← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 22 OF 43

Sashe 22

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Can ta nufa in da mutane suke tsastsaye da ala ma jiran mota suke.
da sauri ta karaso gurin ta ce
"Sannun ku mota kuke jira?."
suka ce Eh.
ta ce "Ga mota can babu kowa cikin ta, ku karasa mana ku shiga."
ai ko da sauri suka nufi in da ta nuna musu, ita kuma ta yi saurin isa gurin
abokin harkallar ta sukayi magana kana ta juyo da sauri, gurin su Miemie.
mutanen da ta ce misu ga mota can suna zuwa kuwa suka kama d'uruwa cikin mota.
Miemie ta ce
"Aa ya ya haka ya da shiga mana mota?."
suka ce gidan amarya zasu kuma ance musu wannan motar gidan amarya ce.
Feeryal ta ce
"Miemie rabu da su su shiga kamar zai d'au ke mu ai motar."
tun kan ta rufa baki suka shige.
Miemie ta shiga gaba tana cewa
"To ai sai ki zo ki shiga nan mu had'u mu makuru."
tayi maganar tana hura hanci.
murmushi Feeryal tayi ta shiga ta zauna gefen ta tana kokarin rufe murfin motar,
Zuly ta karaso gurin tayi saurin rike murfin
"Ah me zan gani haka wariyar launin fata za'a gwada min, mota ta cika ni ina kasa,
to ai kuwa sai dai ke ki fito, mu nima wata motar,
yauwa gama mota can sauko dan Allah muje mu shiga can, ba girman ku bane zama a matse alhalin daga gidan A.A FIYA kuka fito, yaho muje can motar."
ta janyo hannun Feeryal ta fito ta maida marfin ta rufa tana fad'in
"Allah ya tsare gamu a bayan ku muma sai mun iso."
direba ya ja motar suka fice daga harabar Hall d'in.

"Muje ko ga motar can."
suka jera zuwa gurin motar.
ta bud'e gidan baya,
maza biyu ne a zaune a ciki sai kuma d'aya a mazaunin direba, ta shiga ta masa can ta mannu da mazan sosai, ta ce
"Shigo mu lallab'a, ko kuma kai fita kar mu tseta sosai."
wan da yake jikin kofar ta can ya sauka ya koma gefen mai zaman banza.
kana Feeryal ta shiga jiki a d'an sanyaye dan bata tab'a shiga mota da maza irin haka ba.

Babu wan da ya yi magana a cikin su har suka fice.
sunyi tafiyar da baifi na mintuna biyar ba motar ta tsaya.
na mijin da ke gefen Zuly ya bud'e motar ya fita, itama ta sauka, shi ya dawo cikin motar ya rufe kofar.
ta zago ta gefen da Feeryal ta ke ta d'aga mata hannu
"Bye bye 'yanmata sai mun sake had'uwa."
da sauri Feeryal ta dube ta cikin rashin fahimta.
ita ko ta juya tana cigaba da d'aga mata hanu, ta shige wani motar da yanzu ya karaso gurin.
tana shiga aka figi motar da gudu.
wani irin juyowa tayi jin an......!

15
An wani rungumo ta, ido ta waro cike da matukar tsoro.
ya dad'a wani cacumo ta yana fa d'in
"Wayyo kai kaji jiki kamar auduga,
ja motar nan da sauri mu karasa ko mai zai iya faruwa a nan, nazo har wuya fa."
ya ja motar suka shari wata kwana, tuni cikin ta ya d'ura ruwa sai musu-musu take tana tutture shi.
ta fashe da kuka da ihun niman taimako.
a bakin get d'in wani hotel suka yi hon,
a ka bud'e suka shige ciki.
d'aya na mijin da ke zaune a gaban mota ya miko masa key dai-dai san da suka gyara parking.
ya ce
"Room 13 shine d'akin ku asha dad'i lafiya oga."
wani dariya ya sake hahaha. yana shafa fuskar Feeryal da yayi dama-dama da hawaye.
"Yi shiru mana zazzafa wannan irin kuka haka sai kace yanka ki zanyi, kayan dad'i kawai zan baki, kuma ke zake fad'i farashin ki da kanki, ba kyauta zan more kayan alatun nan ba,
muje ki fad'i nawa zan biya."
ya bud'e motar ya fito kana ya miko mata hannu ya ce
"Zo muje ko 'yammata."
da sauri ta matsa baya tana girgiza kai, hawaye na zuba.
ya mika hanu ya janyo ta ya fito da ita tana tirjewa, had'e da ihu.

Babu kowa harabar hotel d'in guri ya yi shiru, sai masu gadin hotel d'in su biyu.
ihu sosai take tana fad'in a taimake ta.
amma masu gadin sai dariya suke suna fad'in
"Kai Zazuu kabi a hankali fa sabuwar hannu ce wannan da gani."
ganin zata bashi matsal sai kawai ya ciccib'e ta ya yi ciki da ita.
a bakin kofar room 13 ya direta ya rike ta gam da d'aya hannun sa, d'ayan kuma ya zura key'n ya bud'e kofar kana ya tura ta ciki shima ya shige ya zare key'n ya maida shi ta ciki ya kulle kofar.

Sosai Feeryal ke kuka kamar zata shid'e,
ta shiga magiya da rokon sa
"Dan Allah kayi hakuri kar kayi min komai, wlh ni bana son kud'in ka bana so dan Allah dan Allah."
ta kuma rushewa da kuka sosai.

