← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 63

Sashe 38

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wani irin mugun sanyi jikin Mum yayi, kukan datake yi yakasa tsayawa, ahankali ta rufe bakinta da hanunta tana kallon Abba dayake huci kaman kumurci kafin ta janye hanun daga bakin tace "Alhaji Nadeeran? Yar da muka raina tun tana 3months old a duniyan nan shine kakeso a matsayin mahaifinta fa kake?" nuna mata yatsa Abba yayi cikin zafi da bala'in masifa yace "ki dena kirana mahaifinta aini ba ubanta bane, Nadeera halaliyata ce ba haramiya ba, akwai aure tsakanina da ita, danna raineta tun tana 3months doesn't make me her father so aurenta zanyi" chakumo shi Mum tayi cikin fushi dawani irin kishi tace "wlh bazaka auri Princess ba, baka isa ka aureta ba saidai in bana numfashi a duniyan nan, wlh bazaka auri Princess yarinyar danake so, na raineta a matsayin tawa kawani bijiromin da zancen nan ni zaka hada kishi da princess? Wlh Alhaji daka aureta gwara ka auro wasu mata dari daga waje zaimin ciwo amma zan iya jure wanan bana princess ba, wani irin concoction kakeso kayiwai ma? bazaka taba auren princess ba wlh saidai in bana numfashi a doron kasan nan na rantse maka" wani irin kallo Abba yamata da tunda ta aureshi bai taba matashi ba yace "cikani, wlh karki bari zuciya ta dibeni namiki abinda bamu tabayiba tsawon shekaru talatin da daya da auren mu, ki cikani hajara" kin sakinshi Mum tayi takara chakumo shi tace "wlh bazan sakeka ba saika janye maganan auren princess, kamayi tunanin tayaya zamu kawo mata zancen bamune iyayenta ba, wlh wlh bazaka auri princess ba" wani irin tunkude Mum Abba yayi tafadi akasa hartana bige gado yace "wlh auren princess kaman nayi nagama, nine ubanta kuma dole tabini kotaki kotaso dole tamin biyayya saina aureta watch and see, saidai ki mutu amma princess saina aureta nasha zumanta ta haifamin cute twins girl, see bama a Nigeria zamu zauna ba garin zan barmuku dan bazan iya tolerating wani cikinku ya batamata rai ba, and wlh inzaki kawomin nonsense am ready na sakeki dama darajan yarana maza kikeci wlh da kike tafiye tafiyen ki batare dakin tambayi izinina ba just because kafin aurenmu parents dinki sunce zan barki kiyi business doesn't mean you can go anytime without my permission, be very careful marriage dinki na rawa Hajara" tsallaketa yayi inda take zaune yay gaban wardrobe wani dogon wandon shaddan shi ya dauko ya sharce ya saka cikin fushi ya saukar da jallabiyar shi yadau car key da wayarshi ya bude kofan dakin nashi ya fuce cikin fushi Mum tabi kofar da kallo, sosai take wani irin kuka wanan wani irin fitina ne tazo ta tarar daga dawowan ta, wanan wani irin kaddara ne da musiba "innalillahi wa innailaihi raji'un, na shiga uku" tayi kuka fin na awa biyu kafin ta tashi ta kakkabe jikinta ta ficemai daga dakinshi ta shiga nata dakin, zama tayi abakin gado tai tagumi tana tunani saikuma tasake fashewa da kuka sosai tafi minti talatin ahaka kafin ta tashi ta shiga bayi alwala ta dauro tadawo ta kabbarta salla, itace jiran Abba shiru shiru har sha biyun dare bakaramin damuwa tayiba dan tana son mijinta sosai Abba is such a sweet kindhearted loving husband and father, ahankali ta tashi ta dawo falo ta zauna akan dogon kujera tana kallon agogo ahaka bacci yay gaba da ita a dogon kujera.
Chapter 38 · 0% Book details