← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 63

Sashe 59

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*masu posting novel waje, kuda Allah*
*karki karanta in baki biyaba*
*in kinason littafin nan Zaki tura 300 3107021073 first bank aisha Muhammad, saikimin magana a watsapp 07012181461*

*BOYAYYEN MUTUN*

Wani irin bubbuga kafa Marwan yafara akasa kirjinshi na tafarfasa, yanamai suya kaman an hura wuta aciki, cikin fushi Abba yace "au bazaka kuyi magana ba ko, nace Marwan yamike tsaye mu bama hammata iska" cikin fushi Mum da batai niyyan magana ba tace "Alhaji!" afusace Abba yawani irin juyo ya kalleta yana nunata da hannu, yace "karki sake ki kira sunana makirar mata, annamimiya, wato kinyi iyakan bakin kokarin ki ki rabani da Princess kicire sonta a raina, amma kikaga sonta kainuwa ne araina dashin Allah, kikaga son princess zanen dutse ne araina, shine zaki sirfafo wanan karyan ki narka, kika bullo ta wanan hanyan kicemin wayanan yan daban yayyin princess dina ne? Yan uwanta ne bla bla bla, to sannu makira, kinji ko nace sannu makirar, mai bakin hali me princess ta tsare miki dakike kishi da ita? To bari kiji Allah ubangiji daya dauramin son Princess araina shi kadai ne zai ciremin shi daga raina, kuma wlh yau koma uban waye Marwan cikin su saiya sakin mini y'a, saiya saki baby girl dita, bazan kiwanci yarinya kimanin shekara ashirin da biyu babu wata uku ba, tai lumu lumu haka da ita, yarinya yar duddurma pakutu kaman kataba jini yafito wani yazo ya auremin ba, ai abunda bazata sabu bane wai taba nonon sirika, ya mori kiwona, kiwon danayi? Ina! " wani irin tashi Omari yayi cikin fushi ya kalli Abdallah yace "Abdallah get the check book from d car" ya kalli Abba dayawani gyara tsayuwa yana tale kafa yace "name your price Malam nawa ka kashe arainon kanwata? 100 million? 200 million? 500 million? How much just name it?" wani irin tashi Marwan da idanunshi sunyi jajir, jijiyoyin kanshi sunfito yayi ya kalli Abba yace "zan baka 50billion naira for rainonta, inma yafi haka name your price zan biyaka instantly" cikin fushi Abdallah ma yamike yarike hanun Ya Marwan dan yaga yanda hanunshi ke rawa and inhar yarike Abba zai iya kasheshi cikin fushi yace "Ya Marwan please mutafi, wlh baza'aba tsohon nan kosisi ba" wani irin ihu Abba yayi yawani irin kaima Marwan naushi a kirji amma ko gezau, yace "dama kaine Marwan? Dama kaine matsiyacin dibabbe wanda aka haifeshi babu cibiya shaidani, zo dan uwatata mubama hammata iska" wani irin jumping Ahmad yayi daga kan kujera yay wani irin ihu. "tirrrrrrr, yauwa Marwan dan Allah give him d beating of his life, karkai sparing tsohon nan, go Marwan" wani irin tunzura Abba maganan Ahmad yayi yay wani irin tsalle yadane jikin Marwan da zuciyarshi kewani irin zafi tsabagen fushi kanshi har wani irin rawa rawa yake, Abba yawani irin gannamai cizo a kirji yana nushin shi a ko'ina kafin ya dira kasa kuma yana nishi, fashewa da kuka sosai Nadeera tayi ta kalli Ya Muhsin da idanunshi kekan Abba da a yanzu jiya ke kaman yatashi ya kasheshi dan bakin ciki da tsanan halinshi, cikin kuka taja hanun Ya Muhsin tace "Ya Muhsin Abba yana dukanshi" ahankali Ya Muhsin ya kalleta yama kasa magana baida karfi ko kadan, da rarrafe taje wajen Mum tarike hanun Mum tace "Mum say something, Abba is beating him" kallon kwayar idonta Mum tayi tai shiru danhar cikin ranta sotake su uku suma Abba shegen duka dako tashi bazai iyayi ba, karan saukan Mari yasa da sauri suka daga kai, Abba ne ya kwashe Marwan dawani irin shegiyan mari, kawad dakai gefe Marwan yayi jikinshi nawani irin rawa ahankali yafara wani irin dunkule hannu da sauri Omari ya