← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 63

Sashe 46

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahankali Muhsin ke bude ido da asuban fari wuraren karfe hudu, sosai yaji kanshi namai nauyi da kyar ya iya bude ido duka ya kalli gefenshi Ahmad ne zaune kan kujeran ya kifa kanshi akan gadon yana bacci, dan ajiyan zuciya ya sauke komi na dawomai wani irin hawaye mai zafi ya gangaromai hakan yasa ya runtse ido da sauri yanaji kirjinshi namai zafi sosai kaman an zuba garwashi, hanunshi yaji an kankame ana shafa gaban goshin shi hakan yasa ya bude ido Mum yagani tsaye akanshi sanye da hijabi idanunta sunyi jajir sun kumbura kana ganinta kasan kuka tasha sosai, hanunta yarike gamgam murya chan kasa irin na mara lafiya nan yace "Mummy Nadeera, I want to see her" ahankali Mum takai kanta ta sumbaci goshinshi tareda rungume kanshi tsam a kirjinta wani irin tausayin shi na shigan ta bana wasaba takai kusan 3min ahaka sanan ta dago kai ta sakeshi tanamai murmushi dukdan ta danne abinda ke cinta tace "how are you feeling Son? Bari nakira Dr yaduba ka" ta mike zata wuce da sauri ya riko hanunta hakan yasa ta juyo ta lumshe idanunta dan bataso tai kuka tai breaking heart dinshi dan dago kai yayi zai tashi da sauri tace "no, no no no karka tashi" tai maganan hawaye na gangaro wa daga idanunta, cikin raunanniyar muryan shi yace "wat is it Mum maiya faru wen I was unconscious?" zata girgiza mai kai ya riketa ahankali yace "please tell me Mum naji sauki, I can handle anything" shiru tayi kafin ahankali ta zauna kan kujera ta rike hanunshi gam takira sunanshi tace "Muhsin" kallonta yayi kafin ahankali yace "Na'am Mum" dan murmushi tamai sanan tace "inaso kamin wani abu da jarumi kadai zai iyamin shi kuma nasan d'ana jarumi ne, jarumin namiji nahaifa dan haka zaka Iya" shiru tayi takara kallonshi sanan tace "inaso ka yakice son Nadeera daga ranka Son, cus your father have ruined everything for you, tayaya zan bari ka auri yarinyar da mahaifinka keso, to bayan auren dawani ido zai dinga kallonma mata? Muhsin understand me am saying all this for your own good daga kai har princess din, koda ace yau babu aure akan princess wlh mahaifinka bazai taba barinmaka itaba ayanda yake jinta aranshi dinan nashi, mahaifinka dabai taba daga hannu ya nunamin ba for 33 years da aurenmu akan princess yadakeni Muhsin" ta share kwalla tacigaba tace "mahaifinka dake sonku kaman ranshi yabude baki ya tsinema Ahmad jiya akan Princess, mahaifinka da his family is number one yanzu bama gabanshi he's only after princess" shiru tayi tana kallon Muhsin dake kallonta asanyaye yana sauke wani irin ajiyan zuciya ahankali ta kama hanunshi tace "Son! I know, I know, I know nice to be blamed for everything that happened, I know am responsible for koma me Baban ku yadawo ayau, but wanan difficult phase dinan damuke facing kaddara ce da dole zai faru, yanzu abinda yakamata muyi shine mu yarda da kaddarar, mukuma nemi taimakon Allah, son zakaso ka auri yarinyar da baban ka try to rape? Try to molest? Zakaso ka auri yarinyar data gama gane sirrin ubanka? Zakaso ka auri yarinyar da mahaifin ka yagama gane sirrinta ne? Zakazo ka auri yarinyar da baban ka is going gaga for, zaka so ka dinga takaran kishi da mahaifinka? Wani zubin ana barin halaliya dan kunya da kawaici dakuma yakamata, and besides Princess dinma yanzu matar aure ce, banaso tasan we are