← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 63

Sashe 55

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_Oh no m Shakur ba Abban ba ba Mum dinba dukansu mahaukata ne rubabbu._
[9/23, 10:15 AM] +91 88002 49616: *Karki karanta in baki biyaba*

*Maman Abd Shakur*

Adaidai lokacin nurse din ta shigo da gudu tana gunguro defibrillator din ta tsaya chak agaban gadon tana karanta machine din dake hade da gadon Muhsin tana kuma kallon patient din da idanunshi suka koma sama, daga kai tayi ta kalli Dr din da ahankali ya zame hanunshi daga kan kirjin Muhsin ya dagokai ya kalli nurse din tareda girgiza mata kai yakai alamun bashi kuma, hannunshi ya daura kan fuskarshi Ya Muhsin ya rufe idanunshi ahankali tareda jan farin bargon gadon yarufe shi ya juyo ya kalli Abba da Mum dake wani irin numfashi da sauri da sauri sunyi suman tsaye ko kyafta ido basayi kallon Muhsin da aka rufe suke ba kakkautawa, cikin tsananin fushi Dr ya kalli Nurse din yace "get his folder from my office time of death 4:30PM" ya kalli Abba da Mum da babu wanda ya iya wani kwawkwaran motsi cikin su yace "I hope you guys are happy now kun kashe danku" yay pointing Mum da yatsa yace "I made it clear to you ranan dakika zo office dina cewa yaron nan bayason any type of hayaniya, bayason damuwa karku, bayason tashin hankali, karku daga mai hankali kark..." bude kofar dakin akayi hakan yasa Dr yadaga kai ya kalli kofan Ahmad ne ya shigo kaman wani abu ya wurgo shi idanunshi sunyi jajir yabi su Mum da yaga fuskarta akumbure da jini da kallo kafin ahankali ya juyo da kanshi ya kalli gadon dayaga an lullube Ya Muhsin da bargo harkai.

