← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

23
"Nayi maka magana kan harka da yaron nan baka dai na ba ko."
ya yi maganar yana dad'a tamke fuskarsa. Zaraddin yakuma sosa keya yana fad'in
"I'm sorry bro."
kai ya jinjina
ya wuce kan keken sa zuwa b'angarensa.

A parlour su Feeryal suka tsaya sabo da wasu 'yan'uwan Daddy dake tare da shi a bedroom d'in shi.
sun b'ata lokaci kafin suka fito, nan suka sami damar shiga duba shi.
jiki a sanyaye Feeryal take gaida Daddy ganin jikin nashi sosai ne.
murmushi ya yi mata yana amsawa da kai.
Aunty na d'akin tana ta faman gyara in da aka b'ata, Umma Karima ta shigo tabi Feeryal da kallon banzan.
tana cewa
"Tun da anyi gaisuwar sai a tashi aje ba zama ake yi ba, ya kamata ma fa a hana masu shigowa gaisuwar nan haka bamusan da me ake shigowa ba,
ba 'yan waje kad'ai za'a hana su shiga ba har da wanda suke gidan,
ana jinya amma kullum ciwo gaba ya ke,
waya sani ma ko ana tufka wasu na warwara ne."
Aunty ta ce
"Idan ma tufkar ake daga gefe ana warwara insha'allah Daddy zai sami lafiya, kullum fatan sauki muke nima masa."
Umma Karima tabi Aunty da kallon banza tana cika tana batsewa ta isa ta hakimce kan kujera.
tana fad'in
"Magana nake kan b'aren da suke cikin gida masu shigowa kan sa, bamu yadda ba idan ba na jikin sa jinin sa ba babu mai kuma zuwa duba shi, za kuma ayi Meeting akan haka."
Aunty tayi kamar bata jita ba dan tasan niman magana take ita kuma bazata biye mata ba damuwar ciwon Daddy ma kad'ai ya ishe ta.
Miemie ta janyo hannun Feeryal sukayi waje.
a bakin kofar parlour'n Daddy ta tsaya tana fad'in
"Wlh matar nan nakusa na tsaya na wanke ta daga sama har kasa,
rashin mutuncinta karuwa yake dad'ayi."
Feeryal tayi murmushi bata ce komai ba dan tasan da ita Umma Karima take.
Kuraiba suka hango tana zuwa, wasu masassun kaya ne a jikin ta, sai wani d'an misitsin gyale data rataye shi a gefen kafad'ar ta.
da wani takalmi mai tsinin gaske a kafarta,
ta toshe ido da bakin glass tana taunar cingam.
"Um kaga amarya ansha gayu wane za'aje club, kuma wai an zo gaida siriki ke nan."
cewar Miemie tana mara baki.
Feeryal ta kalli Kuraiba sannan ta maida kallonta ga Miemie ta ce
"Ai kuwa tayi kyau."
da sauri Miemie ta ce
"Dalla ina wani kyau anan tana tafiya kamar agwagwa, ni har tama ban haushi."
"Ke Miemie Allah ba ruwana taho mu tafi."
Feeryal ta ruko hannun Miemie tana kokarin janta dai-dai san Kuraiba take karasowa kofar parlour'n.
yatsa ta saka ta d'an ture glass d'in idon ta sama, tana wani taunar cingam yana kas-kas.
ta bisu da wani kallon rashin daraja sannan ta ce
"Ku ta ina kukaga mijin Kuraiba ya shige?."
Miemie ta mayar mata da irin kallon da ta musu sannan ta ce
"Waye kenan me irin wannan sunan sai dai ki shiga ciki ki tambaya."
mai da gilashin tayi ta gyara zaman sa a idon ta, ta buga cingam d'in ya bada kara kass.
har sai da hankalin mutanen dake cikin parlour'n ya dawo gurin su, kana tayi musu kallon sama da kasa tacikin glass, sannan ta sa kai ta shige ciki.
da sauri Feeryal ta ce
"Miemie ba sunan ta ba ke nan Kuraiba? to ai mijin ta ke nan ta ke nufi."
