← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 63

Sashe 29

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahankali ya tsugunna agabanta yana kallonta batare dayace mata komiba, harde kafafunta tayi sosai tana kara daure hannayenta a kirji tana goge hawayen datake yi da bayan hannu kanta akasa tana kallon cinyoyinta da takeso taja towel ta rufesu amma ba halin hakan, dan fuzar da iska yayi dan kukan nan datake yi na mugun tabashi bayaso ko kadan, murya chan kasa yace "kinsan inda Mumyn ki takene?" juyo dakanta tayi ta kalleshi kafin ta kawad da kai da sauri bakaramin cika mata ido yayiba cikin manyan fararen kayan data ganshi gabanta na faduwa, girgiza mai kai tayi muryanta na rawa sosai tace "t..ana D..dubai" shirun dataji yasa tadan juyo dakai ta kalleshi ahankali ganin fuskarshi na saitin tane yasa tasake kawad dakai da sauri tace "please zan kirata ne ince tazo ta tafi dani kaji" mikewa tsaye yayi yana kallon agogon hanunshi kafin ya kalleta yace "you are not going anywhere, bazaki kara barin gidan nanba" fashewa tai da kuka sosai tana makemai kafada alamun a'a takasa magana sabida tsoro da shakkan shi, tsayawa yayi yana kallonta kafin yasa hannu yawani irin fizgota ta tashi tafado jikinshi arude takoma baya tana kuka tana kara rike towel din jikinta da kyau, sake jawota yayi ya sakala hanunshi daya ta bayanta ya riketa da kyau yana kallon yanda gashin gaban kanta ya kwanta lub ata goshinta, hadiye kukan tayi gum tana zaro ido kirjinta nawani irin bugawa tana kokarin ture hanunshi daga bayanta amma takasa, ta saukar da kanta kasa tana rera kuka ahankali, ahankali yasa yatsan shi yadago habarta kin kallonshi tayi saima hawayen dake gangarowa, dawani irin calm voice yace "ke yarinya ce? Don't you get tired of crying? Clean those tears" ya nuna mata hawayen daya gama wanke fuskarta, da sauri tasa bayan hannu jikinta na rawa sosai ta share hawayen batare daya saketa ba ta saukar da hanun kasa tana sauke ajiyan zuciya, janye hanunshi yayi daga waist dinta ahankali jin yanajin wani abu da tunda yake bai tabaji ba ya maida hannun cikin aljihu murya chan kasa data dan dishe yace "go and get dress am waiting for you" yay maganan yana nuna mata kofar bathroom din da kai, da sauri hartana neman turgudewa tanadan dingishi tai wajen kofar, bude kofar tayi ta shiga da sauri yana binta da kallo.
Wajen kayan ta taje tana share hawayen ta bude ledan super market din wani dinkakken atampa English da aka mata riga da skirt kayan kalansu brown and milk ne anyi musu stone work daya kara karama kayan kyau sosai ta ciro, saka kayan tayi tana kuka kaman ta shide wanan wani irin rayuwa Abba yasata aciki, bakaramin kyau kayan suka mataba tadau dankwalin su ta yafa dan hijabin ta na falo kuma kayan sundan matseta tafito ahankali tabude kofan batare data kalleshiba tai wurin gadon tana dan dingishi tadau pink hijabin ta dake kan gado da sauri ta saka ta zare dan kwalin sanan tq zauna a bakin gadon tana wasa da yatsun ta batare data dago kaiba, yakai kusan 2min yana kallonta kafin ya mike tsaye yace "let's go" da sauri ta tashi tsaye murmushi da tunda tazo batayi shiba ya lullube fuskarta tace "gida zaka maidani?" wani irin juyowa yayi yazo gab da ita ya daure hannayen shi ta baya hakan yasa tadan matsa baya da sauri tana kallon fuskarshi dake cikin mask, ahankali yace "gida?" gyadamai batare datai magana ba murmushi mai kama dana tsoro akan fuskarta, juyawa yayi yay wurin kofa ya bude kofan yace "lets go" ahankali take tafiya hartazo wajen ta tsaya nesa dashi hannu ya mika mata alamun ta bashi hanunta, hannu dake cikin safan hannu tabi da kallo kafin ahankali hanunta na rawa ta mikamai nata tadaura akan nashi wani irin shock taji harsaida tasaki ajiyan zuciya tana kallon hannayen, shima kusan hakan yaji yadaure ya rike hanun nata dakeda taushi yajata suka fice daga dakin ya rufe kofan tana gefenshi saibin babban gidan take da kallo yanda ko ina yake tsaf tsaf kaman ba mutane aciki, stairs sukayi suka fara sauka, ahankali yake binta sabida kafarta har suka sauka babu kowa afalon sai babban tv dake aiki, sai kallon ko ina take, bude kofar falon yayi suka fita compound, nanma babu kowa sai kallon compound din takeyi da uban motoci kusan shida ke ciki, sukai baya tana bin ko ina da kallo wani white yar babban mage ta gani tana wasanta tana hawa bango da sauri ta rirrikeshi ta tsaya batare data kalleshiba tace "kunada mage i don't like it" kallon magen yayi kafin ya kalleta yanda duka hankalin ta na wajen magen yace "is Abdallah's, muje bazai miki komiba" dago kai tayi ta kalleshi kaman zatai kuka saikuma ta kalli magen tace "are you sure?" matso da kanshi yayi ta wurin kunenta yace "yes muje kona kira miki ita ne?" da sauri takara rike hanunshi tabishi suka bar wajen, gaban wani part suka tsaya kafe kofar tayi da ido hakanan gabanta taji yana faduwa bude kofan yayi ya shiga hanunshi rike da nata tana biye dashi abaya itama ta shigo, ido da ido sukayi da Abba dake zaune kan kujera yana kallon su hakan yasa kirjinta yawani irin buga dum! tafara nishi kaman zata sume tana komawa baya sosai tanaso ta fizge hanunta tafice yaki sakinta.

