← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 63

Sashe 45

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sanyi asuba ne ya farkan dashi daga wahalallen baccin dayayi, ahankali ya kunna wutan dakin dakin yay haske sosai juyo dakai yayi ya kalleta ya kafeta da ido yanda fuskarta da idanunta suka wani irin kumbura fuskan yay ja, ahankali ya matso kusa da fuskar yana wani irin kallon fuskar nata wani irin tausayinta na shigan shi kaman ya dauke mata ciwon yakeji, hanunshi ya mika ya daura akan goshinta zafi yaji sosai alamun tana tattare da zazzabi hakan yasa ya zame hanun yana wani irin jin ciwo aranshi yasa hannu yana gyara blanket din jikinta kafin ya zare jikinshi ahankali gudun karya tasheta ya sauka daga gadon, ahankali yawuce ya shiga bayi wanka yayo sanan yafito daga bayin daure da towel a kwankwason sai wani karamin blue towel a hanunshi yana tsane ruwan kanshi dashi ya tsaya agaban closet dinshi, wani simple white t-shirt yasaka na Givenchy, yadauko wani black wando yasaka ya zira wani flat black palm daya haska white babban kafarshi da kyawawan white kumbunan shi gwanin ban sha'awa, turare ya fesa, jikinshi sai uban kamshi yake yay wani irin kyau kaman mace, lips dinshi da hancinshi sunyi jajir shima sabida kukan dayay jiya gashi shima zazzabi zazzabin yakeji, ahankali ya bude kofa yafito yana kallonta kafin yadau dadduma ya shimfida yahau kai, rakatanil fajiri yayi sanan ya linke yafito daga dakin ya rufo mata ahankali, dakin Omari yafara shiga ya tadoshi sanan ya shiga na Abdallah shima ya tadoshi da kyar yatashi yana turamai baki yace "lemme sleep mana Ya Marwan ai is not yet Time for subhi ko" kunenshi yaja yanadan murmushi, ihu Abdallah yayi yatashi zaune kaman zaiyi kuka yana dafe kunenshi dayaja, ahankali ya zauna kusa dashi ya kama kafadarshi saikuma ya sakeshi ya daure fuska yace "you are sick why didn't you tell me?" girgiza mai kai yayi ahankali saiga hawaye hakan yasa yatashi da sauri zai shiga bayi da sauri Marwan ya rikemai hannu yatashi ya tsaya agabanshi yana kallonshi from head to toe yanda kanshi ke kasa yana share hawaye, ahankali yace "when did you start hiding something from me? Wat is it? Kunyi fada Kaida Omari jiya ne?" girgiza mai kai yayi ahankali hakan yasa yace "den wat is it Abdallah?" yay maganan yana dago habarshi, ahankali bakinshi na rawa sosai yace "Ya Marwan wlh ko, I don't know why but I feel your wife's pain so much, abin nadamuna da kyar nai bacci jiya, please ya Marwan take care of her kaji, kaga yanzu mukadai gareta, she's your wife please ya Marwan love her, banso naga tana wahala, please love her nasan kace you're not in luv but please love her for my sake kaji" dan murmushi yayi idanunshi nadan chanza kala yaja hanun Abdallah ahankali suka zauna abakin gado, cupping face dinshi yayi ya kalleshi shima shi yake kallo dan kawad dakai yayi saikuma yajuyo ya kalli kanin nashi daya kafeshi da ido cikin wani irin murya mai sanyi sosai yace "Abdallah I love my wife so much, starting from the day I saw her awanan hospital, and duk runtse duk wuya I will never leave her alone and I want you to promise me you will keep her company kana janta da hira sabida all her sorrows should varnish ta manta komi, can I count on you to take care of my wife koda bani nan?" gyadamai kai yayi ahankali hawaye nason ya zubomai, dan murmushi yayi yasa yatsanshi ya share hawayen yace "I want to give her a good life, am ready I want to change for her dazar..." yay shiru yana murmushi, ahankali yama Abdallah peck akumatu ya dagashi yace "jekai alwala kazo mutafi mosque" wucewa bayi yayi yana kallon fuskan yayan nashi da duk duniya baida abinda yakeso kaman shi. Omari da tuntuni yake bakin kofan yaji komi ya shigo dakin shima idanunshi yay ja zama yay kusa da Marwan din yana kallonshi yace "what are you telling Abdallah mekake shirin yi Ya Marwan?" yafada yana huci kaman zaiyi kuka, murmushi yamai yace "nothing, but inaso kaje kafara muku processing Visa, u, Abdallah and my wife" zaiyi magana ya dagashi daidai nan Abdallah yafito daga bayin daure da alwala jallabiya yasaka suka fice sukai masallaci.

Inspecta ne yafara bude idonshi arude yana zaro bindiga da sauri daga masakalar bindiga yana pointing gaba, da sauri ya bubbugi na kusa dashi shima ya farka arude yana "yes sir" da hannu ya nunamai gate yace "jeka duba su gen lemme check Alhaji I think kidnapper daya dauke yarinyar ne yadawo" da sauri yay cikin gida kofan dayagani abude yasa ya shiga ciki da sauri yay sama da gudun bala'i yay upstairs yana kwalama Abba kira. "Alhaji, Alhaji" shiga dakin dayagani abude yayi yanabin ko ina da kallo kafin yaga Abba dake kwance da dan gajeren wando jini na fita daga bakinshi da hancinshi a sume ko motsi bayayi da sauri ya buga uban ihu yana kiran sauran polisawan yana dube dube inda zai saman mai riga yasa mai amma bai ganiba, daidai nan sauran polisawan suka shigo daki da sauri suka cucibeshi suka fita dashi suka sashi amota sukakaishi wani hadadden private hospital da sauri aka karbeshi aka dukufa akanshi likitoci na kokarin ceto rayuwan shi, inspecta kuma yafita dan kiran commissioner.
Chapter 45 · 0% Book details