← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 63

Sashe 56

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***
Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan matsa gefe sabida yanda suke kusa kusa da Marwan daketa daddanna system abinshi kamshin shi na fizganta, dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Abdallah daketa kallonta hoping zatace wani abu again, dan hararan shi tayi tana wasa da yatsun ta tana turo baki tana kukkuni kasa kasa tace "ni banason ana kallona fa" "lalalala" Abdallah yafada yana saukar da kafanshi kasa, da sauri ta kallai murmushi yay escaping bakinta, ta wutsiyar ido Marwan keta kallonta, Abdallah ya kalli Ya
Marwan yace "Ya Marwan wlh kama amaryan ka magana ba kaga tanamin kukkuni ba" murmushi sosai tayi, hakanan batasan mesa she always find the guy funny ba, kamanYa Ahmad haka yake mata, ahankali Marwan ya janye system din yana wani irin kallon ta kaman yahadiyeta yakasa magana, turo baki Abdallah yayi kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan bakace komiba kagama dariya takemini" murmushi tayi sosai harda daura hanunta akan fuskarta, daidai lokacin aka bude kofa Omari ya shigo dakin dauke da sallama shima idanunshi akan kanwar tasu da sauri Abdallah ya kalleshi kaman zaiyi kuka yace "Ya Omari kaga amaryan Ya Marwan na tsokanana ko, wlh this nurse ko she's so tsokanacious" fashewa tai da dariya hartana bige kafan ya Marwan, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta barin ma Ya Marwan dake gefenta dayakeji kaman ya tsaga jinin shi ya sata ciki, Ahankali Omari daya kasa dena kallonta ya shigo dakin ya zauna gefen Abdallah gani yayi dariyanta kaman na Momma su, da kyar tai shiru tana murmushin data dade batai irinshi ba dimples dinta nawani irin lotsawa, dukan cinyan Omari Abdallah yayi yace "ehen nurse zokiga Ya Omari yaji ciwo a hannu dama dazu yabige da table ko Ya Omari?" kallon Abdallah Omari yayi, Abdallah ya kannemai ido hakan yasa Omari ya kalleta suka hada ido yace "y..y..uhm" da sauri Abdallah ya fizge hanunshi yaja hanun riganshi sama yace "zoki gani nurse" make kafada tayi ahankali tana leken hanun nashi daga inda take zaune tace "aini banga ciwo a hanunba, in bigewa ne jamai kawai za'ayi zai dena zafi, kajamai" da sauri Abdallah ya kwalalo ido yace "ni? Wai bakiga katon hanun Ya Omari bane kaman na Ya Marwan" murmushi yayi ya kalli hanun ya Marwan din dayay kaman baya jinsu nanko kunenshi nakan duk abinda suke cewa, juyowa yayi ya kalli Nadeera itama shitake kallo ya nuna mata hanun Ya Marwan yana cemata look yana nuna mata manyan muscles dinshi Yana nuna mata ta kalla, makemai kafada tayi taki kallo, turo mata baki Abdallah yayi hakan yasa kaman daga sama tace "wlh kacika shagwaba" hararanta yayi shima harsaida tai murmushi yace "nakai ki?" da sauri tace "ni? Ni ai banda shagwaba" tabe baki yayi yace "wai talle kema audi gori" kama baki tayi tace "wai a ina kaji hausa? You don't look like a hausa man" murmushi yayi yace "kema u don't look like a hausa girl shagwababbiya kawai" makemai kafada tayi ta kalli Omari daketa kallon su kaman yasami film yanajin son kanin nashi aranshi tace "dan Allah waini shagwababbiya ce?" girgiza mata kai yayi ya tallabe keyan Abdallah yace "don't mind him lil sis keba shagwababbiya bace" dan murmushi tayi tana komawa jikin kujera dudda she found yanda yakirata da lil sis a little bit weird amma saita basar tajingina da kujeran tareda lumshe ido kaman mai shirin yin bacci, wani irin faduwa gabanta yayi harsaida taidan ihu tareda bude ido a firgice tana numfashi da sauri da sauri, kallo dukansu suka bita dashi, ahankali Marwan dake gefenta yataso ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "menene?" baki ta tabe tana wani irin nishi tana kallonshi tana shirin yimai kuka, girgiza mata kai yayi tareda daura yatsan shi akan lips dinta yana wani irin kallon ta murya chan kasa danko su Abdallah bazasu iyajin abinda yace ba yace "don't cry for me, menene?" yay maganan yana janye yatsan daga kan lips dinta yamata wani irin kallon ban amsa, ahankali hawaye nacika idanunta ta dafa zuciyarta tace "My heart" ahankali ya kalli kirjin nata kaman mai nazarin abu kafin ya mika hanunshi ya janye nata ya daura nashi akai koshi yaji yanda yake bugu fast fast, fashemai tayi da kuka sosai tace "please kiramin Mum, zanyi magana da ita something is wrong" tafara wani irin nishi bakinta ya bushe sosai, dan juyo da kai yayi ya kalli Abdallah dake kallonsu yace "get me water Abdallah" dasauri Abdallah yatashi yana waigenta yaje kitchen ya dauko bottle water yadawo ya mikamai, budewa yayi ya kai bakinta da kyar ta sha tana fashemai da kuka tace "dan Allah Mummy na" yanda take kukan tana wani irin nishi yasa yajata jikinshi ya rungumeta yana buga bayanta hanunshi daya kuma yana kokarin ciro wayarshi dake bayan wando ya ciro yadawo dashi ta gaba ya bude wayan yay dailing number Mum.