rike hanun koba komi darajan yayan shi da suma basa murna dahalin baban nasu, da kuma Mum dake son Nadeera tsakani ga Allah bai kamata ya daki Abba agabansu ba, wani irin shako kwalanshi Abba yayi cikin fushi yana jijjiga shi yana nishi yace "nace ka sakin min Y'ata, ka saketa, fight me now, tsoro na kakeji, fight me back Marwan, look me in d eyes, ka kasa kallona, ka kalleni muhada ido and fight me back like a Man, mu dambata, princess tasan wayafi chanchanta da ita, ka sakenmin yarinya ta inkana neman zaman lafiya" yakara marinshi tawani side din, da sauri Nadeera ta saki hannun Mum tazo wajen da gudu tana kuka, juyowa Abba yayi ya kalleta ya washe mata baki yana nishi kaman wanda yaje yaki yace "matsa baya my princess karna sameki garin dukanshi, kije ki zauna basai kin shigan min ba, I can take them down wlh, bakiga yanda natsuwa yasoma shigan shi ba, stop crying my baby girl, bazai iya dukan Abban kiba, he's to small for me, don't be scared okay" wani irin gyara tsayuwa yayi yana ware kafa ya daddage ya hambari Marwan akafa saida kafan Abba yay kara yay baya kaman zai fadi yay kara tareda yin baya da sauri ya kalli fuskan Nadeera dake kuka sosai ya daddage ya tsaya yana nishi sosai yace "am fine, am fine princess, stop crying, zan bashi kashine yau" yakara komawa yanadan dingishi dan kafan dayay hambari dashi tamai tsami, chakumo wuyan Marwan din da idanunshi ke kasa har lokacin yawani irin yi ya jijjiga shi yace "nace ka sakenmin my princess, ka saketa nace, bata saki" ya kaimai mari, fashewa da kuka Nadeera tayi tazo wajen da gudu tana kuka sosai tana wani irin yarfe hannu, tasa hannu ta janye hanun Abba daga kwalan Ya Marwan da idanunshi ke kasa har lokacin tace "stop beating him Abba, Abba mesa kake haka, ni I don't like you, bazan taba auren ka ba, koma abinda sukace gaskiya ne koma ba gaskiya bane u will always be my Abba, and ni babu aure tsakanina da Abba na, kaine wanda nasani amatsayin uba and u will always be dat, Abba please stop all dis, wlh bazan taba auren kaba, koka raba auren mu bazan taba auren kaba, tayaya ma zan auri babana? I don't like you Abba, I don't like you, I don't like yo... " wani irin wawan Mari Abba ya dauketa dashi yana huci, da sauri Marwan yadago jajayen idanunshi ya kalli Abban dawani irin idanu masu firgita mutum, da sauri Ya Muhsin da baida karfi ko daya yaji wani irin karfi yazomai ya mike tsaye yana dan dingishi yazo wajen ya tsaya a gefen Nadeera Marwan na dayan gefenta suna ma Abba wani irin kallon, wani kallo Abba yabisu dashi kirjinshi namai zafi kaman zai tarwatse kafin ya maida idanunshi kan Nadeera data fashe da kuka hanunta akan inda yamara ya nunata da yatsa yana dafa kirjinshi sabida yanda maganganun ta yamai wani irin shegen ciwo yace "P...Pr..Princess ni kika gayama magana haka? Ni Abban ki? Ni kike cema baki sona? Princess ni? Wat is my fault in loving you? Kinsan tun yaushe nake sonki? Princess ni" hawaye ya zubo daga idanunshi tsabagen yanda abin kemai ciwo, da sauri Nadeera ta ware ido gabanta na faduwa ganin Abba na kuka akanta, ahankali tace "Abbaa" hannu Abba yadaga mata yana girgiza mata yace "karki ce min komi, baniso naji komi, baniso naji me zakice, princess I fought the whole World for you, I stood by you through thick and thin, am always there to keep you company lokacin da maman ki ke abandoning naki tayi tafiyar ta kasashe, Princess I adopting you wen u were 3months old, u were this small" yanuna dan karamin yatsanshi yana share hawayen dayake yi, yace "I took you to the hospital aka miki check up, nakawo ki gidana nahadaki da family na, namiki suna, every sort of baby toy dat u could think