike hannun Miemie gam ganin jama'ar gurin maza da mata gabad'aya ya tada mata hankali.
"Miemie ni kam zan zauna a moto na jira ki idan an tashi ki zo mu tafi, ga mutane fa."
"Dalla muje mutanen cinyeki zasuyi, illa iyaka ki zame musu abin kallo kamar dai yanzu da ido ya bar kan amarya ya dawo kan mu,
ke ki natsu da'alla ki d'aga mana aji, saura ace azo ayi rawa kiki zuwa,
zo muje ta can ga gurin zama."

Da sauri ta d'ago ta hangi ango da amarya Kuraiba sai washe baki take,
angon nata kuwa na zaune fuskarnan tafi ta kullum murtukewa da rashin annuri.
"Ido ta waro ganin in da Miemie take nuna mata,
sai sun tsaga ta sakiyar filin kafin suje gurin.
"Miemie mu zauna ata can mana."
"Ke tacan zamuje so nake a tantance kasa da sakuwa, sakanin kwalliyar mu danasu Ameerah,
duba kika yadda suke kallon mu,
kirika murmushin nan naki abin zai fi bada show,
ki had'a da juya wannan idanun naki, kinayi kina irin wannan tafiyar naki kamar na yanga."
Miemie ta karasa maganar da dariya..
itama dariyar tayi tana zame hannunta daga rukon da ta mata, ta zille tayi d'aya gefen.
dole Miemie ta biyo ta.

Biki ya yi biki mawaka ana ta gwangwaje basira kowa da kalar baje basirar sa da yake,
anyi manni an zubda daloli.
Feeryal sai zuba murmushi take abun ya burge ta ba kad'an ba.

MC ya gayyaci ango da amarya da su fito fili.
tun MC bai rufa baki ba Kuraiba ta mike,
tana yi masa alama da ya taso.
shiko fuska yadad'a had'ewa.
da sauri Mommy ta mike daga gurin zamanta ta je ta ruko hannunsa, bakin ta yakasa rufuwa
"Taso mana Abdurrahim yau fa ranar farinciki ne, taso ka rike amaryar ka ku shiga fili."
badun kar ya dizga Mommy gaban kawayen ta ba, da babu abin da zai sa ya tashi,
karfa-karfan da akayi masa ma na zuwa gurin ya ishe sa.
ya mike ta kamo hannun amaryar ta had'a da nashi, ya zame hannunsa ya rike iya yatsarta d'aya.
a haka suka shiga filin.
wata sassanyar waka aka sakar musu, amarya ta takarkare ta rika tikar rawa,
shiko yana tsaye abin ma haushi ya bashi ganin yadda ta dage take tikar rawa,
sai kuma wani mammannewa take a jikin shi.

Mommy da uwar amarya Hajiya Luba da Hajiyan Dubai da kawayen su suka taso,
suka shiga b'arin kud'i a jikin su.
sai kace ganye suke wasa musu.
sai kirari ake musu, iyayen ango iyayen amarya.
Farida ma ta taso ta bud'e bakin jakanta.

Bayan su Mommy sun koma gurin zaman su, su Amerrah ma suka taso suka shiga wasa 'yan kud'ad'en da suka zo da su a jakarsu.
Miemie ta mike tana fad'in
ai na mance Daddy ya raba mana 50-50k ga naki ma a jakata."
ta ciro d'aurin 'yan d'ari biyar-biyar sabbi tar mika mata d'aya.
"Taso muje muyi masa liki."
tayi maganar tana kokarin roko hannunta.
da sauri yati baya da hannun ta tana cewa
"Aa kyale ni je kiyi masa likin ga nawa ma duk ki had'a kiyi masa likin kawai."
"Ai baki isa ba kowa ya je ya yi masa liki ke ce bazaki je ba,
ai dai zaki je ki taya shi farinciki, Allah sai kin je taso muje."
"Dan Miemie ni ki rabu da ni kije kiyi masa kawai ni bazani ba."

Hannunta ta figa ta janyo ta tana tirjewa Miemie tana cewa fa sai ta je.
d'an karamin bakin ta ta cuno tana bubbuga kafafunta a kasa tare da yarfe hannunta tana cewa
"Ni dai Miemie ki barni ni dai bazan jeba."
a haka ta janyo ta suka shige filin.
wani irin tafi gurin ya kaure da shi ji kake
rap-rap-rap.
da sauri ta tsaida buga kafa da yarfe hannun da take ta d'ago kai da sauri.
taga mawakin yana takowa in da suke ya yin da yake ci gaba da rera salon baitin sa,
Camera ya dawo kan su.
yana zuwa in da suke ya shiga ciro kud'i a aljuhun sa yana lika mata.
aka kuma kaurewa da tafi had'e da hele..
kai ta sunkuyar a hankali ta soma yiwa ango da amarya liki kamar yanda taga Miemie take musu,
amma kanta a sunkuye.
sai shigowa filin ake madadin a yi wa amarya da ango liki sai mata liki ake.
ita dai kanta a sunkuye bata yadda ta d'ago ba, tana ta lika musu kud'in hanun ta.