Mum dake zaune cukin mota kuka take sosai ko mutum daya takasa kira saima kallon wayar nata da Abba yaciro daga purse dinta yasamata a hannu take, shidai Abba sai kiran mutane yake da limamai, ringing wayan Mum din tayi tabi wayar da kallo dudda tagane number Marwan ne amma takasa picking, sai uban kuka take akaro na uku sanan Abba yace "amsa mana Hajara hakuri zakiyi kinji" da kyar ta iya tai picking call din ta kara akunenta tana kuka sosai takasa magana, daga tachan bangaren saida gaban Marwan yafadi a yanda yaji Mum na kuka da sauri Nadeera dake jikinshi ta dago kai tafashe dawani kukan tana kallonshi, cikin kuka tace "Mummy na ta dauka?" jin maganan Nadeera yasa Mum ta katse wayar da sauri tarushe da kuka sosai, sakinta yay ahankali ya mike tsaye dan jikinshi yabashi wani abu matsawa yayi chan bangaren dining ya tsaya yay dailing number da kyar Mum ta iya picking call din ahankali Marwan yace "why are you crying Mum? Did dat man hurt you?" cikin wani irin murya raunanniya Mum tace "d'ana Muhsin dake kwance a asibiti ya rasu yanzun nan" sosai maganan ta dakai harsaida kirjinshi ya buga yadago kai ya kalli Nadeera dake zaune akan kujeran daya barta tana goge kwalla tana kallonshi jira kawai take taji mezaice, dan murmushi yamata danya kwabtar mata da hankali, kafin ya kalli wayar ahankali yace "may his soul rest in peace, and may Allah forgive his short comings" ahankali cikin kuka Mum tace "Ameen" tareda katse wayan, ahankali ya shigo falon yana kallon su Abdallah da sun riga sun karanci something is wrong daga fuskan shi, kafin ma yakaraso cikin dakin ta tashi da sauri ta karaso tana numfashi sama sama ta rike mai hannu tace "uhmm meya sami Mummy na? Metace? Wlh inaji ajikina something is wrong, please kafadamin gaskiya kaji please" ta karashe maganan tana fashemai da kuka, hanunta ya rike ahankali ya kakalo murmushi yace "come" stairs yay da ita tana kuka sosai ya shiga dakinsu da ita, fashewa tai da kuka sosai tana sake kallon fuskanshi tace "kafadamin dan Allah meya sami Mummy na" rungumeta yayi very tight tanamai kuka sosai kafin ahankali ya cirota daga jikinshi ya jata ya bude kofa suka suka tsaya agaban closet wani doguwan fine rigan abaya yaciro mata sai binshi da kallo take tafashe dawani irin kuka tace "ina zamu?" ahankali ya zage zip din bayan riganta batare daya bata amsaba yacire mata rigan tana kallon fuskanshi tana kuka, ajiye rigan yayi yana kallon fuskarta itama asanyaye, cikin kuka ta dafa hanunshi tace "ina zamu meya sami Mummy na?" yana zage zip din bayan skirt dinta yace "nothing, Mum is fine wife" jan skirt din yayi kasa tsabagen rudewa bama tadamu ba yabi santala santala cinyoyin ta da kallo, doguwan rigan ya dauka ya samata da hijabi. Cikin kuka sosai tace "I.. I want to change" gyada mata kai yayi ahankali yasaketa tadau pad dinta ta shiga bayi da gudu tana kuka, wayarshi ya ciro yatura ma su Omari text su shirya d'an Mum na hospital ya rasu yanzun nan, shiryawa yayi shima yasaka wani light blue yadi mai taushi dayamai bala'in kyau ya fesa turare yana jiran tafito, fitowa tayi tana hawaye sosai ta karaso gabanshi tace "am ready" takalmin ta ya nuna mata ta zura flat shoe jikinta na rawa yarike hanunta suka fito daga dakin, akasa suka samu Omari da Abdallah sunci manyan kaya suma sunyi kyau kaman zasuje gasan kyau sai kallonta suke duk suka fice suka shiga babban jeep din Marwan, Omari na mazaunin driver Abdallah na gefe sai shi da ita abaya suka rufo sanan Omari yatada motar yaja suka fita daga gidan, ahankali ya kwanto da ita jikinshi, dago kai tayi ta kalleshi bakinta na rawa sosai cikin kuka tace "are you sure my Mummy is fine?" gyada mata kai yayi tareda lumshe mata ido yana sake kwanto da ita tai lamo ajikinshi tana sauke ajiyan zuciya.
Chapter 56 · 0% Book details