← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 63

Sashe 18

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaro hannayenshi yayi daga aljihu, ahankali ya cirota daga jikinshi ya tallabo fuskarta da duka hannayen shi ya dago kanta yana kallon fuskarta, wani irin kuka take mai tana sauke ajiyan zuciya tana kallonshi kaman irin jariri yaga maman shi data fita anguwa tabarshi dinan, yanda take kukan yasa ahankali ya janye hannu daya daga habarta yakai kan fuskarta yana share hawayen dake zubomata yana kallon fuskarta murya chan kasa yadan lumshe ido yace "shiiiiii why are you crying like this, jibi yanda eyes dinki ya kumbura and you are running temperature bakida lafiya ne?" bude idon yayi dasukai kaman namai jin bacci ya zubasu akan ta, ahankali yace "Menstrual cramp kesaki kukan nan?" hanunta takai ta daura akan nashi dake kan habarta ta kankame gamgam tana wani irin kukan tana girgiza mai kai, hakan yasa yace "to menene? Why are you crying like this what happen wats d matter?"
"zazzabi take tun cikin dare Son, shine fa taketa uban kukan nan" da sauri ta maida kanta kan kirjin Ya Muhsin ta kankameshi sosai tareda runtse ido tana saukar da wasu irin ijiyan zuciya heart dinta nawani irin racing, juyawa Ya Muhsin yayi tana makale dashi ya kalli Abba dake tsaye jikin kofa dan baimaji shigowan shiba, yana tsaye dauke da takeaway a hanunshi da ledan magani yadanyi zuru zuru yana sanye da fararen shadda riga jumper da wando, inba kaga su Muhsin ba bazaka zaci ya kwan biyu a duniya ba dan yanada jiki mai kyau baida kiba sosai haka, ahankali yadan tureta daga jikinshi yaja hanunta ya zaunar da ita a bakin gadon sanan yay inda Abba yake tsaye ya karbi take away dana magungunan yace "good morning Abba, dana shigo babu kowa afalo saisa nayo nan" murmushi Abba yamai yanadan satan kallon Nadeera da kanta ke kasa tana inda Ya Muhsin ya ijiye ta abakin gado tana share wasu sababbin hawayen, Abba yace "how was d conference, i was saying zan kiraka fa but princess dukta dameni da kuka na manta, Ya conference din son hope everything went well" murmushi yayi yana juyawa yace "Alhamdulillah Abbana, anyi angama saikuma na next year" jawo stool din gaban mirror yayi ya zauna agabanta yana bude take away chips ne da soyayyen egg hakan yasa ya mikamata, ahankali ta karba tana kallonshi, dan kallonta yay shima sai ya tashi daga kan stool din yace "lemme bring spoon for you" yay hanyar kofa, Abba yace "oh kaga fa namanta da spoon din a dining dukta rudani wlh" murmushi yayi yabude kofa yafita, hakan yasa Abba yayo ciki da sauri azabure ta mike hartana neman zubar da abincin da sauri ya tare takeaway yamata wani irin mugun kallo, yakamo hanunta yace "remember what i told you, saina kusa yankaki inkika fada" ya watsa mata wasu irin harara da sauri yajuya yakoma wurin kofan jin ana shirin shigowa, bude kofan Muhsin yayi rike da fork da bottle water mara sanyi yakaraso ciki yana kallon yanda take kuka ta rufe fuskarta da filo, yace "wai kukan bai isaba mtsww" yaja tsaki, zama yayi gefen ta akan gadon ya ijiye bottle water da da fork din agefe ya dagota da kyar ta taso, takeaway yasamata aakan cinya yanadan hararanta yace "stop this kukan, eat idan jikin bai saukoba i will take you to the clinic, eat kafin nabata miki rai" ahankali ta deba tafara ci tana sauke ajiyan zuciya hakan yasa ya dago kai ya kalli Abba da shima kallonta yake, cikin kunan rai yace "Abba wai yaushe Mum zata dawo, kullum nakirata tana meeting saidai tamin text haba mana dis girl is sick bazata dawoba, kullum ita kadai agida mu muna zuwa aiki, Abba please kace tadawo and gaskiya is high time tadena wanan tafiye tafiyen Abba" girgiza kai kawai Abba yayi yana cije baki yace "namata magana tadawo taki wai saita gama abinda ya kaita, na zuba mata ido tai duk yanda taga dama, zaki girbi abinda ta chuka, am coming" da sauri yabude kofar dakin yafita jin zuciyar shi na zafi dan Mum ce tasa ya aikata abinda ya aikata jiya wanan wace irin kaddara ce, dakinshi ya shiga ko kadan baida sukuni koya rufe ido tunani soft hand din Nadeera yake a jikinshi, tunanin soft lips dinta yake dakuma how warm her soft hand is akan abunshi fiye dana uwarta ma, da sauri yay bayi jin sha'awar takara tasomai kaman zaiyi kuka ya shiga shower ya sakinma kanshi ruwa yana wani irin sauke ajiyan zuciya yana "wayyo Allah, wayyo Allah" da kyar yasamu abun ya lafamai yafito ya shirya ya kwanta akan doguwar kujera yana addu'a Allah sa ta rufa mai asiri, karta fadi komi bayason .

