← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 63

Sashe 26

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Taci kukan dayafi na kusan minti takwas tana kallon kofan, da kyar ta lallaba kanta ta sadakar kawai in mutuwa ce ma shikenan Allah ya yafemata kura kuran ta, da kyar tacire hoodie jikinta ta ijiye agefe wani irin kuka tafashe dashi ganin yanda Abba ya raba rigar baccinta biyu gabaki daya jikinta awaje dan riganma ya tattare yay gefe ne, tsabagen yanda take kuka har muryanta baya fitowa ma da kyau, da kyar ta iya ta mika hannu ta kunna shower ruwan zafi kawai ya dinga zuba akanta tundaga kai har kafa kasa na gangarawa kasan bayin tana wani irin kuka, takai kusan 10 minutes ahaka saida taji knocking sanan takashe shower da sauri tadau towel ta daura tana kuka, ganin ba'a shigo ba yasa ta jawo jallabiyar tana wani irin kuka ta zura ajikinta tadan mike kadan taja jallabiyar daya mata yawa sosai kasa ta janye Towel din tasa akai tana goge gashin kanta tana kuka, bama zata iya fassara yanda takeji ba tsabagen bakin ciki, amma jitake kaman ta mutu kawai tahuta hakan yasa ta zame towel din daga kan ta daura akan fuskarta tana kuka sosai, bude kofan yayi ya shigo bayin yana kallon yanda har lokacin kuka take ta daura towel a fuska tana wani irin kuka, kitson kanta na diddigar da ruwa ahankali ya mika hannu ya karbi towel din dake kan fuskarta ya dauketa kaman baby jikinta na rawa sosai ta kule idonta yafitar da ita daga dakin ya zaunar da ita akan gado, wani balm haka ya dauko ya lakata ya shafa a gefen bakinta inda yafashe, yasake debowa ya shafa a gefen fuskarta dan wurin yadan tashi sanan ya tsugunna agabanta ya mika hannu yace "give me ur injured knee" jan jallabiyar ta kadan tai sama ta mikamai kafar jikinta na rawa kaman wacce za'a kashe tana kallon bakaken safan hanun nashi, hakan yasa yakarbi kafan ya debo balm din ya shafa akan gwiwar kafin ahankali ya dago kai ya kalleta yanda take nishi tana kallon kafan dan tasan gyara mata zaiyi, murya chan kasa yace "close your eyes" gam ta rufe idon tana kuka mara kara, wani irin ihu tayi da saida gidan ya amsa sakamakon jan kafar dayayi, bude ido tayi tana wani irin mugun kukan azaba ta dafa kafadarshi a mugun rude sabida zafi tanaso ta amshe kafar tana kuka tama kasa magana, sosai tabashi tausayi hakan yasa yakasa cigaba dayi ya saki kafar ahankali, dawani irin murya mai cunkushe da bakin ciki yace "stop crying, are you hungry?" girgiza mai kai tayi cikin kuka mara kara. "kwanta" kwanciya tayi da sauri kaman wata marainiya, murya chan kasa yace "sleep" da sauri ta kulle idanunta jikinta na barbar tana magana kasa kasa. "Mumy Mumy dan Allah kizo, wayyo Allah am scared, Mum mugun tsoro nakeji yau" yakai kusan 5 minutes akanta, yana kallon yanda take maganganu kasa kasa kaman irin sababbin mahaukatan nan kafin da sauri ya juya yafita daga dakin yanajin bakin cikin rashin illata mutumin daya mata haka. Da Omari da Abdallah yaci karo sun taso cikin bacci sun fito daga dakinsu sakamakon ihun dasuka ji na mace, atare sukace "Ya Marwan wacece tai ihu" alamu yamusu da surabu dashi kawai ya sauka downstairs ya kwanta akan dogon kujera zuciyar shi na wani irin tafarfasa, da sauri Omari da Abdallah sukai dakinshi ahankali suka bude kofan batare dasun shiga ba, kara ware ido Abdallah yayi yana kallon wicked Nurse dan bazai taba mance fuskarta ba yanda ta takure a kwance ta kankame jikinta tana kuka sosai idanunta a rufe tana pisipispisspis da baki basujin metake cewa, fuskarta da gefen bakinta yay jajir, da sauri Omari ya rufo kofan daga shi har Abdallah suka juyo zuciyarsu namusu wani irin zafi suka sauko kasa akanshi suka tsaya atare sukace "meya sameta?" tashi yayi ahankali ya zauna yana dafe kanshi kafin ahankali ya finciko Omari ya zaunar dashi gefenshi ya finciko Abdallah ma ya zaunar dashi gefenshi, kaman wani wanda ya bugu yace "wa..waya ce yataba ta? How dare he try to molest her? Wlh wlh every single pain that she's going through now saina rama mata double" yay shiru tareda daura hannunshi akanshi sai kuma ya janye ya mike tsaye wani irin ball yay da center table din palon na glass jikake rugugugu, wani irin ihu yayi ya daki kujeran one sitter da kafa da sauri Omari yatashi ya rikeshi yace "calm down Ya Marwan, calm down please" fizge kanshi yayi yay wani irin ihu. "leave me Omar" sai kuma yahau kan stair case da gudu, binshi sukayi bude kofar dakin yayi azuciye yana magana yace "who was dat man?" gani yayi tayi bacci atakure hakan yasa duk suka tsaya suna kallonta, ahankali Abdallah ya shiga dakin yaja bargo ya lullubeta ganin yanda ta takure kaman maijin sanyi, sai ajiyan zuciyan kuka take uhhu'uhm take, tsayawa yayi ya kafe fuskarta da kallo yanda yay luhu luhu wani irin kuka ne yazo mishi hakan yasa yajuya da sauri zai fita dakin hanunshi Marwan yarike da sauri ya fada jikinshi ya saki kuka ahankali yana shesheka, "Ya Marwan waya mata haka? Wanan ai zalinci ne, abun namin wani irin ciwo Ya Marwan wlh am not going to spare that man we will not spare him" shafa kanshi Omari yayi shima heart dinshi namai zafi sosai yace "we will not spare him Abdallah, stop crying" daga kai yayi ya kalli Marwan da ya rike Abdallah ne kawai amma kanshi najikin bango yay wani kala, ahankali yace "Ya Marwan calm down please" gyadamai kai yayi kafin yabude kofa yaja Abdallah suka fita Omari na binsu abaya.

*Idan kika karanta baki biyaba keda Allah*!!!

*Maman Abd Shakur*
Chapter 26 · 0% Book details