← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 2 OF 43

Sashe 2

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Tuni gidan ya d'auki labarin aljanu sun tashi a kan Feeryal,yan kai kawo masu yayata batun sunata fad'in karya da gaskiya harda masu cewa Feeryal tsirara tafita, babu komai a jikin ta.
Hankali tashe Ammah da Miemie suka nufi sashin Aunty.
har lokacin Feeryal na kwance flat a tsakiyar parlour Aunty na ta tofa mata addu'o'i, tana yi tana hawaye.
Ammah ta karaso da sauri ta ce
"Kamata mu kaita d'aki Hajiya Fatima."
Aunty ta mike tana share kwalla suka kinkimeta suka shige da ita d'akin ta.
Miemie ta biyo su tana hawaye cike da tausayin Feeryal.
a kan gado suka kwantar da ita.
Ammah ta ja blanket ta rufe ta, tana fad'in
"Sun sauka fa bacci take yi."
Aunty ta gyad'a kai jiki a sanyaye.
Miemie ta zauna kusa da ita tana sharar kwalla.
duk tausayin Feeryal ya cikata.
Ammah tayi ta karfafa Aunty, sai ana kiran sallar magriba kafin ta tafi,
har lokacin kuwa Feeryal bata farkaba.
Miemie kam tananan suna tare da Aunty a d'akin har wajen karfe 10 na dare kafin Feeryal ta farka.
da taimakon su tayi wanka ta sa kaya har ta d'an tab'a abinci.
sai wajen 11 Miemie ta koma sashin su.

Washegari.

Hajiya ce zaune gefenta Abdurrahim ne zaune yana dan kishingid'e idanunsa a lumshe,
tun da ya shigo gaishe ta Hajiya ta tsare shi da batun wai ta sami labarin shi ya tsare Feeryal bayan da kowa ya kasa riketa.
Hajiya ta bubbugashi tana fad'in
"Kai abokin turawa yanaganka haka kamar mara lafiya,
dama ina kai ina fad'a da aljanu bare yarinyar ma da ita kanta aljanace,
salon kaje taro su sushige maka jiki,
waya sani ma ko sun shige ka, ina da wani ajiyayyen hayaki bari na d'auko kayi."
a hankali yabud'e lumsassun idanunsa ya mike zaune yana jan d'an gajeren tsaki,
Hajiya ta ce
"In banda hali irin na Fatima daga isowarka kasar ko hutawa ba'a bari kayi ba a wani had'aka da kama aljana,
in ba mugunta ta so kulla wa ba, bari naje na d'auko hayakin nan nayi maka, haba dan Allah mugunta kiri-kiri mutane sun iya shi,
Allah kad'ai yasan wasu irin aljanu ne suka shiga jikinka."
Hajiya na kokarin mikewa shi ya rigata.
yatashi yasaka takalmansa yyi ficewarsa.
Hajiya tadaga murya tana fad'in
"Kai abokin turawa kaji iya shege ka tsaya ayi maka hayakin a kora maka su, shine zaka tafi,
bari naje na sami Daddy'n ku,
wlh ba'a isa a salwantar min da rayuwar jikana na fari ba, ina dalili ina mafari."

Daf da zai shiga shashinsa saiga kiran mommy yashigo wayarsa,
yajuya yanufi shashinta yana shiga yagaisheta,
ta amsa a dabarbarce tana fad'in
"Abdurrahim ina ce dai lafiya bbu inda kaji ciwo?
meya kaika da fad'a da aljanu alhalin yarinyarma ita kanta aljanace,
to karnasake jin kashiga sabgar yarinyar nan inma mutuwa zatayi ta mutu ba abinda yadameka,
ta fita zata tafi gun danginta aljanu in da ta fito ina ruwan ka da tsare ta,
imma Hajiya Fatima ce ta ce ka tsaro mata ita,
to ban yadda ba kar na sake ji,
dan in ba kasa sani ba ka sani, yarinyar aljana ce d'auko ta tayi a cikin ruwa babu kalar fitinar da bata haifar ba,
da kage ganin ta yanzu haka fitina ta haifo musu a can Abuja gidan iyayen Hajiya Fatima'n,
shine aka dawo da ita nan mu ta karasa mu,
shine suka fara daga kanka,
tun da sunsan kaine magajin gidan,
suke so su san yadda zasuyi su sabautar da rayuwar ka."

