← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 38 OF 43

Sashe 38

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Shirye-shiryen bikin Maryam da Inspector Nasir yana ta matsowa,
duk abun da aka sawa rana komi daren dad'ewa zai iso.
ana saura sati d'aya bikin Aunty da Feeryal suna zaune a parlour kiran Maryam video call ya shigo wayar Aunty.
Aunty na d'agawa Maryam ta turo baki tana fad'in
"Aunty Faty wai sai yaushe ne zaku zo ne kam, biki saura sati d'aya ai yau ya kamata kuzo."
Aunty ta ce
"To mara kunyar amarya mai kiran a zo bikin ta."
dariya duk sukayi Feeryal na dariya ta ce
"Aunty Maryam an gama d'inkamin ashobe na kuwa?."
"Ke da Sadam yazo ya karb'i naki wai zai kai da kansa a d'inka miki,
jiya ma suna nan yayi ta kiran wayar ki baki d'aga ba."
shiru Feeryal tayi sarai taga kiran shi jiya, bata d'auka ba, yau da safe ma sai da ya mata missed call yakai biyar bata d'aga ba.
maganar Maryam taji tana fad'in
"Ai bakiga d'inkin da yasa akayi miki ba ya nuna min hoton su a waya."
murmushi kawai tayi tana kwantar da kanta a kafad'ar Aunty.
Aunty ta bita da ido tana son karantar yanayin ta.
"Aunty Faty dan Allah ku taso gobe."
Maryam tayi maganar tana marairaice murya.
Aunty ta ce
"Sai ana gobe d'aurin aure zan shigo, ni kad'ai Daddy ya ce zan zo banda Feeryal,
ya ce har yanzu ba'a gama bincike ba,
shigowarta Abuja yana da hasari yanzu."
da sauri Feeryal ta d'ago murya kamar zatayi kuka ta ce
"Ayya Ammie ni dai zanje."
"Aa Feeryal ki bari tukun komai yagama dai-dai ta, idan natafi ana gobe kwana biyu kawai zanyi na dawo."
"Ayya yanzu Aunty Faty banda ita ke nan a zuwa, wlh ni har naji auren ma yafita min a rai."
Maryam ta fad'a kamar itama zatayi kuka.
Aunty ta kashe wayar ganin duk suna son caza mata kwakwalwa.
Feeryal har da kuka ita ala dole sai ta bita.
da kyar Aunty tayi ta rarrashi har sai da Daddy ya shigo ya taya ta.
ya ce tayi hakuri itama zataje saura kiris a kammala bincike...

