← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 63

Sashe 40

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Lashe mata kafa dataji anayi yasa ta farka a firgice, raguna tagani kusan guda hudu da yaransu sun zagaye ta suna lashe inda ke jini a kafarta kaman tadawo abinci, wani irin ihu tayi ta ja kafar nata a tsorace tana komawa baya tana kallon su yanda suke mata "emeeee" aka, mikewa tsaye tayi da kyar tana dafa bishiyar ta arce da gudu tana kallon raguna data firgita su suma sun kwasa da gudu tasake fasa ihu, sosai take gudu da duka karfinta tana juyawa tana kara kallon saman dajin gabaki daya batasan inda zataba, karan motoci dataji yasa tawani irin kara karfin gudunta tana numfashi, bigewa tayi da bishiya taji kanta na juyawa da kyar ta koma baya sanan ta cigaba da gudu kaman tababba, yanka dajin kawai take jin karan motoci yasa tawani irin fashe da kuka takara karfin gudunta tai hanyar da kyar ta iya fita taganta akan titi mai kyau davatasan kona ina bane, fashewa tasakeyi da kuka sosai titin ma daidai motoci ke wucewa da gudun gaske, gudu tacigaba dayi duk motan dayazo tana kokarin tsayar dashi amma basa tsayawa, sosai tai gudu na kusan minti shida, hango wani Fulani man mai kiwo tayi yana kada shanun shi da raguna hakan yasa tai wajen da gudu ta ta tsaya kusa dashi cikin kuka tace "malam dan Allah ka aramin wayanka nakira mamana wani zai saceni ne" yanda take kuka yasa yace "assha yarinya garin yaya? Aiko saidai kiyi fulashin wayanta a kwadala tai aggareta" gyadamai kai tayi tana share hawayen ta da bayan hijabin ta, ya ciro wayarshi rakani toilet daga aljihu ya mika mata yana gyara rokon sandar kada shanun hanunshi, tsugunnawa tayi a gefenshi har lokacin jikinta baibar rawa ba tasaka number Mum tai dailing akashe, fashewa da kuka tayi tasaka na Ya Muhsin shima akashe sosai tafashe da kuka har dan Fulani na tambaya lafiya ta girgixa mai kai, number Ya Ahmad ta saka saida yakusa katsewa sanan aka dauka kafin ma yay magana tafashe da kuka tace "Ya Ahmad come and pick me kafin ya kamani am scared" daga tachan bangaren ya Ahmad dake tiki zaije siyo wani allura awani babban pharmacy daza ama ya Muhsin ya kalli wayar sanan ya maida a kunenshi, kukan ta dayaji yasa yace "Princess, Nadeera kece" gyadamai kai tayi bakinta narawa tace "kazo ka daukeni Ya Ahmad nine, zai kamani nagudo ne ina bakin hanya wani Fulani na ari wayanshi nakiraki Ya Ahmad kazo please baida kati call me" katse kiran yayi yakirata da sauri ta amsa yace "calm down princess yimin magana anatse, yanzu kikace kina ina kinsan wani bakin titi kike? Inane wurin?" girgiza mai kai tayi ahankali tace "I don't know" da sauri yace "bame wayan to" mikama dan filon tayi tace "gashi yayana" karba yayi tana share hawaye tana Kalle Kallen titin daga tsugunnon miko mata wayan dan filon yayi yace "gashi zai miki magana" karba tayi takara a kunne Ya Ahmad yace "kina jina princess zaisaki a mota dazai taho dake cikin Abuja zan jiraki a zuba" gyadamai kai tayi daidai nan dan filon harya tare mata mota ya kalleta yace "zokije Allah tsare gaba, sai akula akuma kiyaye" tashi tayi arude tana kallon hanya kafin taje ta shiga motar bama tamai godiya ba tsabagen rufewa, dama mutum daya ya rage a motan yacika direba yarufe motan yakoma gaba yatada yaja, sosai take kuka tajuya tana kallon baya daidai lokacin taga boyayyen mutum sanye da hoddie dinshi da face mask akan machine ya tsaya daidai bakin hanya yana waige waige, da gudu ta juyar dakai ta dukar dakai kasa tana kuka ahankali, kafe motan yayi da ido saikace yasan tana ciki yabi motan da kallo harta bacemai jikinshi na fadamai tanaciki.