Baki yatabe cike da kosawa da maganganunsu shi an dameshi da maganan da bai shafeshiba,
dan kawai ya taro ta sai abi ayi ta damin shi ana cika masa kunne da wasu maganganu,
to meye damuwar sa shi,
imma aljanar ce sai tayi aljanancin ta.
batare da ya ce da ita komai ba yanemi waje yazauna akan kujera.
ya ce "
mommy ina abinchi?."
ta ce
"Ba nasa a Ameerah ta kai maka."
"Babu wani sai wanda masu aiki sukayi?."
dubansa tayi har yanzu dai d'abi'ar sa nanan na kin cin abincin masu aiki,
wannan gadon da ya yi na Daddy da kakan sa yana b'ata mata rai.
ta ce
"Babu duk masu aiki ne suka girka, to wai meye ne abincin masu aikin yake yi,
manyan ma'aikatan hotel kwararru a fannin girki su ke girki a gidan nan,
meye aibun abincin su, acan waye yake maka girki ba mata kake da ita ba ina masu aikin ne."
bai yi magana ba ya mike ya yi waje.

Tun da sassafe Miemie tashigo shashin Aunty a falo ta tadda Aunty tana aiki,
ta gaisheta tana tambayanta yaya feeryal da jiki
Aunty ta ce
"Dasauki tana daki ma tana bacci haryanzu."
Miemie ta ce
"Ammah ta ce na gaishe ki da jikin ta, bari na duba ta."
"To jice da ita jiki da sauki."
ta ce tom.
tashige d'akin Feeryal tasameta tana bacci acikin bargo.
tazauna a gefenta tana kallon kyakkyawan fuskar ta da yi wasai,
a hankali ta ke sauke numfashi.
cike da tausayin ta Miemie ke kallon ta.
takai awa daya da shigowa d'akin kafin Feeryal tafarka.
tamike da murmushi tana fad'in
"Miemie yaushe kikazo?."
"Tun d'azu nazo nashigo kina bacci."
"Shine baki tashe ni ba."
"Uhm-uhm kiyi baccin dai, Ammah tace a bacci akafi samun sauki."
Feeryal ta kuma murmushi tazamo bakin gado tana fad'in
"Kawai naji bani da lafiya bansan me ke dami na ba,
ina dai jin bana jin dad'in jiki na,
bari nayi wanka Miemie, ko zan ji na d'an ware."
tana mikewa da sauri ta koma ta zauna bakin gado tana fad'in
"Wash!."
da sauri Miemie ta ce
"Ya ya dai Feeryal?."
"Ciwo jikina yake min Miemie, gwuiwa ta ciwo yake min,
Miemie ta ce
"Sannu Allah yasauwaka yi wankan muje ki karya." Miemie nazaune hartayi wankan tafito tashirya
cikin dogon rigan material mara nauyi.
suka fito
falo suka tadda Aunty tagama shirya breakfast.
ta had'asu akan dinnig,
suka haye dinning tare sukayi breakfast har da Aunty.

Feeryal sai yamutsa fuska take tana fad'in wash nan d'inta namata ciwo, can na mata ciwo.
Aunty da Miemie sai sannu sukeyi mata,
Aunty ta ce
"Bari nasa a kawo miki magani ko azo amiki allura ne kawai zakifi jin dad'i."
dasauri taware ido cike da jin tsoro tana fad'in
"Ah ah Ammie karkisa ayimin allura abani maganin kawai."
Aunty ta ce shikenan
"Maganin kawai za'a kawo miki."
Aunty takira family doctor d'insu ya kawo mata magani.

