Sashe 58
Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Yawani yi irin tsalle yayo kanta zai tareta yaga wasu fararen hannayen dake sanye dawani irin hadadden agogon mai tsada sun tare Nadeera, tundaga kafan mutumin Abba yakebi da kallo yana zaro ido inda yaga yasaka wani hermes half cover shoe na maza black, sai shining yake zuwa dogon wandon yadin jikinshi dakeda wani irin hadadden karin guga, dawani irin sauri yakara sa dago kanshi duka ya mike tsaye yana maida hanunshi baya yana kallon mutumin dake rike da Princess da baida bambanci da ba indiye ya kafe coil hair dinshi dake wani irin shining da kallo ganinshi kaman balarabe, ahankali ya daura hannunshi akan kumatun Nadeera yana dan tapping yana bubbugawa cikin damuwa bude idanunta dasukai jajir tayi tawani irin fashe da kuka tana kallonshi, girgiza mata kai yayi tareda dagata ahankali ta mike tsaye ta kalli inda Ya Muhsin ke kwance wani irin kuka na taso mata kafin ta shiga dakin da sauri tsabagen rudewa ko Abba dake tsaye agefe bata gani ba ta zauna agaban Ya Muhsin Abba shima ya shigo dakin da sauri yana kallonta, takai hanunta dake rawa sosai ta yaye ta bude fuskarshi tana kallo, taushe bakinta tayi wani irin kuka yataso mata kaman zata suma tace "noooooo, Umm Umm wanan ba Ya Muhsin dina bane, Ya Muhsin, innalillahi Ya Muhsin dan Allah karka tafi ka barni kaji" ta fashe dawani irin kuka tana kallonshi, ahankali Marwan yakarasa shigowa dakin batare daya kalli koda fuskan Abba ba su Abdallah biye dashi ya samu daya daga cikin kujerun dakin ya zauna su Abdallah a gefenshi yana kallon yanda Nadeera ke kuka abin nataba shi, da muryanta datai rauni sosai takira sunanshi. "Ya Muhsin, Ya Muhsin, Mummy, Mummy dan Allah kicemai yatashi" ta kalli Mum dake kuka itama, sake kallon Ya Muhsin din tayi tana wani irin kuka kafin ahankali tana girgiza mai kai tace "Ya Muhsin ai baka mutuba ko, suna cewa kamutu please katashi dan Allah" tai maganana cikin wani irin tone din kuka hawayen datakeyi yana diga akan fuskarshi, ta daura hannayenta duka biyu akan fuskarta tarufe fuskarta tana wani irin kuka kaman zata sume hawaye nabin hannayenta, sosai Marwan ya kafeta da ido kafin ahankali yasauke idanunshi akan Muhsin data budema fuska, hujin hancinshi ya kafe da ido ko kyaftawa babu kafin ahankali ya mike tsaye ya tako zuwa wajen duk aka bishi da kallo ya tsugunna agaban Muhsin ahankali ya kara yatsarshi daya a saitin hancinshi, tsabagen kukan datakeyi bama tasan da mutum awajen ba, ahankali yasa hannu ya yaye bargo yacire gabaki daya ya ijiye agefe, gabaki daya aka dago kai aka bishi da kallo, dago Ya Muhsin da jikinshi yay sanyi sosai yayi ya jinginashi a kirjinshi da sauri Abba yace "kai wanan balaraben lafiyan ka? Bakaga wanka za'amai yanzu ba kawani dagashi haka" ko kallon Abba baiyiba ya daga kai ya kalli Ahmad dayake kyautata zaton kanin Muhsin din dan yaga kaman, Ahmad dinma kallonshi yake da jajayen idanunshi cikeda mamaki ahankali yace "ban zamzam water, I can feel his pulse" da sauri Mum da Bello da Abba duk suka dawo wajen suna zare ido suna kallonshi, wani irin nishi Abba yayi yace "Ahmad je dakina akwai ruwan zam zam dayawa ka kwaso duka ma kakawo" dawani irin gudu Ahmad