← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 63

Sashe 12

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da aka kira magrib ta tashi plate din takai kitchen ta wanke ta ijiye sanan ta fito tana yarfe hannu ta wuce tai dakinta alwala ta dauro tasaka hijabi tahau kan dadduma tanacikin salla Abba yatura kofan ya leko ganin tana salla yasa ya wuce dakinshi, alwala yayo shima ya fice dan zuwa masallaci, tana idarwa karatu tayi dan taji fitan Abba tasan kuma sai bayan sallan Isha zasu shigo dukan su, saida aka kira sallan isha sanan ta tashi tayi tana idarwa ta linke dadduma ta cire hijabin, dan kwalin riga da zanin dake jikinta ta dauka ta daura sanan ta fice daga dakin tai falo rike da wayarta, zama tai akan kujera tana kallon film wayarta yay ringing da sauri ta dauka ganin Fauzy ce kafin ma tai magana Fauzy tace "ance wai anyi suspending dinki wlh school dinmu yan iska ne, Allah zai saka miki kinji Nadeera" murmushi tayi tace "bakomi ya kike yasu Mum da Ameer auta?" ajiyar zuciya ta sauke tace "Alhamdulillah, Ameer sunje masallaci da Abba, mum na dakinta, gobe zanzo kinanan ko?" girgixa kai tayi tace "wlh Ya Ahmad yace zamu fita" "aiko wlh kezaki zo jibin dan kiji rotten tomatoe" dan dariya tayi tace "naji to zanzo ran Sunday, amma bayan la'asar fa" kaman Fauzy zatai kuka tace "please babe tunda safe zakizo da magrib zaki koma bye banison jin komi" ta katse wayar dip hakan yasa taciro wayar daga kunne tanabin wayan da kallo. "lemme see dat phone" da sauri ta daga kai Ya Muhsin ne zaune kan daya daga cikin kujerun falon yana sanye da jallabiya brown, ahankali ta tashi takaimai wayar batare daya karba ba ya watsa mata wani irin mugun kallo yace "dawa kike waya?" ahankali tace "da Fauzy ce, Ya Muhsin dama inaso naje gidansu ran Sunday ne tunda gobe zamu fita da Ya Ahmad" hararanta yayi batare daya karbi wayan datake mikamai ba, dan murmushi tayi tace "naje please?" dauke kanshi yayi yaciro wayarshi daga aljihu yana danne danne kafin yace "fine ran Sunday na saukeki kafin nai tafiya" "ina zaka?" tai maganan kaman zatai kuka tana kallonshi, ahankali yace "Kaduna to attend one conference, will be coming back the next day dasafe" ahankali tajuya batare datace komiba takoma kan kujeran datake kai ta kwanta kaman marainiya bayan ta jefar da wayar kan center table, dago kai yayi ya kalleta yace "common tashi kibani abinci" tashi tayi tai dining din hakan yasa shima yamike yay dining din yaja kujera ya zauna, warmer ta bude ta zuba mai fried rice din a plate da chicken daidai lokacin Abba da Ya Ahmad suka shigo dining din suma suka taho ta zuba musu taje fridge ta dauko pineapple juice din dasuka hada ta zuba musu kafin ta koma gefen Abba ta zauna tai shiru, kallonta Abba yayi yace "bazaki ciba" kaman jira take tafashe da kuka hakan yasa duk suka tsaya dacin abincin suna kallonta, Abba dayafi kowa rudewa yace "wai menene kike kuka eh Princess?" share hawayen tayi da bayan hannu cikin hakin kuka tace "Abba ba Ya Muhsin bane zaiyi tafiya ba, kowa nata tafiya ana barina ni kadai a gidan" kafin Abba yay magana Ya Ahmad yay dariyan zolaya yace "nima tafiya zanyi yarinya sati daya zanyi zanje UBA seminar a lagos mainland" kara rushewa tai da kuka, Abba ya watsama Ahmad dake dariya harara ya dago kanta yana share mata hawayen yace "karki biyema Ahmad wasa yake miki, Muhsin ne kawai zaiyi tafiya kuma ai washegari da safe zai dawo sabida aikin shi, ashe ma anyi suspending dinki a makaranta baki fadamin ba, yanzu dai yayanki yasamu ya fitar dake case din ansamu glimpse of him, dan keyarshi ma aka gani ta CCTV camera kwara daya dake bayan asibitin daya kamashi, hakan kuma ya nuna abinda kika fada gaskiya ne yanxu dai ance bayan sati biyu ki dawo" murmushi tayi sosai ta kalli Ya Muhsin dake cin abinci shi tace "thank you Ya" gyada mata kai yayi Abba kuma yacigaba dacin abincin shi, ana gamawa duk sukai falo ita kuma ta kwashe kwanukan takai kitchen ta wanke ta gyara dining kafin tadawo falon ta zauna gefen Abba tanajin hiran dasuke na labarai, daganan kuma bacci yay awon gaba da ita wuraren shadaya, tadata Abba yayi ta mike ta wuce dakinta, da kyar ta chanza kaya zuwa kayan bacci ta kwanta sai bacci.

Washe gari sai after one suka fita ita da Ya Ahmad, kwalliya sosai taci tasaka blue lace mai dutse din gold, tayafa gold gyale tasaka gold takalmi da karamin mini gold hand bag, tai wani irin shegen kyau dako ya Ahmad saida ya yaba.

