← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 63

Sashe 8

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

7⃣

Wuraren shida na yamma yatashi awahale sai atishawa yake, addu'an tashi daga bacci yayi kafin ahankali ya sauko daga gadon yana atishawa juyawa yayi ya kalli ac yaga ko akunne ne amma akashe hakan yasa yajuya ya bude kofan bathroom ya shiga, wani irin hadadden babban bathroom ne mai hade da closet an raba wajen part biyu bangaren dama wani irin hadadden closet ne komi na wajen blue, ga kaya kala kala dake jikin hanga ga kuma yar stool a tsakiyar wajen sai bangaren haggun kuma koface wacce bayi ke ciki bude kofan yayi ya shiga.

Yay kusan 15 minutes kafin yafito daga bathroom din sanye dawani maroon hoodie da aka rubuta gifted agaban daya daura hulanta akai sai dogon bakin wando da bakin safa akafanshi sai uban kamshi yake, jinginar da kanshi yay ajikin bangon dakin kafin ya dago kai ya dunkule hannu ya daki bangon dakin da karfin bala'i yana tsaki ganin hoton fuskar Nadeera yakara flashing aranshi, dadduma ya shimfida yay sallan la'asar koda ya idar akan dadduman ya zauna ya daura kanshi akan gwuiwanshi, tsaki yaja yace "damn it" fuskar mace bai taba tsayamai arai kaman na yarinyar nanba but why?! Kiran sallan dayaji daga masallacin gidansu yasa ya mike tsaye, slippers ya zira da sauri yana atishawa yana hamdala yabude kofa yafita daga dakin, sauka yayi yafice yay masallaci danyin sallan magrib. Ko amasallacin magrib da isha'i aka hada sabida hadarin daya hadu sosai yana idar da azkar ya mike yafice daga masallacin kafin su Abdallah su rikeshi da magana dan ko kadan bayaji magana, stairs yahau ya bude kofa ya shiga dakinshi mayar da kofan yayi ya rufe harda saka key ya jingina da kofar yana sauke ajiyan zuciya, atishawa yayi yay hamdala kafin ahankali ya daura hannunshi kan heart dinshi da duk single beat remains him of her in his arms, ahankali ya daga kai ya kalli plain white chiffon curtains din dake jikin babban window dakinshi dake kadawa sosai sakamakon iskan da akeyi na shirin ruwa, garin yay duhu sosai kaman irin tsakar dare dinan sabida hadari sai walkiya sama take, ahankali yatashi daga jikin kofan yafara tafiya kaman kwai yafashe mai aciki yay wurin window ya tsaya ahankali ya mika hannunshi ya shafa labule slowly kafin yakai dayan hanunshi yasa duka hannayen shi ya raba curtains din kowanne yatafi bangare daya hakan ya bayyana window daya dan budu kadan, hannu yatura ya bude window duka waaa, yadaga kai yana kallon sama, bai damu da ko sauro ko wasu kwarin su shigo mai dakiba, shiru yayi yana kallon sama iska da kamshin kasa dana trees yawani irin blowing suna ratsa duka jikinshi suna karasashi jin wani iri da baitaba jin kanshi aciki ba, ahankali ya mika hanunshi ya fitar dashi waje ta window yana feeling yanda iska ke dukan hannu dan yayyafin da ake na zuba akan hannun, hanun ya kafe da ido jikinshi namai wani iri ahankali yace "what is happening to me?".