Ana goge d'aurin auren kuwa, Aunty ta gama shirinta tsaf zatabi jirgin karfe 9 na safiya.
yau Feeryal ko baccin safiya bata koma ba, tana nan tana bori ita sai tabi Ammie'n ta.
tun a daren jiya Miemie tazo ta kwashi wasu kayan ta tana ta murna dan a sashin su zata zauna kafin Aunty ta dawo.
ai kuwa da sassafe ta zo side d'in Aunty.
karfe 8 dai-dai Daddy ya ce Aunty ta fita direba ya kai ta saboda karfe 9 jirginsu zata d'aga.
a tare suka fito Feeryal kayan bacci ne a jikinta ta d'aura hijabi iya gwuiwa a kan kayan baccin, tana tafiya tana sharar kwalla.
Miemie na d'auke da d'an madaidaicin akwatin Aunty.
a can tsakiyar farfajiyar gidan mota ke jiran ta.
Daddy na zaune a bayan motar Abdurrahim na tsaye a jikin kofar gefen da Daddy yake.
tun kafin su karaso direba ya yi saurin bud'e wa Aunty d'aya gefen, suka karaso Aunty na kokarin shiga motar Feeryal ta saki kukan shagwab'a tana bubbuga kafa kasa tare da yarfe hannayen ta,
cikin muryar ta mai sanyi take fad'in
"Ammie ni dai zan biki."
Daddy ya ce
"Aa Feeryal ina mun gama wannan maganar tun jiya,
kiyi hakuri idan komai ya dai-dai zakije ai,
yanzu kam babu halin ki shiga Abuja gaskiya,
kiyi hakuri kinji."
bayan hannun ta takai tana share hawaye tana jan shashsheka, wasu hawayen suna zuba.
Ammah da ta karaso gurin yanzu tayi karamar dariya tana fad'in
"Aa Feeryal wai duk kukan rabuwa da Ammie'n naki ne haka, to ayi hakuri."
Ammah ta dubi Aunty ta ce
"Har kun fito ashe to Allah ya kiyaye hanya, a dawo lafiya."
Aunty ta amsa da amin-amin.
kana Ammah ta d'an rusuna ta gaida Daddy cikin girmamawa.
Aunty ta shige mota tana fad'in
"Yanmatan Ammie kwana uku fa kawai zanyi na dawo, a daina wannan kukan dan Allah."
Feeryal hanci takuma ja tana goge ido da bayan hannu.
direba ya yi wa motar ke Daddy ya dubi Abdurrahim yana cewa
"Ka duba yuwuwar dacewar sayar masa da duka gonakin audugar 30 wad'an da ba'a sasu a jadawalin kai su company ba, na gaya masa kai ba manomi bane likita ne bansan me yasa yake son sako ka cikin lamarin ba,
ko da yake ya ce min wai kafini sanin harkar noma, na ce wane kai tun kan a haife ka nake noma, in ya ce fed'e mutane a d'inke to na yadda."
murmushin gefen baki ya yi tare da rufe masa murfin gefen sa.
Aunty ta gyara zama tana fad'in
"Daddy ka had'a kanka da shi shifa d'an zamani ne."
cikin yin kasa da murya Daddy ya ce
"To bayan ina da ke 'yar zamani ai nima nazama d'an zamanin ke nan."
murmushi ta yi shima ya mayar mata.
kana yacewa direba yaja su tafi, dan shi zai rakata airport d'in da kansa.

Feeryal takuma yin rau-rau da ido sai ga hawaye sharr san da taga motar su Aunty yana shirin fita daga gidan.
Amma ta ce
"Taho muje Feeryal yi hakuri mana kinji, kin san matsalar da yasa baza'aje da ke ba, badun son kare ki daga 'yan ta'addan can ba ai da dake za'aje."
Ammah ta yi gaba.
Miemie ta ruko hannunta ta ce
"Muje Feeryal."
a hankali ta soma d'aga kafarta tana waigen baya in da take hango fitar motar su Aunty.
gajeren tsaki yaja idanunsa a kan waya.
zura wayar dake rike a hannun nasa ya yi cikin aljuhun jallabiyar jikin sa.
kana ya zura hannayensa duka cikin aljuhun,
har suka zo daf da shi zasu gotashi Feeryal bata fasa waigen ba.
ya saka mata kafa ta fad'i tim a kasa.
kara ta sake tare da fad'in
"Wayyo Ammie na, wayyo kafata."
ta rike gwuiwa tana yarfe hannu kwalla na zuba.
da sauri Miemie ta sunkuya tana yi mata sannu dan bata lura da abin da ke faruwa ba.
Ammah ta juyo da sauri ta dawo in da suke tana fad'in
"Sannu Feeryal fad'uwa kikayi ne garin yaya?."
shiko gefe yabi ya wuce cikin garden ya yi zamansa.
Ammah da Miemie suka tallafo ta suwa sashin su tana tafiya tana yarfe hannu...

Kwanan Aunty biyu a ran na uku ta juyo dan hankalin ta na gida gun Feeryal, duk da tasan Ammah zata kula mata da ita.

