← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 63

Sashe 11

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laptop din dake kan cinyarshi ne yazo zai fadi tsabagen yanda yake juyawa yana kallonta da sauri Abdallah ya mika hannu ya dauke laptop din daga kan cinyarshi yace "Ya Marwan" dan juyowa yayi ya kalleshi kafin yakara juyawa yana kallonta tana tsaye akan titi kana ganinta kasan abin hawa take jira, dan sanyi jikin Abdallah yayi, asanyaye yace "itace yesterday nurse from St. Edward?" ahankali ya juyo ya kalli Abdallah, shima Abdallah kallonshi yake ganin ko alamun zai bashi amsa baiyiba yasa yay dan murmushi yabude kofa ya fita daga motan, kalle kallen kasan wajen ya shiga yi kaman mai neman abu, hango wani kusa yayi akasan nan kusa da motarsu kadan hakan yasa yay wurin da sauri saida yafara daga kai ya kalli titin, ganin har lokacin tana nan kan titi bata sami abin hawaba yasa ya cire takalmin kafar shi ya tsugunna ya juyar da kusan yataka nail din tareda runtse ido dan zafi saida tadan bula kafan sanan yay maza ya janye kafar data fara jini, jini na bulbulowa, zama yay akasan wajen ya kwala ihu. "wayyo Allah nurse, nurse" daidai lokacin ta tare wani keke napep tana shirin shiga bama tajishi ba hankalin ta yay nisa gida tana tunanin hala Mum ta dawo yanzu, nuna mata bayanta mai napep din yayi yace "hajiya bake wancan dayaji ciwo ke kiraba?" ahankali ta juya dan ganin mai kiranta, hakan yasa Abdallah ya nunata da hannu kaman zaiyi kuka yace "nurse nataka wani abu, wayyo Allah am bleeding karna mutu, zoo ki dubani" gyara zama tai a keke napep din ta dauke kai saikuma ta sake kallonshi tace "this is a minor injury kacika raki, kaje kai alluran tetanus a any nearby pharmacy" ta kalli mai napep tace "muje malam" kaman zaiyi kuka ya rike kafan yana kallo yace "Nurse wlh karma kifara kisa nai bleeding to death, kinyi nightingale pladge fa zakuyi best dinku for patients, dan haka my life is in your hands now, kizo ko Allah ya kamaki" murmushi tayi daya kara mata kyau, oh yau Allah yahadata da namiji mai halin Ya Ahmad, dan bazan surutu bala'i, fitowa tayi daga keken tace "malam yi tafiyar ka karna batama lokaci" sanan tajuya, karasowa tayi ahankali inda yake tana kallon kafan nashi. Marwan da gabaki daya ya kafeta da ido any step datai taking har cikin kasakasan ranshi yakeji, namomin jikinshi nawani irin amsawa, blood stream dinshi nawani irin freezing. Tsayawa tai agaban shi tana kallon kafan, ahankali ta sauke jakan bayanta ta tsugunna batare data kalli fuskarshi ba, zage zip din jakar tayi ta fito da yar karaman first aid kit din dake ciki ta ijiye a gefe, handglove tazaro daga kwalinsu tasaka a hannu hakan yasa ya kwalalo ido yace "Nurse tiyata zakimin ne wai? kai!" wlh batasan lokacin data fara dariya ba, hannu tadaura akan fuskarta ta rufe tana dariya sosai dan maganan shi ya mugun bata dariya, ahankali Marwan yay wining down tinted glass din motar kasa kadan danya kalleta da kyau, yanda take dariyan da hannayenta data daura akan fuskarta yakara mata wani irin kyau, wani irin tafiyan butterfly yaji acikin cikinshi hakan yasa ya daura hannunshi akan cikin dayaji kaman ma yana murdawa yana kallonta still. Kasa daina kallonta Abdallah yayi yace "wai bazaki dena dariyan ba sai jinin jikina yakare, jibi yanda jini ke fita daga fine kafana fa" janye hanun tayi daga fuskarta ahankali batare data kalleshi ba ta bude kit din ta ciro spirit ta bude ta kwara mai akan ciwon dake jinin, dan kara yayi yace "auuch, me wanan kikasa min? Gaskiya u are a wicked nurse ba kya petting patient" murmushi tayi batare datace komiba tadau cotton wool tana sharewa tace "kaiko kacika raki, ga surutu kaman yayana Ya Ahmad, inyaji ciwo ko haka yake kaman kai" tai maganan daidai tagama cleaning ciwon tana kokarin cire handglove din hanunta sai kallonta yake, ahankali yace "and I know inda ace my sister na nan she would've been just like you" dago manyan idanunta tayi ta kallai daidai tagama cire handglove din, shima ita yake kallo, daukan kit dinta tayi ta maida cikin jakan tace "make sure kaje an maka tetanus injection, Allah sawake" daukan jakanta tayi ta goya zata juya wani irin sanyi ne ya shiga jikinta sosai hakan yasa ta tsaya chak tareda juyowa ta kalli motar su, da sauri Marwan yay wining glass din up tun kafin ta lura, atishawa tayi tai hamdala, mikewa Abdallah yayi yace "inane asibitin ku anan zanje nai alluran" batare data juyoba tace "St. Edward teaching hospital" tai gaba da sauri tai titi daidai lokacin wani keke napep ya tsaya ta tare ta shiga.

