← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 63

Sashe 13

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sallama tayi ta shiga falonsu, Mum din Fauzy tagani a falo tanacin fruits kama baki tayi tace "wanake gani yau yar tselen uwan yarinya baki zumunci dake dawanan takadirin yayan naku Muhsin, Ahmad dan albarka shine kadai ke zuwa gaidani" dariya tayi tafada kanta tace "kai Mumy toba ku kuka samu school of nursing ba dukshi ya cinye mana time" "ai school of nursing dinma ya taddaku da halin" tai maganan tana dungure mata keya, dariya Nadeera tayi ashagwabe tace "kai Mumy nidai ina wuni" tai maganan tana karbe bowl din fruits din hanun Mum tana dariya, dariya Mum tayi tace "ai nasan tunda kika shigo bazan shashi ba, oya tashi ki barmin falona yi sama wurin kawarki kafin ta sauko ku kusa kasheni da surutu" dariya tayi ta mike tsaye tace "bari nakirata muzo, Mum ina Ameer catboy din pjmask?" tai maganan tana hawa sama, dariya Mum tayi sosai tace "ai yanzu yace shine Romeo mai robot, yaje hadda saisa na huta sai 2 zai dawo" dariya tayi takarasa sama tanashan fruit din tai dakin fauzy kafa tasa ta buga kofan saida fauzy dake chatting tai ihu sabida tsoro, tsaki taja tace "me haka zakija kirjina yafashe" "ya fashen mana saime yarinya" tai maganan tareda zama akan bayanta, ihu Fauzy tayi ta tureta hakan yasa takoma gefe ta zauna, da sauri fauzy ta taso tana kallon fruits din tace "dan Allah ban fruit dinnan nasha tuntuni fa naroki Mum tahanani" make mata kafada Nadeera tayi tace "chibdi je akwai fruit a kitchen ki dauka ki yanka naki kema" zama kusa da Nadeera tayi tace "please rotten tomatoe wlh kiwiyan yankawa nake" "aiko zakiyi bindi irin mai remote dinan rubabbiya" dariya Fauzy tayi da kyar ta lallabata tabata sanan sukaci abinci sukai salla suka dinga hira.
Shida daidai Adamu yay parking yama gateman magana yakirata hakan yasa gateman zuwa kiranta, gyara fuskanta tayi tadau jakarta ta suka sauko kasa tama Mum sallama daki Mum ta tashi ta shiga ta fito da babban leda ta bata da kyar ta karba fauzy da Ameer suka rakota har mota rungume juna sukayi sanan tabude mota ta shiga tana musu bye suma bye suke mata har suka bar anguwan sukahau kan titi.

Sundanyi tafiya mai nisa da sauri Adamu ya gangara gefen hanya yay maza ya kashe motar ya bude kofa ya fito yazo ta inda take ya tsaya yana kallon tayan wajen, wani irin dogon tsaki yaja hakan yasa tai wining down tace "menene Adamu?" "wlh hajiya tayace tai less sosai bazata kaimu ko inaba, kuma laifinane tun agidafa nagani nace bari na dauko ki na dawo sainakai asa iska" ahankali tace "to yaya kenan zamuyi?" juyawa yayi yana kallon kan titin da machina da motoci ke wucewa babu mutane ma sosai wajen balle focanizer hakan yasa ya juyo yace "bari nahau machine naje nataho damai hura iska babu wani nisa yanzun nan zamu dawo" da sauri tace "toba akwai spare taya a booth ba?" "eh wlh hajiya akwai amma babu abin cire taya a motan ne" adan tsorace tace "to kodai nahau machine natafi ne kaikazo inka gama?" da sauri yace "a'a a'a kindaisan Alhaji bayason hawa machine sabida rawan kansu ko, wani abu yafaru dake ai na shiga uku hajiya, inda da masu keke napep a hanyan nan ma da dakaina zan saki ki tafi dan magriba tayi tama wuce, bari yanzun nan nahau machine naje na daukosu su hura mana iskan yanzun nan zan dawo kinji" ahankali tace "to shikenan" tana nan zaune tana kallonshi yatare machine ya dane, dan ajiyan zuciya ta sauke gabanta na faduwa faduwa dabatasan na meba, ahankali ta bude kofar motan tafito ta maida kofar ta rufe, tadanyo baya tana kallon yanda tayan yay less sosai kafin ta koma ta jingina da motar tai folding hanunta a kirji tana kallon motoci dake wucewa akan titin gakuma wata babbar jeep dake pake agaban motarsu, tana nan tsaye har wurin minti goma, gajiya da tsayuwan tayi ta juya ahankali tareda daura hannu akan handle din kofar baya zata bude ta shiga taji anwani irin fizgota da karfin bala'i, kafin ma ta ankare da wanda ya fizgotan an jata anyi bakar jeep din dake gaban motar su da ita an bude baya an turata sanan aka shiga, lokacin daya ya zauna tareda rufo kofan, ihu tabude baki zatayi hakan yasa yawani irin fizgota da hannu daya ya daura dayan hannunshi dake cikin safan hannu akan bakinta yana wani irin kallonta batare dayako girgiza kaiba, kwalalo ido tayi gabaki daya sakamakon hasken wutan wata mota dake kan titin daya hasko motarsu tasami daman ganin fuskarshi, wani irin racing heart dinta keyi tafara wani irin nishi kaman mai asma.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

