← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 63

Sashe 37

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wuraren takwas nasafe Abba ya shigo gidan parking yayi a parking space ya sauko daga motan ya shigo part dinsu, zaune yaga Mum afalo taci uban gayu na manya mata tai kyau sosai tana kallon tv kana ganinta kaga tsantsan damuwa akan fuskarta dan bama tagane me ake fadi a tv, sallama yayi ciki ciki hakan yasa ta dago kai ta kalleshi dauke kai yayi yawuce ciki yana kallon kofan dakin Nadeera kaman ya bude ya ganta haka yakeji, bude kofar dakinshi yayi ya shiga yay bedroom dinshi direct kafin ya shiga bayi ya sakinma kanshi ruwa ya mikar da hannayen shi ya dafa bango yana tunani, ko duka duniyan nan ya mallaka zai iya bayarwa inhar zaigano inda princess take d biggest problem in trying to track down her location according to abinda commissioner yace is because bata tare da waya da an iya anyi tracking down location dinta sharp sharp, gashi bai samu yaga inda koda hanyar gidansu ba balle yabada any clue dazaisa agano inda take easily, inda ace yasan sace princess wanan mugun zaiyi daya shanye koma me yake damun shi aranan yahakura, gashinan duk binta dinan dayayi ne yaja wani banza chan ya aureta, runtse ido yayi da karfi ya daki bango yana cikin zafin rai yana fata dakuma rokon Allah akan karya bashi daman tabamai princess harsai angano inda take tadawo gida araba dan iskan aurenta dayayi. Yabata kusan one hour abayi tunanin yanda zaiga princess yake sanan ya kashe shower yabude kofa yafito daga bayin Mum yagani zaune abakin gado hakan yasa ya dauke kai yay gaban wardrobe wani goggagen shadda gizna brown ya ciro ya shiga sakawa ahankali Mum tace "a ina ka kwana jiya Alhaji?" ko kallonta baiyiba saima karasa zira riganshi yayi yay gaban madubi yadau mai yana shafawa tasowa tayi tazo wajen tana binshi da kallo tace "ina kaje Alhaji, a ina ka kwana?" ko kallonta baiyiba danji yayi yanxu koson ganinta bayayi daukan turaren shi mai shegen dadi yayi zai fesa Mum ta fizge cikin fushi ta jefar akasa yafashe tace "nizaka maida mahaukaciya nace ina kaje?" wani irin mugun kallo yamata kafin yay controlling kanshi yace "naje neman abin sona, yata Nadeera, my princess, the apple of my eye, My love" cikin wani irin kunan rai Mum tace "Alhaji wai dan Allah lafiyan ka lau kuwa kokuma you are posses ne nakira malamai ama ruqiya, this isn't you" wani kallon rainin wayo yamata kafin ya dauko wani sabon turare zai fesa takara fizgewa cikin kunan rai tace "Alhaji talk to me wai menama ne? Dan Allah kabar wanan wasan dakake min i know you are joking ko dakace zaka auri Nadeera, nasan nama laifuffuka da dama, jiya nakasa bacci tunanin abubuwan danake ma nayi and nai concluding maybe zakai punishing dina ne you want me to realize my mistakes shine kake cewa u wanna marry princess, Alhaji yanzu kamin bayanin auren dakace kamata da gangster din dakace musan yanda zamuyi mu kwatota because i know wasa kakemin da xancen sonta kake xaka aureta ko Alhajina?" wani irin kallo yamata from head to toe kafin yaja tsaki yace "ina ganin too much business da tafiye tafiye yafara affecting yanda kike tunani ko Hajara, now bari namiki bayani daki daki kiji ki fahimta, zauna kiga" ya wani irin ingiza Mum kan gado ta zauna ya tsaya agabanta ya nuna kanshi yace "ni dai ni dinan uban yayan ki Muhsin da Ahmadu Alhaji Naseer Aluminum Son yarmu Nadeera nake, dazaran an ganta kinajina? Zan shigar da kara kotu zan raba auren inje masallaci a aura mini ita mubar muku kasar Spain zamu, jibi Hajara inama Princess so dakoke dakina budurwa ban miki irinshi ba, ke ina gaya miki princess yar baiwa ce, wato Allah yay