← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 63

Sashe 2

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tana shiga some students mate dinta guda biyu tagani zasu shiga ward da sauri ta taresu cikin innocent voice dinta tace "ammm please ina Fauzy taje ward ne?" atare suka "no yanzun nan ta shigo, taje common room" da sauri tai hanyar common room dinsu kafin HOD dinsu takamata ta turata ward, bude kofan common room din tayi wani irin ihu budurwan dake zaune tana danna waya tayi atsorace tazaci HOD dinsu ce, hararanta tayi ta kulle kofan da sauri tana daura hannu akan lips tana hararanta tace "banza anhana zuwa da waya kina zuwa da waya ko?" ajiye wayar fauzy tayi ajaka ta tashi ta rungumeta tana dariya saikuma ta saketa tace "banza maisa kikai latti yau?" kaman zatai kuka ta sauke jakarta ta ijiye tace "Mum ce tai tafiya fa Fauzy, daga ni yanzu saisu Abba dasu Ya Ahmad fa sai mai mana aiki and ita bata kwana da yamma take tafiya kullum" takara she maganan hawaye na taruwa a idonta, Fauzy tace "sorry kinji yar Mummy kema ai dazaran miji yafito kiyi aurenki ki barmusu gidan su kinji saikinga dama zaki dinga zuwa" dungure mata kai tayi tana hararan ta tace "ke komi aure aure, to dan kiji sainayi school of Post Basic nursing nai specializing a anesthesia ko midwifery kafin nai wani aure" tabe baki Fauzy tayi tace "kya rube agida bokoko" itama tabe baki itama tayi tace "rubaben tumatir yafi dadi" kama baki fauzy tayi tace "laaaa Nadeera yar air cefake, rotten tomatoe" hararanta tayi zatai magana Fauzy tace "dalla nidai dau kayan aikin ki da log book dinki mu wuce baniso na biye miki rotten tomatoe" dariya kawai tayi bata karace mata komiba duk duniya fauzy ce kadai kawarta, yarinyar kawar Mum ce, bakatabajin tsakaninsu, bude jakarta tayi taciro statoscope dinta da log book, ijiye jakukunan sukayi suka wuce suka tafi sukai signing in, dayake wanan week din tana female surgical ward ne itakuma fauzy na pediatric ward hakan yasa ko waccen su tawuce ward dinta danyin aikinsu kafin da azahar su hadu su tafi masallaci, ward dinta ta shiga tana gaida matayen marasa lpy tana duba drip din da aka makala musu, kafin tawuce nurse desk dinsu ko zama batayi ba, senior nurse din dake wurin tasa taje tai taking vital signs din all d patients din ward din hakan yasa ta wuce.

***
Babu kowa afalon hakan yasa yay stairs da dan gudu gudu yay sama, wani daki yabude ya shiga, computers ne kusan uku adakin akan wani dogon table saikuma macbook akan wani dogon lumtsatsen kujera, jakar dake bayanshi ya ijiye akan table din kafin yadau MacBook dake kan kujera ya zauna akan kujeran ya bude yafara aiki, yakai kusan 30min yana danne danne, knocking kofar akayi hakan yasa ya dago kai yana kallon kofan, agogon hanunshi ya danna saiga hoton samari biyu dake bakin kofan nan ya bayyana ta jikin agogon kaninshi ne, Abdullah wanda yake karmi da Omari daya girmeshi, ajiye MacBook din yayi yatashi yay wajen kofan ya bude kofan yakoma inda yake yadau MacBook dinshi ya cigaba da abinda yakeyi, shigowa dakin sukayi suka zauna kusa dashi suka sakashi a tsakiya, na gefen daman shi ne yace "Ya Marwan were you able to hack his system?" wani irin wahalallen tsaki yaja maiyar kara ya ijiye MacBook din akan cinyar Omari dake gefen haggunshi yajuyo ya kalli Abdallah dayamai maganan, cikin wani irin murya irin na terrors dinan dakakkiya yace "no, dole saina sami kwayar idonshi, eye scanner yake amfani dashi, don't worry i know how i will get it, i have to go hospital din da aka kwantar dashi, kun mini abinda nace?" yana maganan irin dole dole dinan kaman wanda yasha wani kwaya yana kallon na gefen shi Omari, Canon camera hanunshi ya mikamai hakan yasa ya karba yana dubawa, hotunan plate number mota ne na motoci guda uku hakan yasa ya gyada kai tareda ijiye camera a gefen shi yace "gud, wat time jirgin su zai sauka da daddare?" Omari yace "10:45pm, suna tare da 8 bodyguards, 3 drivers, zasu shigo kuma da kudin" gyadakai yayi batare dayace komi ba, sai chan yace "su kamal fa hope suna various post dinsu" Abdallah yace "Eh, zasusan yanda zasuyi su makala device din a logage dinsu once sunyi landing" murmushi yayi mai sauti kafin ya kalli Omari yace "kuje ku huta, zanyi wasu ayyuka" murmushi Omari yayi yace "okay Genius, Abdallah muje kadafamin dat ur pasta, am hungry" murmushi yayi tacikin mask dinshi yana kallon kanin nashi, Abdallah ya harare shi yace "bazan yiba ai we have kuku because am d auta ai am not ur kuku ko Ya Marwan" yay maganan yana kallon Marwan dake kallonsu tacikin mask, zaiyi magana Omari yace "don't take side Ya Marwan, Abdallah baida kunya kwanan nan ya rainani wlh me acikin dafa pasta" "Ya Marwan wlh shine ya rainani, he's 28 am 26 but saiya dinga treating dina kaman wani under 12, duk inmun fita operation he always take my post, and dazaran mun dawo gida he will be begging me to cook for him, am only cooking for Ya Marwan kaje kaci na kuku bazanyiba" "saikayi, i said saikayi naughty spoilt brat" "nine spoiled brat?" yay maganan yana mikewa daga kan kujeran kaman zai daki Omari, hakan yasa ya daka musu tsawa tareda daga hanunshi sama. "enough!" natsuwa dukansu biyun sukayi, tashi yayi ya rungumosu duka zuwa kafadun shi batare dayay magana ba, sunkai kusan one minute ahaka kafin ya nisa yace "kudena fada, i hate it, my heart break anytime daga kunayi, Omari have you forgotten Momma's last words?" girgiza kai yayi ahankali jikinshi yay sanyi, hakan yasa yace "good! we are one, we only have each other awanan duniyan, i love you two" murmushi dukansu biyun sukayi atare sukace "we love you you more Ya Marwan" Abdallah ya mika hannunshi yace "and we are" Omari ne yadaura hanunshi akan na Abdallah, ahankali shima ya sakesu ya daura nashi akan na Omari atare sukace "The BM's" ihu sukayi atare suka rungume mai safan fuskan suna dariya kafin su tureshi da karfin bala'i yay kasa suka daddaneshi duk suna dariya, murmushi yayi mai sauti baice komiba dan kansu suka dagashi yay kaman zai kamasu da gudu suka fita suna tafi Abdallah hardamai gwalo suka fita. Ahankali yatashi daga kasan yana gyara zaman bakin glass dinshi yakoma kan kujera ya zauna yadau MacBook dinshi ya cigaba da abinda yakeyi.
Chapter 2 · 0% Book details