Tsaki Dr yayi cikin bacin rai yace "da girman ku, da girman ku, manya daku xakuzo kuna dambe agaban danku mara lafiya, a hospital for dat matter, ku yarane? You guys are very very selfish my God, anyways the damage has been done already, kuzo kuyi clearing komi kokuma nan da 10min zan aiko awuce dashi mutuary" yajuya yabi ta gefen Ahmad dako motsi yakasa yana kallon Muhsin dake alullube, fita Dr yayi hakan yasa Ahmad yadaga kafa ahankali kaman mai matsala a kafa yakarasa jikin gadon ya tsaya chak kafin ya mika hannunshi dake rawa sosai ya daura akan bargon yaja kasa nan yaga fuskar Muhsin da zufa kekan goshinshi idanunshi a lumshe, wani irin faduwa yayi akan guiwowinshi kaman mara lafiya ya fashe dawani irin kuka ya daura kanshi akan gadon yace "innalillahi wa inna ilahi raji'un, Ya Muhsin! Ya Muhsin! dan Allah karka tafi ka barni ni kadai dawayanan mutanen we called our parents, Ya Muhsin you are my strength, my support system, my guardian please wake up, am sorry is my fault, is all my fault, na fita nikadai na barka tareda mutanen nan, Ya Muhsin dina!" yawani irin tashi yana jijjigashi amma ko gezau, fashewa yay dawani irin kuka yama kasa magana da kyar ya iya dago dakai ahankali hawayen dayake suna diga ajikin Ya Muhsin yaja bargon yarufe shi back yana tofamai addu'a kafin yawani irin juyowa cikin fushi yatako har zuwa gaban Abba dake kallonshi jiki asake yace "Alhaji Naseer Aluminum!" saida zuciyar Abba tawani irin girgiza sabida yanda dan cikin shi ya kira sunanshi kai tsaye haka, wani irin kuka kecin Ahmad da kyar cikin kuka ya iya yay magana. "karka, never in your life call me your son, kaiba mahaifina bane, I regret ranan danazo duniyan nan amatsayin danka, na tsanake na tsaneka sosai, I hate you, and kaje sai Allah yamana hisabi dakai kashemin dan uwana dakayi bazan taba yafema ba!" zaro ido Abba yayi yana kallonshi idanunshi sunyi jajir yarasa ta cewa, yajuya ya kalli Mum dake wani irin kuka kanta akasa yace "and you Mum, am so so disappointed in you, kome Mutumin nan zai miki saiki biye mai? I tried talking to you but kince namiki shiru nabarki kiyi magana and vent out your anger, that you are tired, so yanzu you've vented your anger kinyi son ranki danki kuma yarasu kun kasheshi da bakin cikin ku are you happy now? Are you happy Mum? Are you satisfy? Kozaki cigaba ne?" yay maganan yana kuka sosai, girgiza mai kai Mum tayi cikin kuka sosai kaman zata mutu, hannu Ahmad ya daga yana musu clapping yana hawaye yace "wow, wow, wow you guys deserve an award na kashe danku" yajuya dawani irin sauri cikin fushi yafita daga dakin dan zuwa clearing everything ya tafi da wanshi gida, da kyar cikin kuka Mum tadago kanta ta kalli Abba da shima ita yake kallo da idanunshi dasukayi kaman an jijjiga bera a buta tsabagen fitowa, atare sukai wurin gadon suka tsaya, cikin kuka sosai Mum ta kalli Abba tace "Alhaji danmu, Alhaji Muhsin, my son da gaske ya mutu Alhaji?" tai maganan kaman zararra tana janye blanket din daga fuskarshi tana wani irin kallon shi tana kuka, kallon Muhsin din Abba yayi gabaki daya kanshi ya kwance yakasa furta komi sai zaro ido dayake yi gabanshi na faduwa, bude kofan dakin akayi Ahmad da idanunshi sukai jajir ya shigo dawani abokinshi Bello dauke da makara dakuma babban tabarma, wani irin nishi Abba yafara yi yana kallon Ahmad din dako kallon inda Abban yake baiyiba suka ajiye komi akasa yazo ta gaban gadon shida abokinshi zasu dagashi da sauri Abba ya mika hannu zai dagashi Ahmad yamai wani irin kallon da idanunshi dasukai mugun jajir saida gaban Abba yafadi ahankali ya janye hanunshi ya maida kirji kaman mai shirin yin salla yana kallon Ahmad din, Ahmad da abokin nashi sukadau Ya Muhsin suka sakashi a tabarman suka sakashi a makara suka dauka suka fita daga dakin Mum nawani irin kuka tabisu da gudu Abba ma yabisu da sauri ko kallon su Ahmad baiyiba suka sakashi cikin motan ambulance din asibitin dasukai haya suka shiga kafin Mum dake kuka sosai da Abba su iso yawani irin rufe motan yacema direban su tafi suka fita daga asibitin, Mum ta tsugunna a wurin tana wani irin kuka kaman zata mutu bama tasan meke mata dadiba, Abba ya tsaya akanta yana kallonta ahankali yace "H...Ha..Hajara, tashi mutafi, kinji tashi muje" ahankali Mum tamike kaman tababba tace "a'a ina zani dakai wajen Muhsin zani shi kadai muka bari adaki" da sauri ta juya zata koma cikin hospital din Abba yarike hanunta da sauri yace "Hajara dubi, kalleni" cikin kuka sosai ta kalli Abba, Abba yace "Allah yafi nida ke son danmu, dama kuma shiya bamu shiko?" yatambayi Mum ahankali, da sauri ta girgiza mai kai hawaye na bulbulowa Abba yace "to Allah yama Muhsin rasuwa, addu'a zamumai ba kukaba kinji, yanzu zomu tafi gida naga banga motar ki a parking space ba, bakizo dashi bane" gyadamai kai Mum tayi tana wani irin kuka, juyawa yayi ahankali rike da hanunta ganin bata hayyacinta yay bakin gate da ita, yatare musu taxi suka shiga suka zauna yaciro wayarshi yafara kiraye kirayen abokan arziki da abokan business.
Chapter 55 · 0% Book details