Har azahar Miemie sunatare da Feeryal ashashin Aunty.
kafin takoma sashinsu tana shiga taga Faisal zaune Ammah tana d'uma mishi hanunsa da ruwan zafi.
sai wani raki yakeyi yana fad'in
"Ash wlhy Ammah dazafi anya ba tsagewar kashi ba ce kuwa."
Miemie ta karaso tana zauna kusa da su tana leko fuskarsa tana dariya.
"Kai Ya Faisal wlh kana da raki, sai kace kariya kayi, d'an bigewa ne fa."
hararar ta ya yi ya ce
"Ke wlh ni tunani ma nakw kamar kariyar ce, dubi fa hanuna inda ya kumbura."
Ammah ta ce
"Kai da'alla tafi can kariyar ce har zaka iya kwana da ita."
ya ce
"Allah Ammah hannnun nan fa tayi tsami sosai daurewa kawai nake,
wlh wannan bugun badai mutum ba sai dai aljani,
wlh Ammah in kin ga yadda ta wujijjigamu ni da Ajmal da Shamsuddin kyace jarirai ta d'auka tayi jifa da su,
dama Zaraddin kam na kasa shi aka fara bugawa da kasa."

Miemie ta tuntsure da dariya har tana rike ciki cikin muryar dariya take fad'in
"Lallai kunji hannun mazajen aljanu, haba ai wannan abin kunya ne ace dukanku hud'u kun kasa iya rike aljani d'aya, gaskiya kun bada maza."
"Ke dalla tafi can in da Feeryal d'in ce ba mahaukatan aljanun da suka zo kanta ba,
wanda naushi d'aya nayi wa yarinyar can wlh sai ta suma."
"Ba waninnan kun dai kasa."
Miemie ta fad'a tana kuma shekewa da dariya.

Faisal ya kai mata bugu da d'aya hannunsa yana fad'in
"Ke ni sa'an ki ne, mutum uku sakanin mu kafin ke kar kiga basa nan ki d'auka ke kike bina,
Ammah ki gaya mata wlh zan b'alla ta a nan."
Miemie ta mike da gudu tayi kofa tana cigaba da dariyar ta ce
"Bari naje naga su Ya Ajmal da Shamsuddin da Ya Zaraddin ko wani hali suke ciki ko kafarsu ce aka b'alla musu su, Allah ya taimake ku ma da ya turo muku Ya Abdurrahim,
badun haka ba kam sai asibiti."
"Zan rike ki Miemie na rantse sai na fasa miki baki."
tuni tayi waje tana dariya.

Sashin Mom ta nufa ta tadda Zaraddin kwance ga magunguna a gefen sa,
Shamsuddin kuma na zaune.
ta karaso tana kunshe dariyar ta da fad'in
"Sannun ku Ya Zaraddin Ya Shamsuddin ya jikin naku."
Sahla ta yi caraf ta ce
"Ai wlh shegiyar mayyar aljamar nan sai ta bar gidan nan."
Zaraddin ya d'ago da sauri ya ce
"Ina ruwan ki, babu in da zataje tana nan."
baki ta tura tana kunkuni.
shiko ido ya lumshe babu abin da yake masa yawo cikin ido da kwakwalwa sai suffar Feeryal da tattausar jikin ta,
sai wani shigewa cikin kujera yake yana ji kamar tana cikin kijin sa.
Miemie ta fashe da dariya tana fad'in
"Wai Ya Zaraddin duk bugun da kuka sha ne haka kamar fa ko iya tashi baka yi, gadai Ya Shamsuddin shi dai kamar nashi da sauki,
lallai kunji jiki kunji ta maza."
ganin hararar da suke mata tamike ta gudu tayi waje.
ko da taje sashin Mommy bata sami Ajmal ba, Ameerah ta ce mata yafita a mota.
Chapter 2 · 0% Book details