← Book details Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 63

Sashe 31

Boyayyen Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

***
Wuraren karfe uku saura sukai parking akofar gidansu Abba, zare mishi bakin kyallen Omari yayi daga kan fuskanshi ya kwance ma igiyan hanunshi sanan ya bude kofan motan yace "fita" ahankali Abba da jikinshi ya mugun yin sanyi ya fice daga motar, sukaja motar dawani irin arnen gudu suka bar anguwan, yakai kusan 10min tsaye yana kallo hanyar dasukabi jiyake kaman yay kuka ko halan hakan zai sa yaji saukin abinda yakeji, juyawa yayi yabude gate ahankali ya shiga gidan da sauri mai gadi yataso yace "barka da zuwa Alhaji" ko kallonshi baiyiba yawuce ciki ya shiga barrander ya bude kofar dakinsu ya shiga Muhsin yagani da Ya Ahmad zaune akan dining ko wanensu ga abinci gaban su amma baci sukeba, Muhsin yay wani irin rama kaman bashiba, dukansu dago kai sukayi suna kallonshi shima kallon su yake jiyake kaman yaje ya rungumosu koyaji saukin abinda yakeji amma yasan sun tsaneshi hakan yasa yajuya ahankali jiki asanyaye yay hanyar corridor, tashi Ahmad yayi a zuciye yace "Abba daga ina kake? Abba where is Nadeera wai, ina kakaimana kanwarmu ne Abba?" dagamai hannu Abba yayi cikin kunan rai yace "Ahmad! please not now son" cikin fushi Ahmad yabude baki zaiyi magana hanunshi Muhsin yakama ya girgiza mai tareda zaunar dashi, binsu da kallo Abba yayi kafin yawuce ciki yay dakinshi zama yay akan kujera ya kama kanshi da duka hannayen shi biyu yana salati yana goge kwalla zuciyar shi na zafi sosai da kyar ya mike tsaye ya shiga ciki yayo wanka yafito, farar jallabiya kawai yasaka ya dauro alwala yafito falo bai tarar dasu Muhsin ba hakan yasa ya wuce masallaci yayo sallan la'asar ana idarwa yadawo cikin gidan afalo ya zauna yana huci yace "wlh bazan yarda ba" saikuma ya mike da sauri ya wuce dakinshi, wayarshi ya dauko yadawo falo ya zauna yakira commissioner of police ringing daya ya dauka tsabagen yanda ranshi ke tafarfasa dishewa muryan shi tayi da kyar yace "kwamission i want to file a complain yata kidnapping dinta akayi fa, first thing tomorrow morning zanzo danna baku statement dina yanzu am really not feeling well, banda lpy sosai" magana commissioner yamai kafin Abba ya gyada kai ahankali yace "ok thank you so much friend" katse wayar yayi ya jefar akan kujeran dake kusa dashi, shigowa Muhsin da Ahmad sukayi dakin kan dogon kujera suka zauna suna kallon Abban daya kafe tv da ido saikace yana gane me ake cewane dan hankalin shk baya wurin, ahankali Muhsin yakira sunanshi yace "Abba" dagamai hannu Abba yayi batare daya kallesu ba yace "please not now am begging you people kurabu dani inji da abinda ke damuna, Muhsin Ahmad kurabu dani, you boys should leave me alone, let me be" ya maida kanshi jikin kujera yana bubbuga kafa tsabagen yanda zuciyarshi ke tafarfasa, azuciye Ahmad yabude baki zaiyi magana sukaji maganan Mum daga waje, daga kai dukansu sukayi suna kallon kofan harda Abba bude kofan tayi ta shigo tana sanye cikin wani irin shiga ta alfarma, wani ubansu material ne blue ajikin ta daya amsheta sosai ta zuba warwarayen gold da sarkan gold ajikinta, fatanta yay wani irin haske tai wani fresh da lumu lumu da ita, inka ganta zata rantse ba ita ta haifi su Muhsin ba yanda takeda kyau fatarta har wani irin shining take tana wani irin kamshin turaren larabawa nan, hanunta daya rike da wayarta kirar iPhone x dake kunenta tana magana da harshen turenci dayan hanunta kuma rike da hadadden handbag dinta na vintage, gateman biye da ita yana gunguro jakan tafiyarta na LV, matsa mai tayi ya wuce ciki ya ijiye ya fito ta cigaba da wayan datake yi tana maganan kudi, wani irin kallon haushi Muhsin da Ahmad ke mata yarta ta bace saiyau zata dawo yau dinma business magana take, wani irin tashi tsaye Abba yayi yayo inda take ko kunyan su Muhsin baijiba yasa hannu yawani irin jata matsar da wayan tayi daga kunenta tana binshi tace "Alhajina is an important business call wait please mana" ko jinta baiyiba yajata suka shiga corridor tana kallon su Muhsin dasuke binsu da kallo dakinshi Abba ya shiga da ita ya fizge shigeyar wayar dake kunenta ya yar nanfa labari ya chanza salo....
Chapter 31 · 0% Book details