Daidai lokacin Abdallah ya iso akan bike dinshi yace "kaganta kodai mukoma cikin dajin ne Ya Marwan muduba da kyau?" girgiza mai kai kawai yayi batare dayay magana ba tsabagen yanda zuciyarshi ke tafarfasa, wani irin tada machine din yayi a zuciye yadau hamlet ya kafa yajuya yakoma cikin dajin shima Abdallah yabi bayanshi.

Saida suka kai zuba aka sauketa driver yace " kawo kudinki" waige waige tafara ko zataga Ya Ahmad daidai lokacin ya sauko daga motar shi idanunshi boye cikin bakin glass yazo wajen wani irin fashewa tai da kuka tace "ya Ahmaddd" kafin tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka, wani irin murmushi yayi mai ciwo ya ciro kudi da baima san yawan su ba ya mikama direban daya tsaya yana kallon su, karba yayi yay godiya yakoma cikin mota yatada yabar wajen ahankali Ya Ahmad ya dago fuskarta yana wani irin kallonta kafin yasa hannu ya share mata hawayen yace "stop crying" gyadamai kai tayi ya rike hanunta sukai inda yay parking, agaba ya sata yarufe kofan sanan yakoma ta mazaunin direba ya zauna yatada motar tana kallon titi dukansu sunyi shiru yana tafiya, ahankali tace "am hungry Ya Ahmad" gyadamai mata kai yayi yay parking agaban wani eatry nakan hanya ya kalleta yace "am coming" fita yayi ya shiga eatry bai wani jimaba yadawo dauke da abinci a ledan earty da drink da ruwa side dinta yabude yabata sanan ya rufe yakoma ta dayan side dinshi ya zauna ya kunna motar yana kallon yanda takecin abincin, sosai taci takoshi sanan ta rufe abincin ta ijiye akasa tasha ruwa ta ijiye kafin ta kalleshi ahankali tace "Ya Ahmad ina Mum take" batare daya kalletaba yace "hospital" da sauri tace "menene batada lpy ne?" girgiza mata kai yayi batare daya bata amsaba kaman zatai kuka tace "Ya Ahmad please wurin Mummy zaka kaini kaji" gyada mata kai yayi yanajin wani irin tausayin ta, thank God ma Abba yafita daga asibitin yana kaita wurin Mum zasusan yanda za'ayi.

Tafiyan kusan 20min sukayi sabida holdup sanan suka kai hospital din, a parking space din asibitin sukai parking ya kashe motan yafito yana kallon wurin kafin ya zagayo yabude side dinta yana kallonta, ahankali tafito tana kallon ko ina, hanunta yarike yace "muje" binshi tayi tana kallon ko ina tace "Mum batada lpy ne Ya Ahmad?" girgiza mata kai yayi yace "no ba ita bane" da sauri kaman zatai kuka tace "to waye baida lpy" ahankali yace "Ya Muhsin" tsayawa tayi chak ta kalleshi bakinta na rawa sosai tace "Ya Muhsin?" gyada mata kai yayi ahankali, fashewa tai da kuka suna tafiya tana share ido har suka kai gaban dakin, ahankali Ahmad yatura kofan dakin ido da ido tayi da Mummy ta dake zaune kan kujera tai tagumi tana facing Ya Muhsin dahar yanzu baisake farfado wa ba anamai karin ruwa, wani irin kallo Mum ke mata mata kasa magana tsabagen mamaki, wani irin rushewa tayi da kuka ta shiga dakin da gudu tafada jikin Mum tana kuka sosai tace "Mum, Mummy na I really miss you Mummy, Mummy karki kara barina ni kadai kinji" ahankali Mum dataji kuka na zuwan mata ta dage ta danne ta dagota tana kallon fuskarta yanda taga ta rame mata idanunta sunyi zuru zuru sun fada ciki, yauce rana ta farko dataji ta tsani rayuwanta, ta tsani sana'a da business datasa agaba, tafifita su sama da komi na rayuwanta amatsayin ta na matan aure, jibi matsalan data jawoma kanta yanzu, matsalan da bamata da basirar magance wanan matsalan, batada tunani da dabaran magance ta.
Chapter 40 · 0% Book details