Sashe 37
Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read
25
Umma Karima zaune a parkour'n ta ita da iyalan ta,
abin duniya duk ya taru ya dame ta.
shike nan duk bojet d'in ta ya rushe da yanzu ba wannan maganar akeba, da yanzu bata ma kasar ta milla wata kasar.
tsaki ta ja akararo na sau ba adadi.
Nabila dake danne-danne a wayarta ta d'ago tana fad'in
"Kai wai dama wannan duk gidajen Daddy ne da suke Abuja, ai da ya rasu ni cikin wad'an nan gidagen za'a bani da suke Abujan nan."
Bilkisu Saddiqa Rahma suka d'ago a tare Bilkisu ta ce
"Amma Nabila baki da hankali Nabila yanzu har tunanin Daddy ya mutu dan ki sami gidaje kike,
duk cikin mu babu wan da ya tab'a wannan tunanin sai ke
ai ki gansa a raye yafi miki wad'an nan gidajen."
Nabila ta mike ta nufi bedroom d'in su tana fad'in
"Mutuwa ai wajibi komai daran dad'ewa ai dama zai mutu."
"To sai ki bari lokacin nasa ya yi tukun."
cewar Saddiqa.
Umma Karima ta ce
"Kai dalla ku rabu da ita haka, in da ku d'in ne ma hakan zakuyi idan ya mutu sai kunji kuna son wasu gidajen fiye da wasu,
haba dan Allah ku barni naji da abin da ke damu na."
Rahma ta ce
"Umma ai dai bai mutun ba tukun meye na maganar nata, Umma wai me ke damin ki ne kam?."
Umma Karima ta girgiza kai kawai tana jin kamar ta mutu dan bakinciki.
Siyama ta fito tana gyara mayafi ta dubi Umma Karima tana fad'in
"To Aunty Karima ni bari na fita nayi bako a waje."
Umma Karima ta d'ago ta kalleta sama da kasa wasu d'amammun kaya ne a jikin ta.
ta ce
"Wai ni wane ne kika samu ne me zuwa babu dare babu ranar nan, kuma ya d'auke ki kuna fita?."
fuska ta yamutsa ta ce
"Kawai hirar rage zafi ne kafin wancan ya shigo hanu,
d'an fita zamuyi yanzu zamu dawo."
Umma Karima ta juya kai bata kuma cewa komai ba tacigaba da tunane-tunanen niman mafitan ta...
Aunty ce zaune cikin bedroom d'in ta rike da waya a kunnen suna magana da Hajja Umma.
daga cikin wayar Hajja Umma ta ke fad'in
"Ikon Allah kuma tana bacci tasan wani mai magani ya shigo gidan, kinsan masu jinnu irin haka a kusa basa son marasa gaskiya,
gidan nan naku akwai wani abu ke dai kar ki yada addu'a babu abin da ya fi karfin Allah,
amma yanzu ya jikin Alhajin babu komai dai ko."
"Jikin sa da sauki sosai mafarkan ma duk ya daina, sai dai kirjin da yaje kukan sa dama shi tuntuni Abdurrahim ya d'aura shi a kan magani."
"To Allah ubangiji ya dad'a yaye masa,
dama Abban ku najiran yasa mi lafiya ne,
ya same shi da batun wannan yaro Sadam iyayen sa sun zo nima masa auren Feeryal ya ce sujira yasami uban ta idan sukayi magana ya amince sai ya turo su nan Lagas d'in,
to yaron wai shi a sonshi a had'a auren shi da abokin sa Nasir,
Abban ku ya fad'a musu yanzu zata fara karatu matsalar da aka samu da 'yan tawagar d'aukar amaryar nan ne ya tsaida batun tafiya makarantar ta,
sun ce babu damuwa idan akayi auren sai ta cigaba da karatun ta,
sau biyu fa suna zuwa, ban da shi yaron da yazo yafi a kirga."
Aunty ta ce
"Hajja Umma da wurwuri haka bikin Maryam da saura wata d'aya, a dai bari idan aka yi natan sai ayi na Feeryal d'in daga baya,
ni nafi so Feeryal ta kara girma tafi haka kafin tayi aure."
Hajja Umma ta ce
"Fatima a wannan hali da ake ciki na ko da yaushe samari suna kawo mata hari dan ma Allah yana ketar da ita, ai a aurar da ita shi yafi miki rufin asiri ke kan ki sai kin fi samin kwanciyar hankali,
imma baza'a had'a bikin dana Maryam ba bayan bikin ayi natan kawai ya wuce,
tun da bikin Maryam d'in yazo daf, taje ta cigaba da karatun ta tana da aure ai yafi."
Aunty ta sauke numfashi tabbas idan ta aurar da ita zatafi samin nutsuwa da kwanciyar hankali.
kullum tana cikin fargabar yawan kai mata hari da maza keyi.
ta ce
"To shike nan Hajja Umma zan fara samin Daddy da batun kafin Abban ya kirashi in yaso daga baya iyayen Sadam d'in suzo."
sukayi sallama ta kashe wayar.
Siyama bata dawo gidan ba sai da yamma lis saurayin nata ya dawo da ita.
yana sauke ta a mota Saddiqa na fito wa.
ya zuge glass d'in motar suka had'a ido ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa.
ya leko yana fad'in
"Wannan fa naga kunyi kama da ita."
ya yi maganar yana maida kallon sa kan Siyama.
Siyama tawani narke murya tana yauki ta ce
"Saddiqa wai d'iyar Aunty ta ce, ai dole muyi kama."
Saddiqa ta karaso gurin ta dube shi da murmushi ta na cewa
"Inayini Uncle."
ido d'aya ya kashe mata sannan ya amsa gaisuwar nata.
