← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 63

Sashe 39

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***
Kuka tayi bana wasaba yau ko kadan bata sashi a idoba, rabonta dashi tun jiya bayan sun dawo daga side din Abba, tun safe saidai ayi knocking wani kuku da farin uniform ya shigo ya ijiye mata abinci batare daya kalletaba ya fice haka har dare, bayan magrib ma kuka taci tai baccinta akan dadduma sai wuraren karfe daya na dare ta farka cikin bacci da sauri ta tashi tsaye tana sanye cikin wani pink plain t-shirt na mata daya dan kamata sai wani dogon black straight skirt, juyawa tayi tana sosa ido ta shiga bayi ta dauro alwala tafito tana goge hawaye tahau kan dadduma tasaka hijabi tai salla takafe kofar da kallo zuciyar ta na raya mata ta gudu, ahankali ta mike tsaye silifas ta zira tazo wajen kofan jikinta na rawa ahankali ta bude kofan ta leka babu kowa a wurin sai hasken wuta koina yay shiru fes fes karasa bude kofan tayi ta fito tana kallon ko ina kafin tasa kafa tafito cikin sanda tai wajen stairs tana sauka da gudu tana waigen bayanta cikin tsoro fadawa tayi jikin mutum atsorace ta dago kai ta kalleshi yana sanye da bakaken kaya da bakin mask yasaka hulan hoodie akanshi ya goya wani bakin jaka abayan shi kaman mai shirin fita, da sauri ta juya jikinta na rawa zata gudu fizgo hijab dinta yayi ta dawo da baya ta fada jikinshi wani irin atishawa tayi ahankali ya kulla hanunshi acikinta shima yay atishawa yana kara kankameta bakaramin kewanta yayiba, sosai yadinga fada dakanshi tsawon jiya zuwa yau yanaso yanuna ma kanshi ba sonta yakeba saisa yahana kanshi ganinta amma kasa tabuka komi yayi, hanunta tadaura adan tsorace kan hanunshi kaman zatai kuka tana kokarin kwancewa ta cirw daga cikinta, murya chan kasa yace "where are you going" girgiza mai kai tayi tana shirin yin kuka tana kokarin kwance hanunshi daga cikinta takasa, wani irin juyo da ita yayi da karfi ya kulle hanunshi ta bayanta, atare dukansu sukai atishawa kowanen au najin wani irin sanyi matseta yayi da hannu daya yasa dayan hannun ya dago habarta, kallonshi tayi saikuma ta kawad takai ta kalli falon bindigogi tagani da sunkai kusan takwas manya dogaye ga bullet zube akan kujeran da wayanda ke cikin kwali dake bude da wayanda kw ajiye akan kujeran juyo da fuskarta yayi hakan yasa ta kalleshi a tsorace saikuma ta sake janye idanunta tana kallon bindigogin juyo da kanta yayi yana kara matseta, ahankali adan tsorace tace "me kake yi da alot of guns?" shiru yayi yana kallonta ta cikin mask yana kallon yanda small pink lips dinta ke wani irin shining dake fizgarshi, dan ajiyan zuciya ya fuzar jikinshi namai wani iri kafin chan kasa ahankali yace "operation zani" yay maganan yana sata jikinshi gabaki daya kaman zai rungumeta, kokarin janye kanta takeyi daga jikinshi amma yaki bata daman hakan adan rude tace "wani irin operation kai Doctor ne?" girgiza mata kai yayi batare dayay magana ba sai chan murya chan kasa yace "ina zaki?" raurau tai da ido tace "water zan sha" daukanta kawai yayi unexpectedly ta ware baki zatai ihu, lips dinta ya kama da yatsunshi ya rike yace "don't scream" gyadamai kai tayi adan tsorace tana wani irin kallonshi cikeda tsoro, ahankali ya juya da ita batare daya dena kallonta ba ya fara sauka yay daga stair case din da sauri ta kankame riganshi jikinta na rawa, sauka yayi daga stairs din yay hanyar babban kitchen dinsu da ita zaunar da ita yayi akan wani dogon kujera dake kitchen din ya juya yay wajen fridge binshi take da kallo kirjinta na bugawa sosai, dauko cold Eva water yayi ya rufe fridge din ya juyo yadawo inda take ya tsaya a gabanta, bude ruwan yayi ya mika mata batare da yay magana ba hanunta har rawa yake takai zata karba ahankali ta daura hanun kan goran hakan yasa ya sakan mata ta karba tana kallon fuskarshi wondering wai waye wanan boyayyen mutun din, wani irin atishawa tayi dayasata sakin goran ruwan daga hanunta ya zube akan hijabinta dan ihun sanyi tayi da sauri ya dauke goran ya ijiye agefe hannunshi ya daura kan hijabin yacire mata hijabin kai tsaye ya ijiye kan table da sauri ta dukar dakai tana wasa da yatsun ta dan jitake kaman zata saki fitsari sabida tsoro ahankali yadau ragowan ruwan ya bata karba tayi takai bakinta kadan tasha tacire daga bakinta dan dama ba kishi takeji ba, karba yayi ya ijiye agefe sanan ya dago kai ya kalleta, ahankali yatako yazo gabanta sosai wani irin nishi tafara dan sosai ya cika mata ido, cikin wani irin murya yace "karki kara yunkurin guduwa is not worth trying, u cannot escape okay" gyadamai kai tayi da sauri hawaye na taruwa a idanunta lips dinta ya shafa yace "Hey! Don't cry" sake gyadamai kai tayi hawayen na shirin gangarowa da sauri ta share, bakinta na rawa sosai tace "p..please ka kaini gidanmu wurin Mum, i..i..wan.." saita kasa karashe maganan tafashe da kuka mara kara sosai sabida tsoro, ahankali ya sakala hanunshi ta waist dinta ya dauresu abayanta adan firgice cikin kuka ta kalleshi, girgiza mata kai yayi murya chan kasa yace "stop crying" gyadamai kai tayi tasa bayan hannu ta goge hawayen dasukaki dena zuba sai gogesu take da bayan hannu, janye dayan hanunshi yayi daga bayanta ya kai kan fuskarta ya saukar da hanun kasa batare daya sakiba ya rike gam yace "you want wat?" bakinta na rawa tace "i...w..ant to go back to school, nacigaba da practical dina, i want to go and stay with my Mum" shiru yayi yana kallonta saikuma ya girgiza kai ahankali yace "u are my wife i can't release you again, bazaki kara komawa dat house ba da mijinki zaki zauna" shi kanshi baisan yay maganan ba hakan yasa yay shiru yana kallonta yanda take goge kwalla dago kai tayi ta kalleshi tace "da gaske ne dama Abba yamana aure, ni matar aure ce?" gyada mata kai yayi yay shiru yana kallon fuskarta saikuma chan yace "ke matata ce" share wasu sababbin hawayen tayi cikin kuka datake so ta danne tace "how? Tayaya zan auri wanda bansan shiba, maisa Abbana ya auramin kai? I don't know you, bansan kaba fa, kai Boyayyen Mutun ne, bansan kaba" hanunshi ya daura akan fuskarta ya share hawayen datakeyi kafin ahankali ya duko da kanshi yahada goshin shi da nata murya chan chan kasa kaman mai whispering yace "kina so kiga fuskan mijinki?" sosai kirjinta kewani irin bugawa jin kanshi hade da nata kamshin dayake yana wani irin shiga hancinta hakan yasa tawani irin ja numfashi kafin ta saki da karfi adan tsorace tace "e..eh" ahankali ya janye kanshi daga nata ya mike tsaye agabanta yadan tattare hanun hoodie dinshi sama ya daura hannunshi daya akan safan hanunshi na dama ya dago kai ya kalleta yace "are you ready?" wani irin bugawa kirjinta yafara tana kallonshi kaman taga tv ta gyadamai kai tace "y..yes".
[9/14, 7:07 AM] Lady: *Maman Abd Shakur*