yafita daga dakin yaje dakin ya kwaso ruwan zamzam da gudu ya dauko wuka a kitchen mutane sai kallonshi suke yadawo ya bude yamika ma Marwan ahankali yay addu'a ciki ya kafamai abaki yadan shiga bakinshi sanan yamika ma Mum ta karba yace "he's alive, I think doguwar suma yayi dayasa heart dinshi yadena aiki, he need breeze" da sauri suka mammasa baya, da sauri Nadeera tacire hanunta daga fuska tawani irin rarrafo tazo gaban Ya Marwan din dake rike da Muhsin ta dafa cinyar Ya Muhsin arude takira sunanshi cikin kuka tace "Ya Muhsin, Ya Muhsin" ahankali bayan idanunshi sukai wani irin rawa batare daya budesu ba wani irin kabbara akai adakin Allahu Akbarrr!!! Wani irin fadawa jikin Ya Muhsin din tayi tafashe da kuka sosai tana kiran sunanshi. "Ya Muhsin Open your eyes kaji, dan Allah kabude idanunka ganinan nadawo, gasu Mummy na" sosai Marwan ke wani irin kallonta ahankali Muhsin yakarasa bude idonshi duka ahankali yana kallon yan dakin dai dai, Mum dinshi yafara ganin da fuskarta gabaki daya tai jajir, gefen bakinta afashe tana kuka tana kallonshi, kafin ya kalli Ahmad da shima idanunshi sunyi ja, sai abokin Ahmad Bello dake gefenshi hanunshi rike da farin yadi da turare, sai Abba dayake atsaye shima yay zuru zuru yana kallonshi kaman ya sami tv, saikuma wasu mutane biyu dake kan kujera masu kama da larabawa suma suna kallonshi, saikuma wani mutumi wanda yake limamin anguwan su yasa hand glove a hanunshi ya tattare hanun riga yana kallonshi shima murmushi kan fuskarshi, sai kuma wani karan kuka da yakeji da kuma alamun mutum dayaji akan jikinshi, ahankali yana dan layi ya dago daga jikin Marwan dayake kai ahankali yana daga hanunshi da kyar yana dafa kanshi, da sauri Ahmad ya rikeshi muryanshi na rawa sosai yace "Ya Muhsin, My brother" da sauri Bello ya ruga da gudu yafita daga dakin yana ihu "doguwar suma ce, jama'a doguwar suma ce, da ranshi, kafin ma aamai wanka yatashi, doguwar suma ce wlh" sosai ake binshi da kallo mutane nayin hanyar shashinsu ana lekasu, ahankali ta dago da rinanun idanunta ta kalli Ya Muhsin dake numfashi sama sama ahankali cikin muryan kuka tace "Ya Muhsin" fadawa tayi jikinshi tawani irin kankameshi tana kuka sosai sosai kaman zata shide, ahankali Marwan yatashi yakoma inda yake kusa da kaninshi ya dukar da kanshi kasa yanadan bubbuga kafa daya akasa, tsaki Abba daya cika fam yayi ya kalli Nadeera data rungume Ya Muhsin daketa tapping bayanta yace "ke Princess sakeshi, cikashi nace" ya kalli su limam yace "Imam nagode sosai, sai nazo har gida yima godiya, zamu maidashi asibiti yanzu ne" ya mikama Imam hannu yana kallon Bello yace "Bello zo tatttara makaran kutahi dashi" gyadamai kai Bello yayi ya shigo yadau komi yafita imam nagaba, Abba ya kalli su Marwan yace "larabawa naga ku kuka dawomin da princess ko aiko nagode sosai, a ina kuka ganta? Ya akayi kuka rabata da wanan dan iskan terrorist din? Anyways nagode nagode yanzu Princess dina tadawo gida, Dana kuma yafarfado komi ya daidai ta, wlh am so happy my princess is back" yay maganan yana kallon Nadeera dahar lokacin kuka take ajikin Ya Muhsin amma kasa kasa, Muhsin kuma ya lumshe ido natsuwa na shigan shi ahankali abubuwan dakemai ciwo ajiki yanaji