Sashe 41
Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read
Umma Karima ta mike cikin d'aga murya take fad'in
"Rabu da shi Hajiya Halima,
sabo da an gama da kai an wanke an baka, waccen tambad'ad'd'iyar tsintacciyar aljanar ruwan,
ganin ta ne ba'ayi ba kawai da daddare kabi ka d'aga hankali ko bacci bakayi ba, alhalin gurin iskancinta ta tafi sai da akaje aka d'auko ta a hotel gurin samarukan iskancinta,
sai 'yar da ka haifa wani ya sace ta yaje ya mata fyad'e kayi ko oho,
to wlh bazan yadda ba 'ya'yana ba tumakai bane da ko wani d'an iska zai rika hawansu ya share lafiya, zakaga abin da zanyi."
ta ja hannun Saddiqa fuuu sukayi sashin Hajiya.
suna shiga ta fashe da kuka tana fad'in
"Yanzu fisabilillahi Hajiya ace ayiwa yarinyar nan fyad'e, Alhaji ya yi ko oho sai kace zuwa da 'yar nayi gidan nan."
Hajiya ta ce
"Ke da'alla dakata Karima ki na nufin ki ce da karfi akayi mata cikin, ba maza tabi tayi yo cikin ta ba."
Umma Karima tashiga rantse-rantse ta na fad'in
"Ga Saddiqa'n ta fad'a da bakin ta ba saceta ya yi yaje yayi mata fyad'e ba."
Saddiqa ta kama gyad'a kai tana fad'in da karfi ya yi mata har da kukan ta.
Hajiya kuwa ta yadda har tana cewa baza'a kyale yaron ba, kuma zatayiwa abokin turawa magana ya zubar da cikin.
Umma Karima ta koma da kwarin gwuiwa ganin hakarta ya cimma ruwa.
Washegari da safe kuwa Abdurrahim ya shigo sashin Hajiya da shirin tafiya asibiti.
Hajiya ta ce
"Yauwa abokin tuwara da ma yanzu nake shirin niman ka, ka d'auki 'yar'uwan ka kuje asibiti ka cire mata cikin nan karya girma ya zame mana abin gori, duk da fyad'e akayi mata amma mutane bazasuyi la'akari da hakan ba,
gara tun wuri a cire shi tun kafin a busa masa rai ayi zunubi."
wani kallo ya wurgawa Hajiya kana ya juya ya soma tafiya yana fad'in
"Ba dai ni ba ba kuma asibiti na ba."
ya fice ya shiga mota ya bar gidan.
Aunty tashigo sashin Umma Karima ta isketa zaune ita kad'ai sai mai aikin ta da take ta mata hidima.
Umma Karima ta bita da kallon mamakin ganin ta yau a sashin ta, wanda tun ranar da aka kawo ta gidan iyayen ta suka kawota sashin Umma Karima tun daga ranar bata tab'a sake taka kafarta cikin sashin nata ba, duk tsawon shekarun nan sai yau.
Aunty ta nimi guri ta zauna kan kujera kana ta dubi mai aikin nata ta ce
"Bamu guri zamuyi magana."
nan da nan ta juya ta bar gurin.
Aunty ta gyara zama ta kalli Umma Karima wanda da dama ita ma ita take kallo,
Aunty ta yi murmushi sannan ta ce
"Hajiya Karima ke nan kina cike da mamakin gani na yau a cikin parlour'n ki zaune a kan kujerar ki ko?
aje wannan mamakin ki fiskance ni, kin san me ya kawo ni nazo ne na tuna miki abin da kika manta,
yau ga miyagun kalamanki sun fad'a kan d'iyar ki, 'yar da kike kira karuwa ita ta iya tsare kanta da taimakon Allah bata aikata abinda kike ta mata fata ba,
sai gashi ke mai tsoron Allah an samo fasa gurbi cikin koyayen ki;
na dad'i ina jiran rana mai kamar tayau sabo da na mai da miki amsar kalaman ki,
amma kash banso ranar ta kasance rana mai muni irin haka ba,
wlh shine Allah nayi bakincikin abin da ya faru, bana farin ciki dan Saddiqa tayi ciki,
sabo da itama 'yata ce tun da d'iyar mijina ne,
amma ina so ki san da cewa
shi Allah sam baya bacci, shi yasa ya nuna miki ishara idan ke mai hankali ce ki gani,
kina da wasu 'ya'yan mata rai uku bayan Saddiqa ga kuma kanwarki cikon na biyar d'in su;
ki kwanta kiyi nazari kiyi amfani da kwakwalwarki,
kiyi kokarin baiwa sauran tarbiyyar da zai sa su kyamaci zina,
idan kuma ke kasashshiyar uwa ce, to ki shiryawa goyon 'ya'yan gaba da fatiha,
ni da FEERYAL kainuwa ne dashen Allah."
Aunty na kaiwa nan ta mike ta nufi kofar fita.
Umma Karima ta mulmulo ashar ta auna tana fad'in
"Karya kike Hajiya Fatima malamin ki ya yi karya, bai isa ya baki sa'an da zaki shigo min har b'angare na ki nimi ki gaya min magana ba,
ni Karima wlh zaki san da ni kikayi, munafukar banza munafukar hofi,
ciki kuwa sai dai ki ganshi akan wancan tsintacciyar aljanar ruwan badai akan 'ya'ya na,
itama Saddiqa'n ma fyad'e aka mata 'yan gulma 'yan bakin ciki, ba cikin shege taje tayi ba,
cikin shege a kanku zai kare."