"Na gane sarai 'yar rainin hankali mu zata gwadawa iyayi, wai wani mijin Kuraiba to ai ko bata fad'a ba ai ansan mijin ta ne, ni bana son mutum mai iyayi irin haka, ita gatanan me miji,
ai sarai naga shigowar Ya Abdurrahim d'in ta can kofar ba gashi can ba tsaye da uncle Bashir,
dubi yadda ta nufe su ni fa haushi ma tafara bani, ni na tsani macen da batasan kanta ba,
dan kayi karatu a kasar waje sai ka zamo mara jan aji a matsayin ka na mace, komai ka nuna wayewa kawai,
ai badun ciwon Daddy ba muma da last year zamu bar kasar, amma wlh sai dai ma na rike kaina narika jin kaina a big girl,
ni zo mu tafi ma dan Allah naje naji muryar Murad d'ina zuciya ta tayi sanyi."
ta janyo feeryal suka fice.

Zaraddin ya shigo parkour'n Mom
tana zaune ita da Shamsuddin.
Mom ta bishi da kallo har
ya zauna.
ya kalle ta yana shirin yin magana Mom ta ce
"Ya akayi ne Zaraddin?."
ya ce "Mom aure nake so."
cikin farinciki da jin dad'in fitar kalmar aure daga bakin sa ta ce
"Kai nagode Allah shike nan kayi auren ma ka huta da bakin mutane, sai su karaci mugun bakin su ta wani gurin, ka sami matar auren ce, wace yarinya ce wane ne uban ta a garin nan? ai kuwa ko wata baza'a kai ba zayi auren nan."
Mom gaba d'aya farinciki ya lullub'e ta Zaraddin d'an gaban goshin ta da kansa ya ce yana son aure yau, wan da tuntuni Dad ya ce ya fidda mata ya yi aure maganganun mutane sun dame sa a kan halinsa.
ya ce shi bai ga matar aure ba. ya ce
"Mom a cikin gidan nan take kuyi-kuyi magana kawai ku aura min ita,
yanzu nake son a aure min ita,
idan ba'a aura min ita bafa za'a sami matsala."
Shamsuddi ya dube sa yana fad'in
"Yanzu kai Daddy na kwance ba lafiya kake maganar kana son aure yanzu-yanzu da wurwuri,
ta ya za'ayi aure a gidan nan yanzu Daddy yana kwance ba yi da lafiya,
ka daiyi tunani ka bari idan ya sami sauki koma meye sai ayi."
Zaraddin ya harare sa ya na cewa
"Sai me ciwon nasa zai hana a d'aura aure ne, abun da za'a tara mutane kawai a shaida shine me."
Shamsuddin ya girgiza kai tare da fad'in
"Allah ya baka sa'a."
Mom ta ce
"Uhum yanzu kayi magana dan wani ba lafiya in dai ba ango ko amaryar bace ai ba wani abin tashin hankali bane,
bari Dad d'in ku ya shigo muyi maganar, a saida rana karshen wata ayi biki,
wace ce cikin su Bilkisu Saddiqa Nabila Sumayya Miemie ko Ameerah?."
Zaraddin ya ce
"Ina duk ba su ba wancan kyakkyawar Feeryal dai."
wani irin d'agowa Shamsuddin ya yi.
Mom ko korji ta dafe a tare suka furta
"FEERYAL!."
Zaraddin ya ce
"Eh ita ita nake so idan ba ita ba babu wata macen da zan aura, kawai a bani ita idan ba haka ba."
ya wani girgiza kai.
da karfi Shamsuddin ya mike ya nuna shi da yatsa ya ce
"Karya kake Feeryal bata dace da kai ba."
Zaraddin ya mike yana cewa
"Idan bata dace dani ba da wa ta dace, ita nake so kuma sai na aure ta."