Ko kadan abincin baya mata taste hakan yasa da kyar tai kaman spoon uku ta ture zata ijiye yadan juyo ya kalleta yace "kin koshi" gyadamai kai tayi asanyaye hakan yasa ya bude magungunan ya ballo yanda aka rubuta ya mika mata da ruwan goran daya bude mata karba tayi tasaka abaki tasha ta hadiye ya karbi ruwan daga hanunta yana kallon yanda ajiyan zuciya kawai take saukewa idanunta sun kumbura sosai, ajiye ruwan yayi a gefe batare daya kalletaba yace "kiyi bacci lemme go and shower" rikemai hannu tayi arude ta kankameshi ta sakinmai wani kukan, juyo dakai yayi ya kalleta kura mata idanu yayi yanda take kukan ba kakkautawa, ahankali yace "Nadeera" dago rinannun idanunta tayi ta kalleshi, murya chan kasa yace "menene wat exactly ke miki ciwo?" wani irin kuka tafashe dashi tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka, bubbuga bayanta yay ahankali yace "shiiii is okay, stop crying, Mum zata dawo very soon okayy" kara kankameshi tayi tana sauke ajiyan zuciya tana lumlumshe ido, konan da chan bataso yaje dan gani take yana fita Abba zai shigo, ahaka baccin da batayi jiyaba yay gaba da ita, jin yanda take fitar da numfashi hakan yadan janye jikinshi daga nata ya kalli fuskarta ganin tai bacci yasa ya kwantar da ita ahankali sai a lokacin ya lura da yanda gefen fuskarta yay ja sosai alamun mari, kafe wurin yay da kallo yana mamakin wanda ya mareta haka, saikuma yay tunanin maybe shegen kukan datake yasa ko Ahmad ko Abba waninsu ya mareta, inhar Ahmad ya mareta haka wlh saiya sani bari yadawo.

Ahankali yay yunkurin tashi yaji tarike mai riga gam hakan yasa ya kalleta ganin har lokacin baccin take yasa ahankali yacire hanunta ya ijiye gefen ta yatashi yaja bargon gadon ya lullubeta da kyau kafin ya tattare su takeaway yay hanyar fita daga dakin ya kashe mata wuta yafita ya rufo kofa, da Abba yaci karo a corridor
ya tsaya abakin kofan shi yay shiru yay nisa a tunanin karasawa wajen yayi yace "Abba" dago kai yayi ya kalli Muhsin yay murmushi yace "son ya take yanzu?" "she's fine tamayi bacci, bari naje nai wanka Abba" "alright son" juyawa yayi yafice yawuce dining ajiye abubuwan yayi akan dining yafita yay shashin su.

Da sauri Abba yay dakin yabude dakin ya shiga ganin tana baccin yasa yakara sauke tagwayen ajiyan zuciya, ahankali ya tsugunna yana kallonta, kafin ahankali yadan zame bargon kasa kadan yana bin wuyanta da kallo, hanunta ya kamo ahankali ta yanda bazata tashiba yana shafawa ahankali ya lumshe ido sabida yanda hanun keda taushi sama dana mamanta, kasa daurewa yayi ya saki hanunta ya mike tsaye ya zagaya ta bayan gadon yahau ya kwanta abayanta ahankali ya rungumota ta baya ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai kara yace "yauwa my princess sleep with Abban ki" lumshe ido yayi shima wani irin baccin na fizganshi, bude kofan dakin akayi hakan yasa ya dago kai afirgice dan shaf ya manta bai kullo kofan ba.

*another post later*

_Please please wlh yafaru da gaske uba dai dakuka sani dake neman yarshi, sonta yake bilhakki fa, akwai wanda har ciki yama yar tashi. Akwai kuma wani dake cewa shifa bazaima wani kato kewon yaranshi ba batare dayasha romo ba. Duniyar yau bata jiya bane damuka sani ba, mata mutashi daga bacci mu kula da yaranmu mata kawai._

🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

AD

Ya Ahmad ne ya shigo dakin da saurin shi sabida Ya Muhsin tun dazu yamai magana ta watsapp Nadeera bata da lpy sosai, ido da ido sukai da Abba hakan yasa Abba ya mugun rude amma saiya daure ya maze ya shiga tofa mata addu'a yana rike da ita yace "Princess Abba is here Mum dinki zata dawo" dago kai Abba yayi yasake kallon Ahmad yace "Son rawan sanyi take sosai sai kiran mamanta take, saisama na lullubeta da bargo ganin tana sumbatu yasa nahau gadon na rike" yay maganan yana tashi daga kan gadon, ahankali Ahmad ke binta da kallo tun daga sama har kasa ganin yes ga bargo nan a jikinta fuskarnan nata yay fayau yasa yay maza ya kawad da bad tunanin da shaidan ya jefomai arai ya kalli Abban kaman zaiyi kuka yace "kodai mukaita asibiti ne Abba? Wlh Mum bata kautawa kewanta zai illata yarinya" tabe baki Abba yayi yace "i know what to do son muje tasamu tai bacci tunda takoma, fita sukayi daga dakin suka rufo mata kofa. Sosai baccin ya shigeta dan bata samu najiya ba, sai sharan baccinta take.
Chapter 18 · 0% Book details