suna denawa, zuciyarshi datamai nauyi sosai da zafi da yaji ya dena, cikin fushi Abba ya tsaya akansu yace "wai bazaki sakeshi ba Princess?" dan murmushi Muhsin yayi yadago Nadeera, ahankali ta taso daga jikinshi tana kallonshi ahankali ta koma gefenshi tai lamo ta daura kanta a hanunshi ta rike hanunshi gam tana share kwalla idonta, wani irin buga kafa Marwan ya shiga yi da sauri da sauri yawani irin dunkule hanunshi yanadan fuzar da iska Omari daya gama lura dashi ne ya daura hanunshi akan cinyarshi yay patting batare dayay magana ba, ahankali Mum da tuntuni Muhsin take kallo ganin Abba zai fara hali ga danta ya farfado yasa ta kalli Nadeera tace "Princess tashi kutafi" "ta tafi? Ta tafi ina Hajara?" Abba yafada cikin ihu, saikuma yay tsaki yace "nasamu Princess ta dawo wayan nan yan arzikin irin albarka masu kama da larabawa da banmasan a ina suka ganta ba, sun dawo min da ita shine zakice ta tashi ta tafi ta tafi ina? Eh, nace ta tafi ina yar bakin ciki?" da sauri Ahmad yatashi ya kalli Abba dawani irin jan ido yace "Alhaji Naseer please don't start with this your trash, kamana shiru anan inbadai so kake ka kara kai danka lahira ba, kamana shiru and respect your self" wani irin matsiyacin kallo Abba yama Ahmad yace "Ahmadu ni agidana, gidan dana gina da kudina ne kake cewa namaka shiru? To kaci gidanku, dan uwatata anki ayi shirun, anyways ina cikin tsananin farin ciki banison bacin rai, am so happy my baby girl is back" yay maganan yana kallon Nadeera da ta rirrike hanun Ya Muhsin daya lumshe ido yanajin tsanar mahaifinshi aranshi, karasowa wajen Abba yayi ya mikoma Nadeera hannu yace "zomu tafi Princess, yauwa yar albarka zomu tafi" make mai kafada tayi a tsorace tasake kankame Ya Muhsin wani irin tsoron Abba yake bata yanzu, tsugunnawa Abba yayi agabanta yana washe mata baki yace "haba my baby girl, my one and only princess, yarinyar Abban ta, yarinyar kirki, princess din babanta, zo kinji kidena tsorona, iyye kamota kamota, yar duma duma taaa, my chubby chubby gurl, sangandaliya gandaliya ta, haba princess din Abban ta, kinga ko namiki order Lamborghini tama kusa isowa Nigeria ta jirgin ruwa za'a kawo, Kinga yanzu yanda kika dawon nan kotun zamu shiga za'a raba auren ki da danta shegiyar nan saimuyi auren mu musha amarci ko princess mubar musu garin muje Spain honeymoon abunmu" wani irin kuka tafashe dashi da kyar ta juyo kai tadan kalli Abban tace "Abba na wai mena mane? Kataba ganin inda akai aure tsakanin uba da y'a, Mummy, Ya Ahmad, Ya Muhsin" ta kalli Ya Muhsin daya dan bude idanu kadan ya kalleta, girgiza kai tayi tana goge idanunta da bayan hanunta tace "Abba natamin abinda yaga dama kunki mai magana ko, bakaji meyake cewa ba uhm? Tayaya zan auri babana an taba hakane? Is Abba okay? Kaman baida lafiya mu kaishi asibiti please Mummy na" ta karashe maganan tana kallon Mum da idanunta sunyi jajir, cikin tsananin fushi Abba ya nuna kanshi yace "ke dan uwatata ni kike cema banda lpy akaini asibiti? Kin dauka hauka nake kome iye? To bari kiji nafada miki lafiyata kalau, bani na haifeki ba Princess" da sauri Nadeera ta dago kai ta kalleshi, yace "eh bani na haifeki ba, Mummy dakike gani nan ba ita ta haifeki ba, Muh..." da