Shiko wani irin murmushi yake sakewa yana tako wa in da take,
baya ta shiga ja tana girgiza kai.
har ta garu da jikin gado,
hankad'a ta ya yi a kan gadon ya hayo kanta, yashiga shafa gefen fuskarta
"Oh zazzafa ki natsu mana, ni fa ba d'an yankan kai bane,
ni kawai mai bada gudumawa ne agaggauce;
baki tab'a sanin dad'in abin bane, ko kin hange sa a wando ne ya tsorata ki,
ki nutsu mu more juna gaskiya zan sha zaki kamar zuma,
ta ina zamu fara ko kin bani zab'i."
yana maganar yana tafiya da hannunsa jikin ta.

Ido ta rumtse da karfi tana bige-bige da shure-shure, had'i da kururuwa, jikin ta na kyarma.
"Ki dai na wannan ihun babu wan da zai jiki a nan, ko an ji ma babu mai zuwa taimakon ki,
ke dai ki baje kawai mu more."
ya mike a jikin ta tare da rungumota ya matseta a jikin sa ya zuge zip d'in rigarta yana kokarin yin kasa da rigar.
kara ta kwalla ta yanka masa cizo a kafad'a.
da sauri ya sake ta yana murza gurin.
ta mike da gudu ta duro a gadon, ta isa bakin kofa tana kokarin murza ki, ya bita ya ruko ta.
ya janyo ta ya kuma tura ta a kan gadon.
ya bita yana kokuwan tub'e rigar jikin ta.
jikin ta na b'ari tarika ture shi tana kuka kamar zata shid'e.
ganin yana daf da cire mata riga, takuma takarkarewa ta yanka masa cizo a kunne.
yana sakin ta ta mike aguje ta shige toilet ta danna kofa ta murza key tana haki.
ta sulale kasa tare da kuma fashewa da kuka, tana toshe bakin ta...

A b'angaren su Miemie kuwa, har sun d'au hanyar A.A FIYA STREET.
d'aya daga cikin matan da suke cikin motar, ta ce da 'yan uwan ta
"Gaskiya fa dare ya yi karfe 12 da wani abu, yaushe har muje gidan amarya mu kuma juyawa gida, dare zai mana sosai,
gaskiya muwuce gida kawai in yaso gobe sai muje,
dan Allah direba ka sauke mu ko a kan titin,
Area-rod ne mu karasa kaga babu masu abin hawan ma."
Miemie ta juya ta kalle ta ta ce
"To ai muma dare zai mana yaushe har muje can."
"Dan Allah kiyi hakuri baiwar Allah tun da motar gida ce zaku koma ai, yanzu mu idan aka sauke mu a nan babu abin hawan da zata kwashe mu,
ki tai maka a sauke mu a can d'in.
Miemie ta yi shiru tana jan kwafa a kasan ranta.
direba ya juya akalar tafiyar ta su izuwa Area-rod.
a bakin titi suka sauke su kafin su suka juyo gida.

Ko da suka iso gida, duk motoci sun dawo har kowa ya shige b'angaren su.
amarya tana side d'in angon ta a b'angare d'aya na cikin side d'in.
a babban parking lot ya gyara fakin ta fito.
ta nufi sashin su.
tun daga nesa ta hango Abdurrahim tsaye cikin lambon gefen sashin hajiya.
yana sanye da wando 3qtr da singilet, hannunsa d'aya ya zura cikin aljuhun wandon d'aya hannun nasa kuma yana rike da mug, yana d'an kurb'ar Coffee.
a hankali ta karaso batayi sammanin zai tare ta ya tambaye ta ina ta fito ba dan yasan daga gun bikin sa suke,
sai kuma ta ji akasin haka.
"Ina kika tsaya sai yanzu kika dawo, ina sauran suke."
da sauri ta ce
"Wasu 'yan uwan amarya ne suka bi motar mu muka sauke su a unguwar su,
su Ameerah kuma sun riga mu dawowa ma."
"Kowa ya dawo ke kad'ai ce a waje?."
kai ta gyad'a ta ce "Eh."
kai ya jinjina tare da kai mug d'in bakin sa yad'an kurb'a.
sannan ya juya a hankali.

Har itama zata juya ta jiyo maganar Aunty.

"Miemie har kun bani tsoro ina kuka tsaya ne, har sai yanzu kuka dawo, ina Feeryal d'in take?, kowa ya dawo gida ku kuna waje."
Miemie ta ce
"Feeryal kuma ai tun d'azu ta dawo motar su ma ya riga namu dawowa, dan mu sai da muka biya muka sauke mutane kafin muka juyo gida."
"To ina ta shiga ke nan ban ganta ba, dan tun d'azu nake zaune a parlour ina zaman jiran dawowar ku, a wata motar ce ta dawo?."
Miemie ta ce
"A motar 'yan'uwan amarya, motar mu data cika ne wata 'yar'uwar amarya ta ce tazo su shiga motar,
mun rigasu tashi kam amma nasan dole zasu rigamu isowa dan mu sai da mukaje Area-rod kafin muka juyo gida."
da sauri Aunty ta juya tana fad'in
"To ko tazo ta shige d'aki ne san da na tashi a parlor'n banga shigar ta ba.
Chapter 22 · 0% Book details