***

Gida suka wuce suna shiga har dakinta Abba ya kaita yace "jekiyo wanka ki chanza kayan nan kici abinci zai aika Ahmad ya siyo miki magani karki damu everything will be fine" gyadama Abba kai tayi ta wuce bayi tana atishawa tanajin wani irin sanyi ajikinta hakan yasa ta shiga bayi da sauri, wanka tayo da ruwan zafi ta dauro alwala kanta nawani irin ciwo tafito, gaban wardrobe dinta taje tajawo wani dogon riganta baki ta zira ta saka hijabi tahau kan dadduma da kyar tai sallan la'asar dan sosai kanta ke mata ciwo gashi sanyi takeji sosai tana idarwa tacire hajabin tafada gado ta lullube da bargo tana godema Allah da ya tsareta yau bata mutu ba da wanan BOYAYYEN MUTUN dinan fa ya harbe ta, atishawa tafarayi tayi sunkai biyar ajere hakan yasa takara jan banrgo ta dukunkune ahaka bacci yay gaba da ita koda Abba ya shigo dan kiranta taci abinci bacci yaga tanayi hakan yasa ya kashe mata wuta yafita da Ya Ahmad sukaci karo shima zaizo dubata hakan yasa yace "tai bacci son" gyada kai yayi yajuya yay falo shikuma Abba ya wuce dakinshi dake nan corridor zama yay akan daya daga cikin kujerun falon ya zauna wayanshi yaciro daga aljihu number dayay saving da Sweetheart yaciro yay dailing har yagama ringing ba'a dagaba, nabiyu ma haka ana uku ne aka dauka daga ta chan bangaren Mum tai magana ahankali tace "Alhajina please ina meeting da some investors ne, i will call you back i promise Alhajina" ta katse wayar dip, wayar Abba yacire daga kunenshi yabi wayan da kallo yanajin wani irin haushi a ranshi, ajiye wayar yayi ya gyara zama yana kallon news, saida aka kira magrib sanan yatashi ya shiga bayi dakenan falon shi ya dauro alwala ya chanza kayan jikinshi zuwa jallabiya brown sanan ya fito, dakinta yafara shiga har lokacin bacci take tadata yayi ta tashi sanan ya wuce masallaci, da kyar ta lallaba ta shiga bayi alwala ta dauro ta fito tasaka hijabi tai magrib rashin karfin datake dashi yasa bata iya karanta Al Qur'ani yauba, tashi tayi ta bude kofa tafito tayi falo kitchen ta shiga ahankali ta jona ruwa a heater kettle yana tafasa ta hada tea mai kauri ta dawo dining ta zauna tana juya spoon a cup din tana kallon tea, wani irin kewan Mum takeyi bana wasaba sokawai take ta rungume Mum taji dumin mahaifiyar ta kotaji natsuwar datake nema, ahankali ta cire spoon din ta ijiye ta dau cup din takai baki tafara sha sanan ta sauke cup din tana kallon tea dako kadan baya mata dadi, sake kafawa abaki tayi ta kwalkwale sanan tadau spoon din tasaka acikin cup din tamike ahankali ta shiga kitchen din tsayawa tayi awajen tap din tana dauraye kofin tana kallon window kitchen din yanda gari yay duhu sosai sakamakon hadarin daya hadu sai walkiya ake, wani irin abu taji yana fizgar ta hakan yasa ta ijiye kofin ahankali tai wajen kofan dazai sadata da backyard tabude wani irin iska ne ya hurata hakan yasa tadan lumshe ido kafin ahankali ta budesu, kallon sama tayi yanda ko ina yay bakinkirin hazo sai tafiya yake wani irin iska mai dadi dake kamshin kasa na shiga hancinta, sosai take kallon sama jikinta nawani iri, lumshe ido tayi sakamakon yayyafin da aka fara wani iska dayazo ne ya feso da yayyafin akan fuskarta runtse ido tayi sosai kafin ta bude idon ahankali tana kallon sama tace "maisa nakeji kaman wani abu zai faru da rayuwata? Why do I feel as if something is about to happen? Ya Allah please protect me, am very very scared of him, ko rufe ido nayi saina ganshi, i can't get his face out of my head, Ya Allah am afraid of this mask man, ya Allah ka kareni ka tsareni" jinkinta ta rungume yayyafin na feso mata tana kallon saman da wanan karan yay duhu sosai, tai nisa acikin tunani, hannu taji akan kafadarta hakan yasa tasaki wani irin ihu tajuyo afirgice Ya Muhsin tagani tsaye abayanta yana mata wani irin kallo yace "Ke mehaka wai mekikeyi anan bakiga ana yayyafi bane jibi yanda ruwa ya jikaki" yanda ta kwalalo ido tana kallonshi fuskan shi na rikadan mata zuwa fuskan boyayyen mutum, runtse ido tayi da sauri ta kankame jikinta breath dinta na neman daukewa, jijiga kafadunta yayi yace "Nadeera" ahankali ta bude ido ta kalleshi ta lankwasa kai ahankali tace "Na'am" matsar da ita gefe yayi ya kullo kofar kitchen din sanan yajuyo ya kalleta yace "are you okay? Me matsalar ki?" girgixa kai tayi hawaye na taruwa a idonta ahankali tace "am just missing Mum" "don't worry takusa dawowa, Ahmad yakai miki magani daki jeki sha" gyadamai kai tayi tabi gefenshi tafice daga kitchen din da sauri, bin kofar databi yayi da kallo kafin ya bude fridge yadau cold maltina yafita daga kitchen din yay dakin Abba.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

8⃣ - 9⃣
Chapter 8 · 0% Book details