← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 63

Sashe 41

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahankali ta daga hannu ta share mata hawayen fuskanta tass tace "how did you get here Princess ya akayi kikazo nan ina mijinki? Tayaya kikazo?" komawa jikin Mum tayi ta kankameta kaman zata koma cikinta tana wani irin jin natsuwa aranta data dade bata jiba uwa dabance ako ina, cikin sheshekan kuka tace "tunda naji kin dawo kina nan shine na gudo" "kika gudo?" Mum tafada cikin tsananin bacin rai, gyadama Mum kai tayi a jikinta tace "eh Mum nakira number ki akashe na Ya Muhsin ma haka shine nakira Ya Ahmad, Mum wat is wrong with Ya Muhsin?" tai maganan tana kallon Ya Muhsin daya ramemata a ido, dago kai Mum tayi tama Ya Ahmad wani irin kallo tace "ubanwa yace kaje ka daukota wen u know the problem on ground bazaka iya kirana ka sanar dani ba" cikin masifa yace "Mum kidenamin magana haka, d so called gang kikeso ta zauna dashi? And I tried calling you wayanki akashe, d problem on ground can be solved another way bamu barta ta rayu da gangster ba, yanzu on your phone ki kira kawarki Maman fauzy na kaita gidansu let her stay dere kafin Ya Muhsin ya warke musan mezamu yi" ya kalli Nadeera datai lamo ajikin Mum tana sauke ajiyan zuciya kaman wacce tai dambe da mutum dari gaban goshinta nadan jini na kurjewa yace "stand up princess muje ayi cleaning wound dinan mutafi gidan su Fauzy" da sauri ta dago kai ta kalli Mum, Mum din ma wani irin kallonta take shaidan na raya mata wasu abubuwa aranta dan yauce rana ta farko dataga kyan da Abba yake fadi, kyan data saba gani a fuskan Nadeera kyan yarta ne amma yau taga kyan da kowani da namiji zai gani yakuma yaba hakan yasa taji wani iri amma ta danne tana karantoma zuciyarta Nadeera yarta ce tadena kawomata irin abunan, ahankali ta shafa kumatun ta, tamata peck a wurin tana murmushi, harta bude baki zatayi magana aka bude kofan dakin aka shigo wani irin faduwa gabanta yayi batasan lokacin data rike rigan mum gamgamba tana zare idanu, tsabagen rudewaAbba wayan dake kunenshi salubewa yayi yafadi akasa hanunshi dake rawa sosai ya daga yay pointing Nadeera, cikin tsananin rudani da mamaki yace "Princess" da sauri ta saki Mum tareda dirowa daga jikinta takoma ta bayan kujeran datake ta tsugunna tana jan gefen rigan Mum jikinta na rawa sosai, da sauri Abba ya maida takaran dake hanunshi na test din da akama Muhsin Aljihun gaban rigan shi yakarasa shigowa dakin yana dumfaro inda suke, fashewa da kuka sosai Nadeera tayi tanajan rigan Mum tana yarfe hannu kaman taga dodo, mikewa tsaye Mum tayi cikin tsananin fushi tasha gaban Abba dake nufosu bilhakki tace "ina zaka Alhaji wai wat is this a hospital mukefa don't start with dat rubbish of yours, kagadai Princess doesn't know anything about that stuff please Alhajina respect your self kaga danmu kwance mubar shi yahuta yasami lafiya am begging you Alhajina let princess be" wani irin matsiyacin kallo Abba yama Mum ya nunata da yatsa yace "Hajara inba so kike na daddaka ki na tijaraki a hospital dinan bayau ki matsamin naduba yata cikin salama" ya nuna mata gefe da yatsa alamun ta matsa, kin matsawa Mum tayi hakan yasa ya gyada kai yaje ta gefen ta zai wuce Nadeera tawani irin fashe da kuka tanajan rigan Mum, shan gabanshi Mum tayi tarike kugu tace "Alhaji leave this girl alone ha'a wai meke damunka ne? Alhaji lafiyan ka? Kodai ammaka ne? Bakaga tsoron ka takeji ba yarinyar nan na bukatan hutu Alhaji am begging you kabarta, kabarta mana, Ahmad" ta kalli Ahmad daya jingina da bango ya runtse ido dan jiya ke kaman ya kashe mahaifin nashi daya koma bunsuru, tace "come and talk to your father o, wai wat is this Alhaji kaci maita ne kokuma haukan tsufa ce dan gaskiya you are not okay" passs! Passs! Abba ya sharara ma Mum lafiyayyun mari har biyu dayasa Nadeera wani irin zabura ta mike tsaye tana kallon Mum, Ahmad kuma yayo wajen da gudu yawani irin yo kan Abba kaman zai mareshi yana huci kaman mayunwacin zaki yanama Abba wani irin kallon tsana, wani irin kallo Abba yamai da jajayen ido kafin ya mikamai fuskarshi yana turemai kirji dakai yace "to mara kunya zaka rama matane? Nace zaka rama matane?" Yana maganan yana buga kanshi a kirjin Ahmad kafin ya dago ya nuna shi da yatsa yace "kama rama mata kaga yanda duniya zatayi dakai, yaro ya mari ubanshi yaga gayya, kuma kasan kamatudini tudan" yajuya ya kalli Princess dake tsaye tana kuka sosai tarike hanun Mum da tunda Abba ya zuba mata mari biyu kanta ke kasa tana share hawaye, wani irin fizgo hanun Nadeera yayi hakan yasa ta fashe da kuka sosai ta rike hanun Mum gamgam. "Mumm save me". janta Abba yayi yace "nace kizonan mutafi gida ko, am going to lock you up adaki, baki bafita harsai an raba dan shegiyan so called auren nan, kingama fita waje ballema ki hadu da makiyana su hure miki kunne, let's go my princess" cikin kuka sosai Mum tarike dayan hanunta tace "Alhaji dan girman Allah ka kyale yarinyar nan" wani irin tunkude Mum Abba yayi har saida Mum tafadi ta buge gefen cikinta da gado tai kara hakan yasa Ahmad yawani irin ture Abba yakusa faduwa amma bai saki hanun princes ba, cikin fushi yace "Abba wai are you mad? Wat is wrong with you please maisa kake kara zubar da girmanka a idonmu ne, look at Muhsin he's unconscious don't you have any respect for your children Abba?" wani irin kallonshi Abba yayi yana kara damke hanun Nadeera da kyau yace "Ahmad ni, ni, ni ubanka ka tura Ahmad nakusa faduwa?" yay maganan yana wani irin kallonshi irin look dinan da parent ke bama yaransu suji hankalin su yatashi, murmushi irin me ciwon nan Abba yayi yace "nika tunkude ni mahaifin ka Ahmad? Hmmm, Kaje zaka gani Allah ya tsine ma Albarka Ahmad! gaka ga uwarka kunfi sonta ai, shikenan nima bana bukatarku, bazama ku kara ganina a gidan naku ba, munbar muku kenan, lets go princess" yawani irin ja hanun Nadeera da duka karfin da Allah yamai tana ihu ana kallon su yafita da ita daga asibitin ya bude jeep dinshi baya ya jefata ya rufe ya shiga gaba yatada, da sauri Mum ta tashi ta kalli Ahmad daya dawo kaman gawa a tsaye tace "Ahmad let's follow them karya ma yarinyar nan wani abu baya hayyacinshi don't mind tsinuwarshi bazai kamakaba" hanunshi taja hakan yasa yafara tafiya kaman wanda baida jini suka fita daga asibitin amma har Abba yabar premises din, mota suka shiga Ahmad ya zauna yama kasa driving kaman tababbe tsinuwan Abba kawai ke dawomai, ganin haka yasa Mum tafito tadawo inda yake hanunshi taja tafito dashi ta kalli yanda idanunshi suka cika da kwalla sosai sunyi jajir taji kaman ta kurma ihu dan tashin hankali, ahankali tace "don't worry go and stay with your brother bari nabisu" shiga tayi ta tada motan tabar asibitin.

