← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Daddy ya dubi Umma Karima da take haki d'ankwalin ta a hanu ya girgiza kai,
kana ya gyaza zamansa ya d'aga kafarsa d'aya ya d'aura kan d'aya sannan ya dubi, Abdurrahim dake zaune a gefen sa kasan Carpet ya ce

"Abdurrahim je ka suna fad'a ka rabasu."

"Alhaji ka taso kaje ka ganewa idon ka kasheta fa zatayi."

Daddy ya d'au tsiririn gilashin sa ya saka sannan ya d'au jarida ya bud'e yakuma gyara zamansa yasoma karantawa.
Abdurrahim ya mike ya nufi waje domin isar da umurnin da Daddy ya basa.

Umma Karima ta bi bayan sa da gudu tana cewa
"Yauwa Abdurrahim yi sauri kafin ta kashe ta tun da shi ya ki zuwa bare ya d'au mataki, gata can zata kashe maka kanwa 'yar autarku, mayya ce fa taki sakin ta."
bai kula ta ba yaci gaba da tafiyar sa.

Mommy na baje a kasa tana kururuwa ta kasa ta shi.
Hajiya ta fito kafa ba takalmi,
tana ganin hanun Feeryal a wuyan Ameerah tasa hanu a ka ta kawo ihu ta saka,
"Wayyo Allah zata kashe min jika,
me kuka tsaya yi baku nemo itace kun buga ma 'yar banza ba, ku d'auko itace ku jinke ta da shi,
kuna gani zata kashe ta, wayyo Allah na shiga uku zata kashe min jika."
Hajiya tayi kan Feeryal da duka tana jan rigarta.
"Sake ta bazaki kashe min ita ba gayyan tsiya yau zaman ki ya kare a gidan nan."
bata rufa baki ba ta jita a kasa bip ta ture ta.
Hajiya ta yi kururuwa tana cewa
"Ni Abukabar zai kawo abin da zata kashe ni da jokikina a gidan nan."

Aunty ko hannu bibbiyu ta had'a tana roko da magiya had'i salati.
security kuwa suna ta kokuwan b'anb'are hannun Feeryal a wuyan Ameerah da jikin ta ke b'ari numfashinta na sama-sama.
babu makogoron yin ihu.

Suna ganin sa suka sake ta suna cewa
"Sir akwai matsala fa, ina ga sai an kira liman ya mata rokiyya, mun kasa cire hannunta a wuyanta."
"Abokin turawa ku had'u ku jata ku fidda ita a gidan nan, ku kai ta can cikin ruwa ya tabbata wannan 'ya ba mutum bace,
ina zan iya da gayyar tsiya, bazata kashe ni ta kashe min jikoki ba."
fuska ya dad'a murtukewa tare da gyara tsayuwarsa ya saka hannunsa a kafad'arta ta baya ya fizgota, ya fincikota ta da karfi tayi tangal-tangal ta zube kasa.
Ameerah ma ta fad'i kasa tare da sakin wahallen kara tana dafe wuyanta.

Feeryal tayi wani irin mikewa tare da calla kara tayi kan Ameerah dake kasa tana rike da wuyan ta,
Aunty tayi saurin shiga sakanin su tana fad'in
"Haba ku kuwa bakusan girman Allah da manzon sa bane,
me yasa kuke irin haka."
tuni ta kauce ta gefen Aunty
ta mika hanu tana kokarin kuma shako Ameerah, ya sa mata kafa ta fad'i kasa rip.
ta kuma calla kara ta shiga birgima a kasa tana bige-bige, can kuma ta mike flat gaba d'aya jikin ta ya sake, tashiga mai da numfashi.
Aunty ta yi kanta tana jijjigata da kiran sunan ta.

Da sauri Hajiya tayi kan Ameerah ta rungumo ta tana duba wuyan nata
Mommy ma ta zo ta rungume ta na dudduba jikin ta.
Hajiya ta ce
"Sannu kinji Ameerah Allah ya isa miki sai ta bar gidan nan taje can ta karata, haka kawai so take ta kashe ki kina zaman zaman ki tazo ta same ki ta shakure miki makogoro anya ma ba turo ta akayi ba,
dan ta had'a kai da 'yan ta'adda dama,
to wlh ba a gidan nan ba,
ina ji ina gani bazata kashe min jika ba,
ke Fatima d'auki tsiyar ki kisan yadda dare ya yi muku."
Miemie da tun d'azu take hawaye da sauri ta ce
"Hajiya wlh ba laifin Feeryal ba ce, zamu tafi gyaran gashi ne Ameerah ta tsare mu tarika zagin ta, takuma d'auki kyanwa ta jefa mata a jiki,
kuma tana tsoron mage."
Abdurrahim ya yi tsaki ya juya ya bar gurin.

Mommy ta ce
"To ai dole taji tsoron mage tun da ba gaskiya a lamarin ta, bazan zuba ido a cutar min da 'ya ba sai na d'auki mataki."
"Matakin ke nan yanzu-yanzu ta bar gidan nan."
cewar Umma Karima.
Hajiya ta ce
"Ai dama kam zama ya kare mata a gidan nan dan gobe bamusan wa zata kuma cirewa makogwaro ba,
kuje ku kira min Abubakar, sannu kinji 'yar nan tashi muje zai zo ya same ni."
Hajiya ta d'ago Ameerah da bakin nan nata ya mutu murus, suka tafi sashin ta.
Mommy ma ta koma nata shashin bayan ta gama zazzage bala'i.