"Kamar ke ce amaryar sai kike fi dacewa da angon."
da sauri ta waiga bayan ta, wata babbar mace ce tsaye tana mata liki ta baya.
murmushi matar ta sakar mata, itama tayi mata gajeren murmushi.
tana juyo wa idanunta ya yi karaf da nashi.
wani mugun kallo ya wurga mata,
da sauri ta zame jiki ta fice a filin ta koma gurin zaman su.

Amarya Kuraiba ta bita da ido.
wace ce ita daga fitowar ta ta cinye taron ko ita amaryar ba a yi ihun fitowar ta haka ba.
ta had'iye abu mai d'aci a wuyan ta, ta aje tambayar ta cikin ranta sai bayan biki zata bibiyi wace ce ita,
da zata fito filin da aka tanadar domin ta har ta janyo hankalin mutane kanta.
daga an ga 'yar wata kasa sai duk a rud'e.
tayi kwafa a kasan ranta.
ta maida hankalin ta kan angon nata,
ta cigaba da shishigewa jikin sa.

Daga in da Mommy ke zaune take ta aikawa Feeryal harara, wan da ita batama san tayi ba.

Feeryal na zama ta sauke numfashi Allah ya gani ba son shi cikin irin wannan taron take ba.

Bayan ango da amarya sun zauna aka gayyaci kannen ango.
duk yadda Miemie taso ta tashi su shiga fili fir take, haka ta kyale ta ta je suka tika rawar su..

Duk da cikin taro ne bai hanashi busa sigarin sa ba, yana yi yana karkata baki irin na 'yan iska.
cikin muryar 'yan kwaya ya ce
"Kai dubi wata had'ad'd'iya zazzafan kayan dad'i."
"Ai tun d'azu na lura da irin had'iye yawon da kake akanta, kai fa Jazu ba karamin maye bane amma na mata."
wani dariyar rashin mutunci ya ke ce da shi
"Ke Zuly mata abin so ne, wancan yarinyar ta tara kayan dad'i a guraren nan."
dariya tayi tana kallon in da take
"Ba karya kam ta aje komai zam-zam amma nan gani nan bari, sakanin ka da shi kallo daga nesa."
"In dai zaki taimaka min me zai hana bazan samu ba."
"Nawa zaka biya?."
"500k."
"Seriously yanzu nake son jin su a banki na."
"Idan kika gama aikin ki zaki jisu, kin san dai bama haka da ke."
"Baka da matsala."
ta fad'a tana mike wa, ta nufi in da su Feeryal suke zaune.

Kujerar da ke fuskantar Feeryal ta ja ta zauna da murmushi kan fuskarta tana fad'in
"Sannun ku dai sister's to ya bikin?."
"Gashi ana kan yi."
cewar Miemie."
zama budurwar mai suna Zuly ta gyara idanunta a kan Feeryal ta ce
"Tun daga can na ke ta hango ki, na ce yau daren nan tawa ce nayi samuwar kawa,
sunana Zuly."
ta karashe maganar da miko mata hannu.
ido Feeryal ta bita da shi batare da ta miko nata hanun ba, sai murmushin da tayi mata.
Zuly ta dubi Miemie ta marairaice murya.
"Kawar tamu bata magana ne dan Allah kice ta ce min wani abu mana."
Miemie ta tab'e baki
"Da alama dai yanzu ta kurmance."
"Hahaha amma anyi kyakkyar kurma anan to a haka nake son ki da kawa,
kin ga ke ma kin zama kawata tun da ke kawar kawata ce,
ni suna na Zuly ke fa."
maganar ta bawa Feeryal dariya.
tad'an dare.

Hannu Miemie ta mika mata kamar yadda itama ta mata tana cewa
"Ni kuma Miemie ita kuma Feeryal."
"Wow nice names, amma ku kannen ango ne ko naganku da ankon kannen ango?."
Miemie ta ce
"Eh mu kannen sa ne."
sosai ta dage tayi ta zuba musu hira, Miemie uwar 'yan surutu tana taya ta.
har Feeryal tad'an saki jiki tana d'an sa baki cikin hirar.

Karfe 12 dai-dai aka tashi, motoci suka soma jidar mutane suna maida su gida.
tuni ango ya shige nashi motar ya yi gida batare da yajira komai ba,
dan dama ya yi yinkurin tafiya har sau biyu Mommy ce ke hanashi.
aka kwashi amarya da kawayen ta aka tafi da su A.A FIYA STREET.

Su Miemie sukayi waje gurin nasu motar.
har gurin motar Zuly ta biyo su,
suna kokarin shiga mota,
ta ce
"Dan Allah ku d'an jira ni na duba na gani ko motar da nazo ciki ta tafi,
dama kai amarya zanyi sai na biku kawai."
ta juya da sauri suna tsaye suna jiran ta jikin mota.
Chapter 21 · 0% Book details