Kakkabe jikinshi yayi yay murmushi yabude kofan motar su ya shiga ya zauna ya rufo ya leko da kanshi ya kalli yayan nashi yana murmushi yace "how was my act?" ahankali yace "kana hauka ko, inba hakaba tayaya zaka taka nail comfortably, wats wrong with you Abdallah" murmushi yayi yana murza key motar yace "because you are in love" "what!" yafada angrily, tada motar yayi yace "Allah Ya Marwan, dudda baka fadamin abinda yafaru jiyaba tace a St. Edward take aiki which was inda mukaje jiya and naga yanda kake kallonta dat wat made me do abinda nayi sabida ka kalleta da kyau, finally kaga wata kanaso, finally you've seen someone, finally kai developing feelings ma someone, finally Ya Marwan zaiyi aure, finally Ya Marwan is in luv" tsaki yayi "something is really wrong with you Abdallah, kai! are you sick upstairs?" yay maganan kaman wani dan daba dinan, tsaki yasake yi ya dau MacBook dinshi yafara danne danne amma bama ya gane komi, sake dago kai yayi ya kalli Abdallah ta madubi yace "karka karamin irin maganan nan, i hate it! am not in luv, i just don't know what is wrong with me, i guess fushi nake kan rashin concluding aikin jiya" murmushi kawai Abdallah yayi yacigaba da tukin shi batare dayace komiba.

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

1⃣1⃣ - 1⃣2⃣

Shi kadai ya dinga jera uban tsaki yafi sau goma, gabaki daya fuskarta yake gani barinma lokacin data daura hannayen ta akan fuskarta tana dariya, tsaki yayi yamaida hankalinshi yacigaba da aikinshi da MacBook yana so ya natsu amma ina ya kasa a screen din MacBook dinma ganinta yayi tanamai murmushi hakan yasa yawani irin jan dogon tsaki yarufe system din da sauri yace "damn it!" sai uban huci yake kaman kumurci yana duddunkule hannu, murmushi Abdallah yayi yacigaba da tukinshi abinshi yace "ari".

Koda takai gida babu kowa duk sun tafi aiki Abba ma bayanan, mai aikinsu ce kawai agidan gaisheta tayi ta wuce daki tai wanka kaya ta chanzo har lokacin tana murmushin rakin Abdallah tafito tai kitchen tana taya yar aikin nasu aiki sukai hadadden girki ma Mum sukai arranging gidan aka share ko ina sai kamshi yake, tafito da kayan wankinta sukai backyard inda washing machine yake ya wanke su ya dauraye ta ciro ta shanya sanan ta dawo dakin lokacin an sakko daga masallacin juma'a hakan yasa tai dakinta taje tai salla, wayarta dake ringing yasa ta mike da sauri ta dauka agaban madubi, Mum data gani yasa tai wani irin tsalle ta zauna akan gado tadau wayar saikuma ta saki kuka tace "Mum tunda kika tafi baki nemeni ba kona kiraki baki dauka why Mum" dan dariya Mum tayi daga ta dayan bangaren tace "sorry my princess, busy nake sosai, meetings nakeyi wlh dawasu investors, apart from hakan ma inaso nasai share wani mutumi a burj al Arab amma sai yanga sukemin wai akwai wasu akasa, yanzu dai how are you? Abban ku told me what happen to you, sorry princess dina Allah ya kara tsaremin ke da protecting dinki kinji" gyadakai tai ahankali tace "Ameen Mum, karfe nawane zaku iso?" "ina princess?" "nan mana Mum, bayau zaki dawoba?" dan dariya Mum tayi tace "haba princess dina ke bakiso Mum dinki ta nemo kudin aurenkine? In aka tashi bikinki namiki biki, biki mai suna biki ba bikiki ba, biki da sai Nigeria da Abuja ta girgiza, kefa nake nemanma kudin nan uhm Apple of my eyes" make kafada tayi a shagwaban ce tace "Mumy ni wlh banaso, please just come back i want to hug you Mum, wlh kullum sainai mafarkin ki" takarashe maganan tana kuka, sosai zuciyar Mum ta karaya hakan yasa tace "kinga ko princess ayanzu haka danake miki magana i don't know yaushe zan dawo ma, cikin kaso goma a abubuwan danazo yi ko kashi uku ban kammalaba, but i promise you, i promise you princess, i will double my effort just for you kadai, dan kawai nagama da wuri nazo nima i miss my baby girl, my one and only baby girl, forget duk brothers dinki are kobo u are d only naira in my life, oya laugh inji" dariya tahau yi hawaye na fita, tana mugun son Mum dinta itace naira rayuwan mum, su Ya Muhsin da Ya Ahmad kobo ne su haha abinda ke kara sata jin dadi kenan, dariyan da Mum taji tanayi yasa ta sauke ajiyar zuciya hankalinta yadan kwanta sosai dan tunda Abba yay fushi yamata text din abinda yasameta dan bata kirasa back ba takasa samin natsuwa, ganin yanzu she's smiling yasa hankalinta ya kwanta sosai, ahankali tace "okay princess i will hang up now akwai inda zani i will try as much as possible nadinga kiranki kullum kinji, no matter how tight my schedules are, I love you" ahankali tace "I love you too Mum saikin dawo" "yauwa yar albarka bye" katse wayar Mum tayi hakan yasa tafada gado tana kukan bakin cikin bazata dawo yauba ahaka bacci yay awon gaba da ita sai wuraren biyar ma ta tashi da sauri ta fada bayi ta dauro alwala tazo tai sallan laa'sar sanaj ta fita ta debi fried rice kadan ta dawo palo rike da plate din ta zauna akan kujera tanaci tana kallon zee world.
Chapter 11 · 0% Book details