Umma Karima ta juya kan Aunty dake ta kokarin ganin Feeryal ta dawo hayyacin ta.
tana ta aika mata habaici.
bata ma san tana yi ba burin ta d'iyarta ta dawo hayyacinta, tana ta tofa mata addu'o'i.
zuwa can ta dawo gayyacin ta,
da taimakon Baba Rabi suka tallafe ta suka tafi da ita side d'in Aunty.

Dole Daddy ya je kiran da Hajiya take ta ai ka masa.
ta in da take shiga batanan take fita ba,
dole Feeryal ta bar gidan.
Daddy ya ce
"Hajiya ai ba laifin yarinyar ba ne idan kika duba Ameerah ita ce me laifi, yau duk Miemie ta fad'a min irin tsokanar da Ameerah take mata kuma bata tab'a ramawa ba,
kuma yau d'in ma ai ba ita ce ta rama ba mutanen kanta ne suka tashi, sakamakon abin da bata so take tsoron sa ta jefa mata mage a jiki,
Hajiya duk ki bar maganar nan sab'ani ne kawai irin na yara, idan aka fiye magana irin haka sai na rikajin ciwo na kamar zai tashi,
yarinyar da ta kusan tafiya ma."

Hajiya ta walalo ido
Daddy ya yi maganar da bata son ji game da lafiyar sa.
"To to ai shike nan amma irin wannan shaka da tayi mata kamar zata kasheta, in yazo da sautsayi ai sai ya tafi da rai,
amma Abubaka kana ma shan maganin ka kuwa,
Kulu kira min Ajimi yaje ya kira min abokin turawa,
yazo ya duba ka imma zai baka wani maganin ne du yazo ya baka, ai yazo da sauki ma tun da yana gidan."
"Hajiya ba damuwa zan je na same shi dan naji kirjin na min zafi."
"Yi maza hanzarta kaje ka same shi, ina amfanin tara mutane a gida hankali na tashi in kaga yaya kaje can Yelwa ka huta ka bar musu gidan."
Daddy ya yi waje.

Hajiya ta dubi Ameerah tana cewa
"Ungo karb'i ki sha ruwan sanyin nan, zakiji wuyan naki ya yi sanyi, ai takusa ta tattari tsiyarta ta tafi kowa ma ya huta."
Ameerah ta karb'i ruwa ta shanye tana maida numfashi.
"Jeki kiyi wanka ki rire wad'annan kayan da sukayi kuran ki sauya wasu,
zan sa abokin turawa ya baki magani."
Ameerah ta mike bakin nan mud'us ta koma sashin su.

Ameerah na zaune a parlour kusa da Mommy tana cin abinci bayan tayi wanka, Ajmal ya shigo ya dube ta yana zama kan kujera ya ce
"Ke Ameerah wai kije in ji Ya Abdurrahim."
baki ta turo sannan ta aje plt d'in abincin ta mike ta fita.

A parlour'n shi ta iske shi zaune ya d'aura kafa kan d'aya.
Laptop na kan cinyarsa yana latsawa.
d'an nesa da shi ta tsaya ta ce
"Gani Ya Abdurrahim."
"Zo nan."
ya fad'a yana nuna gabansa tare da sauke kafafunsa kasa ya aje Laptop d'in saman table, ya gyara zaman sa.
Ameerah ta ja kafa tazo gaban sa, tana waige-waigen ganin ko akwai wanda zai ceceta kusa dan tasan babu tuntub'i sai ta sha dukan da bata san laifin ta ba.
a gaban sa ta sunkuya tana wiki-wiki da ido.
ya d'au belt a gefen sa, tana kokarin gudu ya janyo ta sai da ya yi mata bulala goma kafin ya sake ta,
yana cewa
"Idan kika kuma sa ta sake d'aga mana aljanu a gida, ta tara mana jama'a sai na d'aye miki fata,
Stupid Get out."
Ameerah ta mike da gudu tayi waje tana kuka.

Da kuka ta fad'o parlour'n Mommy da sauri Mommy ta mike tana fad'in
"Kuma tare ki tayi zata kashe ki?."
cikin muryar kuka ta ce
"Ya Abdurrahim ne ya bige ni."
"A wani dalilin laifin me kikayi tun baki dawo daga jinyar da aka d'aura miki d'azu ba."
"Ai tasan laifin ta shegen niman magana ne da yarinyar nan, ina ruwan ta da Feeryal me ta tsare mata a gidan nan,
kullum ke kenan niman tsokana,
ai da fasa miki jiki ya yi sosai ta in da gobe bazaki sake niman wata yarinya da tsokana a gidan nan ba."
cewar Ajmal yana hararar ta.
Mommy ta rike hab'a ta bud'e baki
"Au dama akan ta ne yamiki wannan dukan, bayan kashe ki da ta so yi."
"To Mommy ko ma me ai ita ta jawo."
"To shanyayye ai dama kai da shi kamar wa Hajiya Fatima na haifa mata, duk ta lashe ku ta barbad'a muku magani cikin abinci."
Ajmal ya mike ya fita yana hararar Ameerah........!

12
Tun daga ranar Aunty ta hana Feeryal fita ko nan da can, ko da Miemie ta zo sai dai su karaci hirar su a nan ta tafi.
jin guri shiru hajiya bata kuma cewa ko mai ba, hankalin Aunty yafara kwanciya.

Tuni shirin biki ke dad'a matsowa, uwar ango Mommy da uwar amarya, Hajiya Luba ba zama, ana ta shirin yadda biki zai tafi ta yanda baza a ji kunya gun kawaye ba.
tuni gidan Alhaji Abubakar A.A FIYA yafa d'aukar baki 'yan biki dangi na nesa da na kusa.
Chapter 17 · 0% Book details