← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 63

Sashe 7

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda polisawa sukazo yan asibiti da students suka taru sakamakon yanda motocin su ke kuka, hana kowa hawa stairs din sukayi akai sama, Fauzy da dawowan ta kenan daga kai matar Blood bank taga polisawa sunyi sama gabanta ya shiga faduwa ta shiga tambayan students din wajen ina Nadeera dan azatonta harta dauko folder tadawo zata wuce common room kenen kaman ance ta daga kai taga polisawa guda biyu nawani irin jan Nadeera dakd kuka suna saukowa gashi sunsamata handcuff, salati Fauzy tayi hawaye na gangaro mata tai bakin benen da sauri tana tuttura mutane tace "Nadeera wat happen" kafin ma tai magana polisawan sunyi waje da ita, goge hawayen dake zubo mata tayi da gudu tai common room dinsu jakarta ta bude hanunta har rawa yake taciro wayarta ta kunna contacts ta shiga tafara dubo number yan gidansu, na Ya Muhsin tafara cin karo dashi hakan yasa tai dailing number shi, har yagama ringing ya katse bai dauka ba tamai na biyu ana ukune ya dauka ahankali yace "sis ya kike?" cikin tsananin tashin hankali tace "Ya Muhsin anyi arresting Nadeera" takarashe maganan muryanta na rawa sosai kuka na neman kufce mata "what! Mene?" Yafada yana mikewa daga kan kujeran office dinshi, gyadamai kai tayi kaman yana gabanta, cikin kuka tace "eh anyi arresting dinta yanzunan polisawan suka wuce da ita, i don't know what happen amma har handcuff sun samata a hannu" katse kiran yayi yadau car key dinshi dake kan table yafita daga office din yana gyara zaman tie din wuyanshi, lift yashiga ya kaishi kasa ya fita yay parking space da sauri ya shiga mota yaja yafita daga building din, tafiyan dabazai wuce na 15 minutes ba yakaishi police station din dayake kyautata zaton nan aka kaita danshine wanda yake close to hospital dinsu, parking yayi yafito yana gyara zaman black suit din jikinshi daya kara fito da kyanshi da kamaninshi da Mum, shiga police station din yayi gabaki daya ranshi abace, police din dake gaban kanta yasama yace "anan aka kulle Nadeera Naseer?" "bari na duba yallabai" bude book din gabanshi yayi yana dubawa kafin ya dago yace "eh nanne amma inkanaso ka ganta saikabi ta hanun Inspecta Aliyu Alkali, bari namai magana" da sauri ya juya yay hanyar office din da aka rubuta inspector ajiki, gabaki daya boiling yake yana girgiza key motar hanunshi yanadan bubbuga kafa akasa, ko minti biyu ba'ayi ba police din yadawo yace "you can go in yallabai" sa kai yayi ya shiga ciki bude kofan office din yayi ya shiga office din yakarasa gaban table din yana kallon Inspecta Aliyu da shima kallon Muhsin din yake, batare daya zauna ba yaciro ID card dinshi ya nunamai yace "Barrister Muhsin Naseer, Am Nadeera's Lawyer and brother as well, on what charges kai arresting sister na? And as her lawyer i demand to see her" gyara zama yayi Inpecta yayi yana kallonshi, ajiye pen din hanunshi yayi kan table yahade hannayen shi yace "munyi arresting dinta sabida tai injecting patient which happen to be the minister of finance dayay hatsari kwanakin baya yasamu bugewa akai da deadly substance, ur sister ka kira ta ko? Ko client dinka nema whatever dai try to intentionally murder a patient daga aikenta zuwa dauko folder, dazaran mun soma interrogating dinta saita dinga mana suman pretense" wani irin kallo Muhsin yamai kafin yace "inaso na ganta nace" "sure" Aliyu Yafada tareda mikewa yadau hulan polisawan shi dake kan kujera ya kafa akai yadau kulkin shi yana wani irin bubbuga wa a hanunshi ya zagayo ya kalli Muhsin yace "follow me" fita yay daga office din Ya Muhsin biye dashi, wani lungu sukabi da cells daban daban da aka kukkulle mutane aciki suke, agaban wani cell ya tsaya ya zare uban keys din daya makala jikin wandonshi ya ciro daya yabude makullin cell din dashi yabude kofan, dakine dababu komi aciki sai simenti saikuma dan dakali haka dawani wash hand basin dayay baki dake gefe, tana zaune akasa ta jingina da bango ta cusa kanta acinya tana kuka farin kayanta duk sunyi stain din datti.