of aduniyan nan nasai miki shi dakudina dakina yarinya, nasaki a one of the best schools da Nigeria keji dashi, I clothed you, hired one of the best nani, na kaiki Montessori kika fara tun daga creche har zuwa primary school, where turawa oyinbo ke koyar dake, kikai girma you told me bakison BSc Nursing normal school of nursing kikeso I took you there, d best damuke dashi agarin nan, St. Edward school of nursing and midwifery, nasai miki laptop, nai fentin dakin ki to your dream color baby pink, Princess I've always given you wat you wanted kafin na tai coughing dinshi out, I've always been there for you my baby girl, I know nai couple of mistakes but am human Ain't I?" yasake goge kwalla yana jan majina yace "and human make mistake, I wanted to wait for you kigama school of nursing dinki nafada miki everything sai muyi auren mu mutafi spain, but rashin Mum dinki shiya kaini namiki nai pushing dina har nai abinda nayi but it was never my intention" yafashe da kuka sosai yana goge idanunshi da hanun rigan shaddan jikinshi, yace "takan ki an zubarmin da hakora, wanan mutumin hit me badly, he injured me, he kidnapped you from me ya auremin ki, walls din stomach dina as am talking to you right now is very very weak princess, but dudda haka bantaba giving up ba on u, I've suffered alot because of you amma ko kadan sonki bai ragu a..a..rai..na..ba" yafashe da kuka sosai da sauri Nadeera data fashe da kuka dan maganganun Abba sun mugun tabata ta matsa zata kama hanunshi cikin wani irin kuka da tausayi Marwan yawani irin fizgota yace "let's go" yajata dawani irin force yay hanyar fita daga dakin da ita, wani irin ihu Abba yayi cikin kuka yarike Marwan gamgam yana kuka yana kallon Nadeera dake kuka sosai tana kallon shi ya mika mata hannu yana kuka harda majina yace "Princess don't leave me, don't leave me dan Allah, zan wulakanta, zan tozarta, My Princess karki bari yaraba ki da Abban ki, wayyo Allah princess kinaso Abban ki yamutu?" wani irin runtse ido Marwan yayi dan Abba yafara kaishi karshe zai kasheshi faa, ihu Ahmad yayi ya rike hanun Ya Muhsin da hawaye ya gangaro mai yace "na rantse da Allah Abba ya haukace, ko kaffara bazan yiba, kalli Abba fa yanda ya makalkale Marwan kaman dan biri alalo alalo, wlh Abba deserve to be examine and admitted in the asylum kai! The old Man head don loose noti fa" Nadeera kuka Abba kuka ya makalkale Marwan gam gam, ahankali Marwan yamika ma Omari Nadeera da hannu yace "take her away" wani irin ihu Abba yayi yay wani irin jumping ya rungume Nadeera tsam tsam yace "Princess karki bari arabani dake I will just die, I will die wlh, Princess dan kaunar dakike ma Manzo sallalahu alaihi wa sallama karki bari arabani dake, Nadeera! My baby girl, I need you, my princess, karki bari arabani dake" wani irin fizgo Abba Marwan yayi yawani irin bankare shi mercilessly kaman roba kafin yawani irin murde wutsiyar hanun Abba a zuciye jijiyoyin kanshi kaman zasu bullo tsabagen fushi jikake kakar kakar kasssas ya balle ma Abba wutsiyar hanunshi duka biyun Abba yay wani irin ihun azaba, wani irin ture Abba yayi yafada a tsakiyar dakin ya nuna shi da yatsa yace "never in your come close to my wife or touch my wife mugaffal" yawani irin ja hanun Nadeera dake kuka kaman zata mutu tana kallon yanda Abba ke kallon hanunshi da tana iya ganin yanda fatane kawai yarage tsakanin wutsiyar hanunshi da tsintsiyar hanun dan Marwan yakarya kashin tass, Abba nawani irin kuka yana kallon hanun yafita da ita daga gidan su Omari biye dashi yawani irin jefata cikin mota ya karbi key a hanun Omari suka shiga yawani irin ja motan da mugun gudu.
Chapter 59 · 0% Book details