"Dani ta dace ba da kai d'an kwaya ba, Feeryal tawa ce."
da karfi Zaraddin ya shako wuyan Shamsuddin ya ce
"Idan ban kashe kaba na nuna maka halin kwaya anan,
idan ka sake cewa Feeryal taka ce idan ban bubburma maka wuka ba."
Shamsuddin shima ya cukime shi yana fad'in
"Mu burmawa juna wuka dai, duk iskancin ka ka isa kayi min na kyale ka ne,
na fad'a baza a aura maka ita ba,
kayi abin da zakayi."
da sauri Mom ta shiga turesu tana fad'in
"Bakuda hankali ne yanzu akan mace kuke fad'a, macen ma aljanar ruwa,
to duk cikin ku babu shegen da ya isa ya aure ta,
baku isa ku auro min wancan bakar mayyyar aljanar ba."
Shamsuddin ya sake shi ya juya da sauri ya nufi kichin yana fad'in
"Zakaga abunda zan yi a kan ta kuwa."
Mom ta sa hanu a kai ta yi kiruru tana fad'in
"Wayyo Allah tambad'ad'd'iyar yarinyar can ta had'a min yara fad'a zasu kashe kansu."
Zaraddin ya fito da wuka ya yi kan
Shamsuddin.
Dad da shigowar sa ke nan ya buga masa sawa.
"Zaraddin! kar ka soma."
da sauri Mom ta shiga sakanin su hannun ta akai bata fasa kururuwa ba.
da d'ebewa Feeryal albarka ba.
Zaraddin ya saki wukan kasa yana huci ya ce
"Wallahi da na nuna maka halin kwaya Feeryal kuma ni zan aureta ba kai ba."
Dad yakuma buga musu tsaya
"Banzaye shashshun yara, yan zu akan mace kuka shirin kashe kanku,
ina ta son ganin rayuwar ku yaci gaba ina son ganin komai ya juya ya dawo karkashin mu,
amma kun tsaya shashanci, barsu su kashe kansu."
Zaraddin ya juya fuu ya yi waje yana huci.
Miemie dake tsaye bakin kofa rike da kula Ammah ta aiko ta ta kawo wa Mom ta tsaya tana kallon ikom Allah.
ai tana bata kular ta juya.
in da tabar Ammah da Faisal nan ta same su, ta karaso baki na kaikayi na son bada labari.
ta zauna tana rike hab'a da fad'in.
"Cafd'i jam da yau anyi kisa agidan nan."
Ammah ta waro ido ta ce
"Kisa kuma?."
Faisal ya ce
"Ji wannan makaryaciyan ai ke narantse Miemie kin shiga uku da baki."
ya yi maganar yana kai mata bugu a baki, ta kauce tana fad'in
"Wallahi da gaske ne Ya Zaraddin da Ya Shamsuddin suke fad'a,
Ya Zaraddin har da d'aukan wuka wai zai kashe Ya Shamsuddin, wai kuma kasan akan wa suke fad'an? akan Feeryal jifa wai duk suna sonta."
Ammah ta ce
"Ikon Allah lallai yarannan basu da hankali shine har da d'aukan wuka."
Faisal ya yi shiru kamar ruwa yaci kansa.
Miemie ta kalleshi ganin yadda jikin sa ya yi sanyi ta ce
"Ai kaima Ya Faisal tuntuni na gama gano ka kaima sonta kake,
Feeryal dukkanin ku baku da ce da ita ba."
hararar ta ya yi ya ce
"Ke ina ruwan so da wani dacewa ko rashin sa,
da Ammah zataje ta sami Aunty nasan da za'a bani ita."
"Babu in da zani ma duk kuje ku nimi matanku a wani wajen."
cewar Ammah.
Miemie ta fashe da dariyar ganin yadda ya wani narke murya kamar maraya.
ya bita da hanu ta mike da gudu ta shige d'aki tana dariya.
Chapter 34 · 0% Book details