Sosai Abba ke wani irin gudu da ita, kuka take tana jijjiga marfin motan tana dana sanin gudowan datayi. Binsu Mum takeyi dan tana hangosu sai ihu take tana kuka tana sambatu. "dukni naja, is all my fault, na banzan tar da aurena, bana kula da mijina, bana bama yarana hakkin su, bana sauke hakkin aurena, Ya Allah nasan nimai laifice amma please don't punish me tawanan hanyan, Ya Allah natuba". Mutuwa taji motan tayi a tsakiyan titi ta kunna ta kunna yaki kunnuwa ta daga kai taga motar Abba taimata mugun nisa, da sauri tafito mutane na ihu tahada goslow bata damuba ta tare machine tahaye sukabi Abba amma yabace mata bat ko hanyar dayabi bata saniba.

Sosai taci kukanta tai bacci cikin kukan, Abba yajuyo ya kalleta ya saukar da ijiyan zuciya kafin ya cigaba da tukin shi yay tafiya kusan 35 minutes sanan ya horn agaban wani babban gida a gwagwalada mai gadi yabude ya shiga, kana ganin gidan kasan sabon gidane, kashe motan yayi yajuyo yace "My baby Princess munzo gidanmu" .
[9/16, 10:11 AM] Lady: *this book is for sale karki karanta in baki biyaba, if u still go ahead and read keda Allah*

*Maman Abd Shakur*
Chapter 41 · 0% Book details