not her parent abun zasu mata yawa, bantaba tunanin akwai rana dazata zo da zaisa mufada ma princess we are not her parents ba, ubanka yariga ya aurar da ita dudda guy din gangster ne, but naga affection dayake having mata, and wherever there's affection love definitely exist there, and inhar akwai So! to their Love can conquers everything, karkai mamaki kaga sanadin princess ya shiryu yadawo good man sunyi building family maiban sha'awa, addu'a zamu mata da fatan alheri kaji Muhsin, kahakura da Nadeera dan matar wani ce and babu kyau kana son matan wani" ta karashe maganan tana kallon idanunshi dasuka ciko da kwalla sosai ya tsaya yana kallonta kaman wata madubi, gyadamai kai tayi ahankali tana kokarin mayar da kukan datakeji ta shafa kanshi tace "talk to me Son wanan look din na breaking heart dina, yimin magana Umm my Muhsin, are you okay" wani irin tashi yayi daga kan gadon yafada jikin Mum ya kankameta yafashe dawani irin kuka sosai mara kara sosai hawayen na diddiga ajikin Mum, kankameshi Mum tayi tana patting bayanshi tace "cry, cry kaji ko zuciyarka tarage nauyi, I know how much you love princess, nasani, nasani son, kuma naso nabaka ita, I love you so much Son and am sorry is all my fault, duk laifi nane" sosai yake kuka jikinshi na rawa zuciyarshi namai wani irin zafi, daci, cikin kuka sosai yace "I love her, Mum wlh I love her so much, Mum bantaba yin budurwa aduniyan nan ba sabida I have Nadeera, Mum I love her so much, Mum I love her, Mum I love her, Mummy I love princess so much wlh" yanda yake kukan kaman zai shide ajikinta yasa ta ciro shi daga jikinta tana sharemai fuska da hijabin dake jikinta, ahankali Ahmad da kanshi ke kife dan duk maganganu dasuke yanaji ya goge hawayen dayake yi na tausayin wanshi, batun yau yasan Muhsin nason Nadeera ba dudda bai fadamai ba amma yaga sonta a idanunshi, sharemai hawayen dasuka kasa dena zuba mum tayi tana girgiza mai kai idanunshi sunyi jajir jikinshi yadau zafi, ahankali yarike hanun Mum da muryanshi data dishe tsabagen kuka yace "Mum zanbar kasar, lemme just go back to Toronto inda nai karatu idan na cigaba da zama anan ina ganin Abba I can die wlh" daidai nan Ahmad shima ya daga kanshi yana goge kwalla yace "am going with u" kallon yaran nata Mum tayi jitake kaman ta kurma ihu da kyar da taimakon ta dana Ahmad Muhsin dake ganin jiri sosai yatashi suka kaishi bayi ya dauro alwala yafito sai yahau kan dadduma yana salla yana share hawaye zuciyarshi na tafarfasa, a raka'a na biyun kawai ya yanke jiki yafadi sabida wani irin duhu daya gani dakuma kunenshi dasukai dummm!.
[9/18, 12:06 PM] Lady: *karki karanta in baki biyaba*

*Maman Abd Shakur*

Saida gari yadan yi haske kadan yafito daga masallacin yabar su Omari achan ya shigo part dinsu, kitchen ya wuce straight ya bude fridge ya dauko ice bag ya rufe yafito daga kitchen din yana tafiya a natse dan har yanzu cikinshi nadan ciwo ciwo yawuce sama dakinshi ya bude ya maida kofan ya rufe tareda kafeta dawasu irin idanun kaman zai cinyeta, ahankali ya karaso jikin gadon ya tsugunna agabanta yana kallon yanda fuskarta yatashi ga idanunta sun kumbura tsabagen kuka, hawaye sun bubbushe akan fuskarta tsabagen kuka, hanunshi ya mika ya janye dogon kalabanta daya sauka agaban fuskarta ya maidashi baya yanadan sauke ajiyan zuciya kafin ya daura icebag din akan kumburin fuskan nata yana dan danewa.
Chapter 46 · 0% Book details