hallita ne awurin nan, tafimini ke sau miliyan kan miliyan, Allah yay kira, yay zubi awajen nan, yatace idan na aureta sai yanda nayi da ita dama gata dajin magana very innocent girl wlh ba irinki ba dakika nunama duniya kinfi karfina, bari kiji kin riga kin shani na warke raras, auren Princess zanyi ke bakiga yanda muka dace bane jibifa sunayen mu Naseer da Nadeera wayyo Allah na" yay maganan yana wani irin shafa kirji yana kallon sama yana wani irin murmushi daya bayyana fine set of teeth dinshi, salati kawai Mum take aranta dan gani take kaman tabin hankali Abba yasamu, kallonshi tayi tace "Alhajina kodai tsufa ne yafara kamaka muje asibiti ne?" wani irin ihu Abba yamata kaman zai daketa yace "ni kike cema tsoho? Kibari mufara aure nida princess ta haifamin twins kafin kice nai tsufa, kinma tunamin lemme call commissioner yace dama nabashi yau da gobe lemme call him inji how far about princess dina, in sha Allah sai an ganta in sha Allahu saikinga aurena da princess, banyi baccin dareba jiya Allah naketa kaima kukana da yardan ubangijin al'arshi princess zata bayyana zakiga aurena da Princess hajara, agaban ki direba sai tuka mota yakaimu airport mu barmuku garin, nama mata order Lamborghini duk randa tadawo shi zan bata as gift i really really miss my baby girl" cikin Wani irin mugun kishi da gushewan tunani Mum tace "in sha Allah, da yardan Allah baza aganta ba, indai niyyarka kenan da yardan ubangiji bazaka sake saka princess a idanun nan nakaba in sha Allah kagama ganin Princess aduniyan n..." wani irin mugun mari Abba ya dauke ta dashi dayasa tasaki wani irin wawan ihu dan ya mugun shiganta, Muhsin da Ahmad dasuka shigo dan gaida Mum sukaji ihun ta shigowa dakin sukayi da gudu, tsayawa sukayi suna kallon Mum data dafe kuncin ta tana kuka sosai tana kallon Abba, ga Abba tsaye akanta yana huci kaman zaki yana ganin su ya nunasu da yatsa kafin ya nuna Mum yace "kuma maman ku magana tafita daga idona, ta kiyaye ni inhar tanason aurenta and you Muhsin" yanuna Muhsin da idanunshi sukai jajir yana sanye da black suit hanunshi rike da necktie yace "yes, yes, yes, I know kunsan komi by now kunga komi kunga komi ta CCTV footage, dat is why kuka tsaneni haka ko gaisuwa bani samu daga wurin ku kuma nagode da hakan bakomi yasani aikata hakan ba uwarku ce tajamin ita tajefani halaka amma yanzu nasan maganin matsalata, Muhsin start with divorce proceedings wanan dan daban daya dauke Nadeera shiyasa akazo har gida shekaran jiya aka daukeni yasa nabashi aure Nadeera aka daura auren akan sadaki 200k, yanzu kwamisona yace nabashi yau da gobe Nadeera zata fito, once sun ganota tadawo gida zamu maka dan shegiyan dan ta'addan a kotu mu raba auren nasu na aureta, kufada ma mahaifiyar ku tun wuri tai karatun ta natsu dan wlh aurena da princess babu fashi, and duk randa tasake maganan banza akan Princess dita wlh abakin aurenta, i can fight the whole world for my babygirl inhar war ne am ready kota gabas kota kudu kota yamma kota arewa zanyi fighting, me and my princess mutu karaba takalmin chicken" kuri Muhsin yayi yana kallon mahaifin nashi tun yana gane meyake cewa haryaji zuciyarshi ta tsaya chak ko kadan baya ganin kowa sai duhu, daga Abba dake ta bambamim bala'i dabayaji yanadai ganin bakinshi na motsi sai Mum dake zaune kan gado da Ahmad dake kallon Abba yanaji kaman ya tsireshi basu lura da Muhsin ba kawai karan fadin abu sukaji da sauri kowananesu ya kalli inda yaji karan atare dukan su sukace "Muhsin" gabaki daya idanunshi sun kafe yana kallon sama baya numfashi ko digi.
[9/13, 11:52 PM] Lady: *this book na kudine if you are interested chat me 07012181461*
Chapter 37 · 0% Book details