sauri Ahmad yawani irin kirashi yace "Naseeru!" dakuwa Abba yamai yace "uwataru ne ba Naseeru ba, shegen yaro mai kama da sangami" ya kalli Nadeera da idanunta ke kyam akanshi yace "Muhsin dakike gani ba wanki bane, Ahmad ma haka, a gidan marayu muka dauko ki a eygpt tun kina yar wata uku muka dinga rainanki, da kudina namiki suna na rada miki Nadeera, na kaiki asibiti, na raineki nai kewonki har kikai girma haka, kikai kyau, bakutu dake, shine kuma zan barma wani ke ya more aikina?" wani irin kallon Abba take kirjinta nawani irin bugawa, ahankali ta saki hanun Ya Muhsin ta juya ta kalli Mum da ke kallonta zatai magana Mum ta rigata tace "yes princess hakane we are not your biological parents, adopting dinki mukayi daga motherless home, and Abdallah da Omari" tamata pointing su Abdallah dake zaune kusa da Marwan da kanshi ke kasa tace "are your biological siblings, sanan Marwan your husband is your cousin, munso mufada miki mijinki yace ki warke tukunna, all I know shine u will always be my daughter, my baby girl my princess okay, tashi kibi mijinki kutafi" wani irin gangarangan maganan yamata akai gabaki daya zuciyarta yakasa containing d shocking revelation she just heard, na Abba bata yarda ba amma na Mum kam ta yarda, maganan Abba ne yadawo da ita daidai yawani irin tsalle ya tsaya agaban su Abdallah yana kallon Mum yana cewa "waye Marwan din cikin su, au dama kune? Ina masks din dakuke sawan? Har gidana kuka shigo sabida kun isa, Hajara nunamin ina Marwan din wlh saina zubar mai da hakori yanda ya zubar da nawa, saina mai lilis na rantse and saiya saki princess kafin yabar gidan nan nahada shi da hukuma" yay maganan yana wani irin tattare hanun riga sama, wani irin smirking Mum tayi Muhsin yabude idanunshi tass yana kallon mahaifin nashi, Nadeera ma kallon Abba take daya gama tattare hanun riga yawani irin wage kafa yana nuna musu power yana kallon su ukun yana huci, wani irin fashewa da dariya Ahmad yayi, dariyan da rabonshi da yinta tun jiya yace "dan girman Allah koma waye Marwan cikin ku dan ya rasulullahi kuma wanan tsohon shegen duka, wlh kaji kunya Naseeru" juyowa Abba yayi ya kalleshi ya nuna shi da yatsa yace "banga laifinka ba Ahmadu, dama chan tsinanne ne kai, tsinuwar kesaka yin haka mai kama da uwatata" ya kalli su Abdallah yace "waye Marwan cikin ku nace, wlh kodai yatashi mubama hammata iska kokuma zanyi rushing dukan ku uku, and saikun sakin mini y'ata yau" yawani irin gyara tsayuwa yana gyara kafa yana shirin yin gusha gusha kaman irin dan Chinese dinan yay wani irin ihu yace "dan uwatata nace Marwan yafito muyi fito nafito dan wlh saina rama dukana dakuma asiri dayamin yasa nabashi auren princess bana hayyacina, dan uwatata da ubatata Marwan ka mike tsaye kazo mubama hammata iska" ya juyo ya kalli Nadeera dake wani irin kallonshi yace "don't worry princess I can take them down, ina mugun sonki princess da I can do anything for you, I love you so much my baby girl, don't worry kinji" yajuyo yana wani irin gyara tsayuwa yana kallon su yace "Marwan ka mike mu fafata nabaka kashi wlh, sai kasan ka tabani, uban wayace ka auremin y'a? Wlh saina zubar ma da hakora, ka mike kona hadaku ukun na rushing dinku".