Aunty tayi waje abinta.
Umma Karima bata fasa kumfar baki ba.
kira ta shiga kwad'awa Saddiqa.
Saddiqa ta fito ta ce
"D'auko mayafinki kizo muje a burge d'an banza, baza'a haifo shi ya zame min masifa alakakai ba,
dama hauka nake na bari a haifo shi."
Saddiqa ta koma ta fito da mayafi.
sukayi waje Umma Karima bata fasa bala'i ba.
Asibitin Dr L'cana suka je ta tura masa kud'i masu yawa, shi kuma ya sunkuya aikin sa.
yayi-yayi cikin ya fita abin mamaki ciki yaki fita,
shi kansa abin ya bashi mamaki duk kwarewa a iya cire ciki irin nashi, sai ga wannan yana son gagarar sa.
kwaya ya cusa mata a gaban ta ya ce suje gida kwayar zaisa cikin yafita dan dole.
tun daga hanya Saddiqa ta fara wash-wash,
Umma Karima ta ce
"Ai dama nakuda zakiyi sai ki daure har ya fita."
abu sai gaba-gaba yake har suka iso gida, Saddiqa ta shige d'aki tayi ta birgima.
kan kace me tafara fita hayyacin ta,
ihun Bilkisu ne yasa Umma Karima tasowa da sauri ta shige d'akin su.
ta tadda Saddiqa a sume, tayi ta yayyafa mata ruwa wai ko dan ta farka ina.
ba sai ga Umma Karima tana salati da kai kawo cikin d'aki.
tayi ta kiran Daddy a waya Daddy bayama gidan yana gun meeting.
ta fita a haukace tayi sashin Hajiya tana ihun fad'in
Saddiqa zata mutu.
suka dawo da Hajiya da ta rud'e ta birkice jikarta zata mutu.
Rahma ce tayi ta kiran Daddy da layin ta kafin ya d'aga ta sa kuka tana fad'in
"Saddiqa zata mutu."
ya ce
"Rahma idan lokacin ta ne ya yi Allah ya yafe mata, dama ai shi mutuwa wajibi ne ga kowa."
ya kashe wayarsa.
Hajiya ta ce wa Nabila da ke kusa da ita
"Kira abokin turawa yazo yanzu kar yarinyar nan ta mutu fa."
Nabila tayi masa missed call biyar ana shida ya d'aga, ta mikawa Hajiya.
a rud'e Hajiya ke fad'in
"Abokin tuwa kazo ka ceci ran kanwarka Saddiqa zata mu."
d'ip ya kashe wayar sa.
Hajiya jin shiru ta ciro wayar baki bud'e.
Bilkisu ce tayi tunanin kiran Family Dr su Allah ya yi taimako ba'a dad'e ba kuwa ya iso."
da kyar ya samo kanta ta farfad'o tana farkawa kuwa sai ga jini ya b'allo mata.
Umma Karima ta sauke wani uban numfashi.
Hajiya ta bud'e baki tana fad'in
"Yoo cikin ne zai b'are dama yake son tafiya da ita, gara ai da ka b'are da ka zauna ka zame mana abin kwatance cikin dangi."
bayan likitan yayi mata duk abin da ya kamata ya tafi, sukuma suka sunkuya gyaran in da jinin ya malala.
Bayan dawowar Daddy da daddare Hajiya ta je da kanta ta sanar masa, cikin ya b'are.
kai ya girgiza kawai dan yasan Umma Karima ce tayi kalan nata, bawai fita ya yi na Allah ba.
Saddiqa wata guda tayi tana jinya zuwa lokacin ta ware ta sami sauki sosai...
Daddy ne yafito daga bedroom d'in Aunty da shirin tayiya office,
Aunty na biye da shi rike da hular sa.
sai da suka zo tsakiyar parlour ya tsaya tare da duban ta.
murmushi tayi masa cikin zolaya ta ce
"Daddy wai kai bazaka tsufa bane kullum fa a haka kake baka kara gaba."
janyo ta ya yi yana kokarin rungume ta tayi saurin gocewa tana dariya da fad'in
"Aa Daddy a nan kuma idan Feeryal ta fito fa."
murmushi ya yi mata ya kalli kofar Feeryal ya ce
"Wannan 'yanmatan taki da alama bacci take har yanzu, a taso ta tayi breakfast."
har ya juya zai tafi sai kuma ya kuma juyo wa murya da alamar shiga yanayin sanyin jiki ya ce
"Fad'imatu idan na dawo akwai wata maganar da nake so muyi da ke,
amma kafin nan zan tinkari Hajiya duk da zuciyana yana bugu da sauri-sauri,
har ina jin yana min zafi, amma zan tinkare ta ahakan duk da bani da tabbacin samin nasara."
Aunty ta dubeshi cikin rauni ta ce
"Daddy mene ne kuma."
murmushi ya yi mata ganin nan da nan ta shiga damuwa ya ce
"Babu ko mai sai na dawo ai nace zamuyi magana ko, kiyi min addu'ar samin nasara, a gurin Hajiya."
kai ta jinjina.
har gurin mota tarakashi sannan ta mika masa hularsa, direba yaja shi zuwa sashin Hajiya......!
Mommyn Twins ce