Da hannu ya nunamai cikin cell din yace "gatanan" hakan yasa Ya Muhsin yatako zuwa wajen ya tsaya ajikin kofan yana kallonta sosai heart dinshi yay breaking, ahankali yace "Nadeera" dago fuskarta da hawaye yagama wanke wa tayi jin muryan Ya Muhsin ta kalli Yayan nata idanunta tsabagen kuka har kumbura sukayi wani irin tashi tayi jiri na dibanta tayi kan Ya Muhsin da gudu, fadawa jikinshi tayi tafashe dawani irin kuka mai kara tana shesheka, patting bayanta yayi yace "is okay, stop crying" dago kanta yayi jin yanda jikinta yay zafi sosai yana kallon fuskarta ya tura hannu a aljihun shi yaciro handky, share mata fuskarta tass yayi yace "stop crying, tell me what exactly happen?" rirrikeshi tayi tana nishi tsabagen yanda kuka yaci karfinta tana kokarin magana heart dinta na racing ta kasa ita tsabagen yanda zuciyarta ke gudu kaman zai fito ta baki, tunda take bata taba shiga irin tashin hankalin nan arayuwanta ba ita a police station no, agabanta aka karya mutane biyu dazu, kokarin yima Ya Muhsin bayani take takara tafiya luuu zata zube akasa da sauri ya tarota jikinshi yana kiran sunanta "Nadeera, Nadeera" shiga cell din yayi sosai ya zauna kan dakalin tana jikinshi tapping fuskarta yayi adan rude yace "Nadeera, Hey, Princess" "ahap kaga abinda take tamana kenan tunda muka kawota, dama idan criminal yay committing act aka kamashi he always come up with stuff like this dan mu tausaya musu mu..." "will u shut d fuck up and get me water bakaga ta sumaba ne?" Ya Muhsin yay maganan angrily, wani irin kallo Inspecta yamai yace "suman pretense ba, zama ta farfado ne bata bukatan ruwa" wani irin mugun bacin rai ne ya dira a zuciyan Ya Muhsin ya kalli Inspecta dayakeji kaman ya shake shi yace "am gonna sue you for this, i will sue you for breaching human rights, tanada right tai accessing health care and medication, she's not doing well and u people ignore that calling it a pretense" dan sosa kai inspecta yayi ganin yanda Ya Muhsin is serious kuma yasan gaskiya ne duk abinda yace, dan sassauta murya yayi yace "to ai naga she's a nurse ne she can help her self?" wani kallo Ya Muhsin yamai hakan yasa yace "fine am sending water for her now" yajuya yabar wajen hakan yasa Ya Muhsin yasake tapping kumatun ta yace "princess open your eyes, Nadeera" daura kanta yayi akan kafarshi ya tattare karamin hijabin ta dasuka gama jikawa da ruwa, cirewa yayi hakan ya bayyanar da kananun kalabanta datai parking ya shiga pipitata da hijabin daidai nan wata police woman ta shigo da bottle water ta bashi da sauri ya karba ya bude ya debo ruwan kadan a hannu ya yayyafa mata a fuska hakan yasa ta bude ido dasukai ja ahankali tana kallonshi asanyaye tana sauke ajiyan zuciya, murmushi yamata yace "hey karki kara suma am here, karki karajin tsoro" handky yasa ya goge mata fuskar tass ya dagata, fashe mai da kuka tayi tana rikemai hannu tana kallon kofan cell din, kankameshi tayi sosai tafashe da kuka tana kallon kofa tace "Ya Muhsin dan Allah karka tafi kabarni wlh karya mutane sukeyi, agabana suka karya ma wani