Siyama ce ta fito daga d'aki ta wuce dinning ta bud'e kular abinci zata d'iba.
da sauri ta toshe hancinta ta juya da gudu ta koma d'aki, ta wuce bayi tashiga kela amai.
Umma Karima da ke zaune a parlour ta bi bayanta da kallo.
zuwa can ta fito tana yamutsa fuska.
Umma Karima ta ce
"Ya dai Siyama me ya faru kamar amai naji kike yi?."
fuska ta dad'a yamusawa ta ce
"Wannan matar Sukai na ce ta dai na cika wad'an na Spices d'in cikin abinci amma bataji ba, wari suke min da zaran na zo ci sai naji zuciya ta na shi."
ido Umma Karima ta ware ta ce
"Siyama kar dai zargina ya kasance gaskiya, gaba d'aya yanayin ki ya koma irin na masu ciki,kwana biyun nan."
kame-kame ta shiga yi tana fad'in
"Ci..ci...ciki kuma Aunty Karima a'a kam ni kam bani da komai."
Umma Karima ta mike zumbur ta ce
"Haba Siyama nasan jiya fa nasan yau, to me zaki b'oye min ma tukun,
wani irin hauka ne ya kaiki barin ciki ya shige ki, wannan d'an iskan dake zuwa babu dare babu narar nan shine ya miki ko?,
na shiga uku ni Karima zaki lika mana abun fad'a."
da sauri ta d'au wayarta ta kira lambar Family Dr su, yana d'agawa ta ce
"Duk abin da kake kabari ka zo, ina niman ka."
ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya wlh bana ma garin nayi tafi sai jibi zan dawo."
Umma Karima ta kashe wayar da sauri bata jira ya gama maganar nashi ba.
ta ce
"D'auko mayafin ki da sauri kizo muje, yau cikin nan bazai kwana a jikin ki ba,
kafin wani ya ankara an cire d'an banza,
ina zan iya ina fama da wani damuwar wani damuwar ya kuma kunno kai,
akwai wani arnen likita gurin shi yanzu zamuje yanzu ba sai anjima ba."
ta shige d'aki da sauri itama ta d'au mayafin ta suka fito.
tun kafin su karaso parking lot take kwad'awa direba kira, ta ce ya taho da makullin mota da sauri.
suka shige mota tayi masa kwatancen asibitin da zai kaisu,
wani private hospital ne.
suna isa ta janyo ta da sauri sukayi cikin asibitin.
bayan an bud'e musu Folder aka turasu ofishin likita.
suna zama Umma Karima ta soma kora masa bayani jiki na rawa, ta ce ko nawa ne ita zata biya bata so cikin ya kwana a jikin ta. ya caja su 500k batare da b'ata lokaci ba tayi masa transfer zuwa account d'in sa.
kud'in suna shigo masa ya mike ya ce yana zuwa.
ya fita.

Abdurrahim na zaune cikin office d'in sa sako ya shigo wayar sa.
ko da ya d'auka ya bud'e, hoton Umma Karima da Siyama ya gani.
yana kokarin aje wayar kira ya shigo.
sunan Dr L-cana ya bayyan a screen d'in wayarsa.
kamar bazai d'aga ba har wayar takusa yankewa kafin ya d'aga.
daga cikin wayar Dr L-cana ya ce
"Hello AA How far, how you are there."
ya ce "Fine."
Dr L-cana cikin harshen sa da bai gama sayawa ba ya ce
"Wannan kamar matar Daddy'n ka ne na gane fuskarta, d'ayan ce dai ban gane ta ba sai dai naga sunyi kama ko daughter ta ce,
abortion suka zo ayi wa yarinyar,
nayi wani tunani nace bari na sanar maka,
kar azo a sami damuwa, shin nayi mata?."
a zafafe ya ce
"Then, So what! meye nawa da zaka kirani kana gaya min, It is not my.concerned, I don't have problem,
damuwar su ce wannan,
so please Don't call me again;
ko ma meye ku kara ta."
ya kashe wayarsa yana jan dogon tsaki.........!

Mommy'n Twins ce
Chapter 38 · 0% Book details