Juyowa tayi ta kalleshi a mugun rude ta fashe da kuka sosai tanaso ta fizge hanunta ta gudu waje tsabagen yanda ta tsorata kaman taga dodo ya riketa gam yaki sakinta, da karfi tsiya ta shiga tureshi tana bubbuga kafanta akasa. "sakeniii" tana ture kirjinshi tana kokarin bude kofa, tare kofan yayi ya rungumota jikinshi da kyau yana bubbuga bayanta yana kallon fuskar Abba tacikin mask yanda Abba ke wani irin kallon bayanta idanunshi sun chanza kala, ahankali yacirota daga jikinshi ya shafo gefen fuskarta yace "shiiii" fashewa tai da kuka sosai tace "please dan Allah ka matsa, wlh am scared zai kamani" ta fashe da wani kukan gani take kaman Abba zai taso ya kamota, girgiza mata kai yayi tareda kama hanunta da karfi yay cikin dakin da ita tana tutturjewa tana makewa abayanshi, zaunar da ita yayi akan kujeran dake facing na Abba tana yunkurin ta mike tsaye ya maidar da ita ya zaunar yace "calm down zaiyi magana dake ne will come back in 10min time, calm down babu abinda zai miki kinji" fashemai ta dawani irin kuka ta dago kai ta kalleshi tana girgiza mai kai tana makemai kafada, ko kadan batason ganin Abba balle ita kadai dashi awuri, juyawa yayi zaitafi da sauri ta rikemai riga ta kara karfin kukan ta, juyowa yayi ya daka mata tsawa yace "i said sit!" da sauri ta zauna tana nishi hakan yasa yajuya yafita ya rufo musu kofan, maida kanta tayi kasa jikinta na rawa sosai tana goge fuskarta da hijabi har cikin ranta jitake da Abba gwara wanan dodon ko kadan batama son ganin Abba hakan ya tuna mata abubuwan daya mata kuma batason hakan, sotake ta manta.
Chapter 29 · 0% Book details