hannu, wani kuma kafa" takara she maganan tana wani irin nishi zata sake suman hakan yasa yace "Nadeera look" bottle water ya kafa mata abaki dan yanda lips dinta suka bushe shows she's dehydrated da kyar tasha ruwan sanan ya ijiye yasa kanta akan kafadarshi yana shafa kanta hakan yasa tasomajin natsuwa sunfi 2min ahaka sanan ya saketa ya kamo habarta yace "fadamin maiya faru no more cry babu abinda zasu miki am here" gyadamai kai tayi kafin ta shiga bashi labarin komi. "Ya Muhsin BOYAYYEN MUTUN dinan ne, i have nothing to do with all wat they're saying wlh" "is okay tashi muje" dagata yayi yadau hijabin ta yasaka mata ya kamo hanunta yarike ganin yanda kafafunta ke rawa suka tafi office din inspecta, kafesu da ido Inspector Aliyu yayi harsuka karaso gaban table din ya zaunar da ita akan kujeran gefenshi, kallonta yayi yace "tell him wat you saw" gyadamai kai tayi tana kokarin hana kanta hawayen dake shirin zubowa ya juyo ta kalli Inspecta dake kallonta tafada mai duka abinda yafaru, murmushi yamusu yace "to tayaya BOYAYYEN MUTUN din dakike cewa yawuce 2 security dake bakin passage din yaje dakin? And how did he get out batare da kowa ya ganshi ba? Koshi aljani ne?" hawaye ta share tace "wlh am saying d truth ba karya nakeyiba" ganin yanda takeyi yasa Ya Muhsin yace "since the patient is still alive inaso nai bailing dinta" hulan kanshi yacire yace "okay fine amma with the condition duk lokacin da muka bukace ta zaka bayyanata, anytime her presence is required she will appear" jiyayi kaman ya buge bakin dan iskan inspecta, cije lips yayi yace "fine!" bail documents yatashi ya dauko yabashi yace "sign" byro yaciro Nadeera na binshi da kallo yay signing sanan ya mikamai takardan mikewa yayi ya dagata yarike hannunta sukai kofa. "bye queen of suma" wani irin kallo Ya Muhsin yamai itako ko juyowa batayi ba hakan yasa Inspecta yay dariya yace "Yayan mu zaka bani ai ko dan gaskiya ina ciki" wanan kara juyowa Muhsin yayi completely yana rike da hanunta ya kalleshi nakusan 2min fuskarshi babu alamun wasa yace "stay within ur limit" yaja hanunta tareda bude kofan suka fice a kanta suka hadu da Abba da Ya Ahmad dake tsaye suna jiran Muhsin dan police din wajen yace musu lawyer ta yariga yazo hakan yasa suka gane Fauziya ta kira Muhsin kenan shima, kafinma su karaso Abba da Ya Ahmad sukai wurinsu hankali tashe suna kallon yanda Nadeera tadawo mara lpy mara lpy, fadawa jikin Abba tayi ta fashe dawani kukan, Ahmad ya kalleta sanan Ya kalli Ya Muhsin yace "what happen bro Fauziya ce dukta kiramu tace anyi arresting dinta" yatsine fuska yayi yana kokarin ciro phone dinshi daga aljihu yace "is a long story muje gida kawai, Abba mutafi" "kagama komine?" Abba yay maganan yana share mata fuska tareda rike mata hannu, ahankali yace "eh nagama kuwuce da ita gida am going to the hospital now" fita duk sukayi atare Abba da ita suka shiga bayan motar Ya Ahmad ya Ahmad kuma ya zauna a mazaunin driver shikuma Ya Muhsin yay wurin motarshi ya shige yaja yay dan zuwa hospital dinsu.
Chapter 7 · 0% Book details