Siyama ta dube shi tana fad'in
"Baby sai yaushe?."
"In kin so ko anjima da daddare sai na dawo."
"Ah ka bari sai gobe."
"To Allah ya kai mu."
ya dubi Saddiqa ya ce
"To sai anjima 'yanmata."
hannu ta d'aga masa ta ce "Mu kwana lafiya."
ya ja motar sa ya yi gaba, su kuma suka shige ciki Saddiqa tana cewa
"Aunty Simaya a ina kika samo wannan amma fa ya had'u."
Siyama ta washe baki ta ce
"Ba kad'an ba fa bamu jima da had'uwa da shi ba, kinga har maganar aure yake min,
amma duk had'uwar shi ai bai kai yayan ku ba, badun ina da sammanin samun Abdurrahim ba da wannan zan aura."
Saddiqa tayi dariya suna shigewa parlour'n su.
Da daddare Siyama na kwance suna waya da saurayin nata, cikin hirar tasu yake tambayar ta ina mai kama da ita.
ta ce "Tana can d'akin ta."
ya ce "Allah kuna kama fa sosai kyakkyawa kamar ki."
Siyama ta washe baki dajin dad'in an yabe ta an ce mata tana da kyau.
ta ce
"Ai haka kowa yake fad'a muna kama da ita, d'azu ai itama sai da ta tambaye ni wai a ina na samo had'ad'd'en gayen nan."
dariya ya sake yana fad'in
"Au ki ce ita ma ta tambaye ni kamar yadda na tambaye ta yanzu."
"Eh wlh tayi maganar ka d'azu ma, ko na kaimata ku gaisa ne?."
"Aa ki barta dare ya yi kidai bani number ta ma gaisa ko ta Whatsapp ne, mai kama da baby na kyakkyawa."
Siyama tayi dariyar jin dad'i, ta ce
"Tom zan turo maka."
suna gama wayar ta tura mishi lambar Saddiqa.
Koda Aunty ta sami Daddy da batun da Hajja Umma tayi mata kan Major Sadam, yanzu ya matsa yana so inda so shine samu a had'a bikin su dana abokin sa Inspector Nasir.
Daddy ya yi shuru sannan ya ce ace
su dakata tukun ba yanzu ba...
Kullum Umma Karima a cikin tunani take na yadda zata bi ta idda samin nasara a karo na gaba ta ke.
har in tana bukatar samin nasara kuwa ya zama dole Feeryal tabar gidan,
ta nan ne kad'ai idan tayi jifan ta zai fad'o kan wanda take so batare da an tsare shi ba.
sai dai wannan karo tana bukatar taimako dan ta lura a yanzu dole sai ta sami mai tallafa mata kafin ta idda kudirin ta.
da sauri ta mike ta d'au mayafi tayi sashin Mommy.
a parlour ta tadda Mommy ita da su Ameerah.
Mommy na ganin ta tasan wani labarin ta kawo mata, ta jata sukayi cikin d'aki.
a bakin gado duk suka zauna, Mommy ta dubeta ta ce
"Ya dai Hajiya Karima akwai labari ke nan."
Umma Karima ta gyara zama cikin dabara da kwarewa a iya makirci take fad'in
"Yanzu Hajiya Halima haka zamu zuba ido mucigaba da kallon matar nan,
da wannan aljanar ruwan da ta kawo mana ita gida, ta zame mana fitina alakakai,
to bari kiji ina mai maganin da na kawo shi rannan ya duba Alhajin nan,
ya ce yarinyar ba karamar matsafiya bace, aiki tayi da tsafin ta har ta kore shi a gidan,
yanzu haka ya ce idan bamusan yadda mukayi muka fitar da ita a cikin gidan nan ba,to wlh mu sai ta fidda mu kaf a kan 'ya'yan mu."
Mommy ta dafe kirji ta ce
"To yanzu meye mafita Hajiya Karima, wannan hasabibiyar yarinyar ya zamuyi da ita?."
"Mafita d'aya mud'agawa Alhaji hankali mu tada bori cikin gidan nan, mu zuga Hajiya musa ta tasa shi ya kore ta,
in ba haka ba fa ina mai tabbatar miki muzata kora cikin gidan nan,
kuma duk shirin Hajiya Fatima ce makirarriya ta kwantar da kai ta had'a mu da gamasheka, tana sarar mu ta kasa."
Mommy ta ce
"Amma fa Hajiya Karima idan muka ce zamu d'aga hankali da yawa kinsan halin Alhaji karshe ya ce, zamuyi a bakin auren mu,
ni kinsan fa saura biyu ne sakanin mu ya guntule d'ayan tuntuni,
gara ke ma bai tab'a yi mi ko d'aya ba,
ni ina ganin kawai mubi a sannu mu sami Hajiya mu tuna mata ai dama ya ce,
idan aka gama bincike ne akan wanda suka sace ta mai tawagar d'aukar amaryar nan,
zata koma can Abuja, mu tuna mata da wannan batun dan naga kwana biyu tayi shiru, kuma nasan har da ciwon Alhajin ne ma yasa tayin shiru,
tun da ya sami sauki zance ya kare tasashi ya koreta ta koma can in da akayi gayyar ta."
Umma Karima ta d'anyi shiru bataso haka ba, taso Mommy ta d'auki zugarta kamar yanda kullum take sata akan keken b'era.
ta ce "To shikenan hakan ma za'a sami nasara, bari zan sami Hajiyar nasan yadda za'ayi."
nan ta cigaba da kisawa Mommy yadda zasuyi kafin ta koma sashin ta...