Parking yayi awurin paka motocin a park din suka fiffito, atare suka jera har zuwa wani wurin hutawa haka cafe ne da akai bukka ga kujeru da table a hadaddu aciki, order yafara musu na mock tails da chicken wings sanan sukai ciki suka zauna ya ciro waya kiran deejay tace "sun kusa karaso wa" ko 10min ba'a karaba ta kiranshi hakan yasa ya kalli Nadeera datai nisa a chatting da Fauzy yace "ke am coming" murguda mai baki tayi tace "nine ke?" amma harya juya yay gaba abin shi basu wani jimaba yadawo tareda wata kyakywar mace taci bakin hadadden doguwar riga suka shigo wajen tashi Nadeera tayi ta rungumeta tana murmushi tace "Anty barka da zuwa, please zauna nabarki a tsaye" tai maganan tana nuna mata kujera zama Deejay tayi suna hira abinsu suka ma manta da Ya Ahmad daya gama shaka yana hararan Nadeera, nan aka kawo mock tail da chicken wings din daya musu order daukan mock tail dinta tayi ta saka straw aciki tadan zuka sanan ta cire baki ta kalli Deejay tace "natafi nima nazagaye wajen Yayan mu nata hararana to nabaku gurin, asoye amma kar akone" tai maganan tana ma ya Ahmad fari da ido itadai Deejay dariya taketa musu, ficewa tayi daga wurin tana tafiya ahankali abinta tana sipping mock tail dinta tana zagaye gun, ahaka harta fito ta baki bakin hanya inda motoci ke wucewa, ajikin motarsu ta jingina tana facing hanya, hanunta daya rike da mocktail din dayan hanun kuma rike da waya tana daddannawa.

"p..park d car." yacema Omari dake tuki, gabaki daya hankalin shi nakanta, yanda take tsaye jikin mota tana danna waya dayan hanunta kuma rike da mocktail yasa yaji zuciyar shi na bugu, gangarawa gefen hanya Omari yayi yay parking yajuyo danya kalli wannashi ya tambayay maisa akai parking anan saiyaga hankalin na waje ma, ahankali ya juya danyaga maiyake kallo suda sukeda important work zasuje karbo wasu supplies na operation din gobe dazasuyi, wata kyakywar yarinya yagani tsaye jingine da mota bama yaganin face dinta sosai dan kanta aduke yake tana danna waya yake kallo, juyowa yayi ya kalleshi yace "Ya Marwan zamuyi latti fa, wats up with dat gurl why are you looking at her?" ahankali batare daya juyo ya kalli Omari dakemai magana ba yace "shiiii" hakan yasa Omari bai sake magana ba ya koma kujera ya ciro wayarshi yana dannawa.

Wani irin sanyi ne taji yana shiganta hakan yasa ta dago kai da sauri tana yatsine fuska tareda tura wayartata ajaka, takai hannun tana gyara gyalen jikinta tanadan kankame jikinta sabida sanyin, ahankali Marwan ya mika hanunshi dake cikin safan hannu ya daura akan glass din motar daidai ta saitin inda take ya daura dayan hanunshi kuma akan kirjinshi dake wani irin bugawa. Yatsine fuska tasake yi ganin hakanan she's not comfortable, kara gyara gyalen tayi daya rufe mata hannu sosai sanan ta juya ahankali ta koma ciki, wani irin kallo yake binta dashi yanajin wani iri dabaisan na menene ba harsaida ta bacema ganinshi, ajiyar zuciya ya sauke mai kara dahar saida yasa Omari juyowa yace "kodai jikin ne Ya Marwan" dan gabaki daya jiya da daddare ma basu gane kanshi ba, sosai yadinga zazzabi bayan sun koma gida, dan kome yakeyi ita kawai yake gani ko kadan baida sukuni yarasa gane kanshi, yarinya kaman aljana taki fita daga kanshi, girgixa kai yayi kafin yakarayin wani hucin yace "let's go" kunna motar Omari yayi suka hau titi.

Sai wuraren magrib suka baro park din, saida suka ajiye Deejay akofar gidansu sanan suka taho bayan ya tsaya ahanya yay magrib kafin sukai gidama ankira isha, yana parking yawuce masallaci itakuma tai cikin gida wanka tafara yowa ta shirya cikin simple gown tai salla kafin tacire tasaka kayan bacci tafada gado sai bacci da asuba ma Abba ne ya tadata taje tai salla tai karatu tafito ta hada musu breakfast.

Sai wuraren 12 narana Ya Muhsin ya shigo yace "ki shirya will drop u off kafin na wuce" gyadamai kai tayi ta wuce daki wanka tasake yowa ta shirya cikin doguwar bakar riga mai hade da baby pink color da Mum tasiyo mata daga 🇴🇲 Oman, bakaramin kyau doguwar rigan yamata ba gashi anbishi da stones, gaban madubi taje ta shafa hoda ta shafa man baki akan pink lips dinta sanan tai rolling gyalen rigan baki tadau small mini bag dinta baby pink tasaka baby pink flat shoe sanan tadau wayarta tafito, amota tasami Ya Muhsin hakan yasai tai motan ta bude ta shiga ta rufo, tace "gani Yaya" tada motar yayi batare daya kalleta ba yay horn mai gadi yabude musu suka fita, tafiyar kusan 20 minutes yakaisu anguwan su Fauzy, agaban gidansu yay parking baice mata komiba, hakan yasa ta juyo ta kalleshi kaman zatai kuka tace "Allah kiyaye hanya Yayan mu, please kadawo gobe kaji, byeee" gyada mata kai yayi sanan ya juyo ya kalleta yace "6 Adamu zaizo ya dauke ki so get ready kafin yazo karkisa yay ta jiranki" murmushi tamai tace "to, bye" tamai waving hannu tana murmushi, shima dan murmushi yamata yace "bye" bude kofa tayi ta sauka daga motan tai knocking gate din aka bude mata ta shiga tana ma Ya Muhsin bye, murmushi yayi yatada motar yay reverse yabar anguwan.
Chapter 12 · 0% Book details