Sosai take gudu akan keken, kutsawa cikin dajin kawai takeyi batare datasan inda ta dosaba, tai tafiya kusan na minti goma taji kafafunta sun sage da tukin keken hakan yasa ta rage gudu tana goge zufan goshinta wani dandamali keken yaci karo dashi hakan yasa da ita da keken suka wani irin juyi tadinga tumble tumble tana gangarawa dan slope din har takai wani bishiya ta wani irin buge da bishiyan ta sume awajen jini nabin kafafunta da gefen goshinta.

Yakai kusan 15min abayi sanan yafito, shirya wa yayi a closet tsaf wani black hoodie da dogon wando yasaka da talkami yasa face mask dinshi dana hannu dan akwai inda zashi, feshe kanshi yayi da turare sanan yakoma gaban bayi yadau wet dogon riganta dake kasa ya bude bayin yasa a washing machine sanan yafito ya bude kofa yafito dakin, sosai gabanshi ya fadi ganin gadon empty babu kowa akai, ahankali ya juya yabi ko ina na dakin da kallo ganin wayam babu ita yasa da sauri yay wurin kofa ya bude yafita yana waigen waige yana kwala a kaninshi kira. "Abdallah, Omari, Omari!" sauka kasa yayi da gudunshi yana kallon ko ina, yay kitchen da sauri, babu kowa a wajen yafito yana wani irin kwalama kanin nashi kira "Abdallah, Abdallah Omari!" yawani irin daka ihu azafafe "Abdallah!" da gudu Abdallah dake daure da towel yafito daga sama yace "Ya Marwan menene kasa naji tsoro wanka nake saisa ban amsaba yanzunan nadawo daga sport ya Omari tun dazu yafice" yay maganan yana saukowa daga benen, muryan shi har rawa yake yace "w..where..have you seen my wife?" girgiza mai kai yayi yace "yanzun nan nadawo wah happen?" hanyar waje yayi da sauri yace "I can't find her go and get dress" da sauri Abdallah yace "wat?" amma harya fita sama yakoma da sauri ya sako riga da wando yafito shima saida ya zagaye gidan sanan yabiyoshi waje amma harya hau kan bike dinshi yay gaba azuciye.
Chapter 39 · 0% Book details