1⃣1⃣ - 1⃣2⃣

Shi kadai ya dinga jera uban tsaki yafi sau goma, gabaki daya fuskarta yake gani barinma lokacin data daura hannayen ta akan fuskarta tana dariya, tsaki yayi yamaida hankalinshi yacigaba da aikinshi da MacBook yana so ya natsu amma ina ya kasa a screen din MacBook dinma ganinta yayi tanamai murmushi hakan yasa yawani irin jan dogon tsaki yarufe system din da sauri yace "damn it!" sai uban huci yake kaman kumurci yana duddunkule hannu, murmushi Abdallah yayi yacigaba da tukinshi abinshi yace "ari".

Koda takai gida babu kowa duk sun tafi aiki Abba ma bayanan, mai aikinsu ce kawai agidan gaisheta tayi ta wuce daki tai wanka kaya ta chanzo har lokacin tana murmushin rakin Abdallah tafito tai kitchen tana taya yar aikin nasu aiki sukai hadadden girki ma Mum sukai arranging gidan aka share ko ina sai kamshi yake, tafito da kayan wankinta sukai backyard inda washing machine yake ya wanke su ya dauraye ta ciro ta shanya sanan ta dawo dakin lokacin an sakko daga masallacin juma'a hakan yasa tai dakinta taje tai salla, wayarta dake ringing yasa ta mike da sauri ta dauka agaban madubi, Mum data gani yasa tai wani irin tsalle ta zauna akan gado tadau wayar saikuma ta saki kuka tace "Mum tunda kika tafi baki nemeni ba kona kiraki baki dauka why Mum" dan dariya Mum tayi daga ta dayan bangaren tace "sorry my princess, busy nake sosai, meetings nakeyi wlh dawasu investors, apart from hakan ma inaso nasai share wani mutumi a burj al Arab amma sai yanga sukemin wai akwai wasu akasa, yanzu dai how are you? Abban ku told me what happen to you, sorry princess dina Allah ya kara tsaremin ke da protecting dinki kinji" gyadakai tai ahankali tace "Ameen Mum, karfe nawane zaku iso?" "ina princess?" "nan mana Mum, bayau zaki dawoba?" dan dariya Mum tayi tace "haba princess dina ke bakiso Mum dinki ta nemo kudin aurenkine? In aka tashi bikinki namiki biki, biki mai suna biki ba bikiki ba, biki da sai Nigeria da Abuja ta girgiza, kefa nake nemanma kudin nan uhm Apple of my eyes" make kafada tayi a shagwaban ce tace "Mumy ni wlh banaso, please just come back i want to hug you Mum, wlh kullum sainai mafarkin ki" takarashe maganan tana kuka, sosai zuciyar Mum ta karaya hakan yasa tace "kinga ko princess ayanzu haka danake miki magana i don't know yaushe zan dawo ma, cikin kaso goma a abubuwan danazo yi ko kashi uku ban kammalaba, but i promise you, i promise you princess, i will double my effort just for you kadai, dan kawai nagama da wuri nazo nima i miss my baby girl, my one and only baby girl, forget duk brothers dinki are kobo u are d only naira in my life, oya laugh inji" dariya tahau yi hawaye na fita, tana mugun son Mum dinta itace naira rayuwan mum, su Ya Muhsin da Ya Ahmad kobo ne su haha abinda ke kara sata jin dadi kenan, dariyan da Mum taji tanayi yasa ta sauke ajiyar zuciya hankalinta yadan kwanta sosai dan tunda Abba yay fushi yamata text din abinda yasameta dan bata kirasa back ba takasa samin natsuwa, ganin yanzu she's smiling yasa hankalinta ya kwanta sosai, ahankali tace "okay princess i will hang up now akwai inda zani i will try as much as possible nadinga kiranki kullum kinji, no matter how tight my schedules are, I love you" ahankali tace "I love you too Mum saikin dawo" "yauwa yar albarka bye" katse wayar Mum tayi hakan yasa tafada gado tana kukan bakin cikin bazata dawo yauba ahaka bacci yay awon gaba da ita sai wuraren biyar ma ta tashi da sauri ta fada bayi ta dauro alwala tazo tai sallan laa'sar sanaj ta fita ta debi fried rice kadan ta dawo palo rike da plate din ta zauna akan kujera tanaci tana kallon zee world.
Chapter 13 · 0% Book details