← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 60

Sashe 6

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasun su na zama ne a kasashen waje, wasun su na wasu garuruwan, wasu na wadansu anguwoyin acikin garin Nukaa din wadanda aure ya sauya musu wajajen zama. Ma'ana mafi yawan matan dangin dake auro wasu mazan da ga wasu dangin... Duk kuwa da kashi tamanin na cikin dari auren zumunci suke yi. An taba samun sabani ne sau biyu akan wasu auren da aka hada na zumunta. Har abun ya fara kawo tangarda da son rabuwar zumuntar. Dakyar aka iya sasantawa aka kuma kawo karshen hadin auren zumuntar. Ya zama dik me son auren babu takura yaje waje ya auro...

×××××

Hancin motocin su Amb. Junaid ne da iyalan sa suka shiga dandatsetsen katafaren babban gidan na kandem estate.

Babban gidah ne daya ci sunan a kira shi da 'aljannar duniya' komai yaji. Domin tsayawa ma a baku labarin yadda gidan ya kawaatu da komai na rayuwa tabbas bata lokaci ne. Sannan zuciya zata iya tantama akan hakan.

Masu gadin suka tashi da sauri suka yo kan motocin da number jikin plates din motar ke rubuce da manyan bakin kandem 01 zuwa kandem 05...

Tsayawa motocin sukayi. Amb junaid ya bude kofar mazaunin da yake. Masu gadin da maaikatan gidan maza sukayi dafifi akan sa. Sanin shi mutum ne mai karamci da adalci, dattako ya kamata, da Kuma kyautatawa da jikin sa, gumin sa da kuma aljihun sa.

Haka ya rika basu hannu suna musaba. Bakin sa abude yanata musu murmushi suma suna rissina masa cike da girmamawa.

Sai da ya tabbatar ya gaysa da kowa acikin su sannan ya daga musu hannu . Suka rufe masa murfin motar direbobin suka ja motar zuwa ciki.

Kai tsaye motocin sukayi bangaren mahaifiyar sa... Wanda shima nasa gidajen a sashen suke. Gate ne kawai ya raba su. Nata yayi dama nasa ya kalli hagu. Amma da yar tazara a tsakani.

Motocin suka danna kai cikin gate din. Suna karasa parking suka furfuto daga cikin motar . Shine agaba suna biye da shi a baya...

Ya doka sallama ya shiga cikin babban parlorn. Dattijuwar hajiyar na zaune akan wata kujera samfurin Italy. Babban Qurani ne a hannun ta. Fuskar ta saqale da gilashin kara ganin ta.

"Hajjaju na.... Hajiya ta" ya fada da sauri cike da madaukakiyar murna marar misaltuwa

Ta dago ta kalle su tana amsa sallamae. Murmushi tayi faffada. Ta mayar da kanta kan quranin da take karantawa. Ka'dane sai ta kai aya take ajiyewa. Allah ya temaka tana karshen shafin tana karashewa kuwa ta daga hannun ta tana addua kamar ko da yaushe . Suma suka daddaga hannuwan.

Amb Junaid nata kada kai yana cewa,

"Aamin, Allah ya amsa... Allah ya amsa Hajiya... Amin Amin."

Karbar Qur'anin yayi ya ajiye a inda take ajiyewa.

Tayi murmushi tana kallon su daya bayan daya,

"Allah yasa Qur'ani ya cecemu. Amin"

"Amin Hajiya"

"Aamin Amin"

"Allahumma Aamin hajia."

Suka shiga amsa adduar da tayi. Domin Hajiya Maryam akwai Ibada da yawon karanta alqurani. Tunda kananuna shekarun ta har girman ta. Shi yasa Allah ya amince duk tsufan ta ganinta bai tafi ba. Tana iya karanta komai idan rubutu yayi karanchi ne take karawa da temakwan gilashin karatu na kara girman ganin rubutu.

"Hajjaju barka da Rana... Mun same ku lafiya? Ya jiki hikin na ki? Fatan komai da komai kalau Hajiya? Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa yasa kifi ha ka, Amin...."

"Amin junaidu, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka junaidu."

"Amin Hajiya Amin."
Ya matsa daf da ita. Hawayen dadi daya nabin daya a fuskar sa. Duk girman sa idan yana gaban hajiyar su ganin sa yake dan karami.

"Allah ya albarkaci zuriyar ka junaidu. Allah ya albarkaci dukiyar ka junaidu, Allah ya albarkaci komai na ka junaidu. Allah Amin."

"Aamin Hajiya... Aamin."

Nan da nan daya bayan daya suka rika tasowa suna gaishe da Hajiya tanata amsa musu. Amb Junaid yaki matsawa daga gaban ta sai ma sake gyara zama da yayi sosai yana jin sa cikin wani irin nishadi marar misaltuwa

Amaal ce karshen tasowa ta nufi wajen hajiyan tana murmushi. Hajiya Maryam ta bude baki tana murmushi.

"Ahh takwara ta ce? Zo nan yar albarka..." Ta janyota jikin ta tana shafa kanta,

"Hajiya ya kafar ta ki?" Ta tanbayeta tana mammatsa mata su

"Da sauki maryama. Nagode kinji? Je ki huta Allah yayi albarka Amin."

"Bangaji ba Hajiya."

"To ai shikenan idan sarkin agaji yazo ka kyale."

Suka saki dariya baki daya idan aka tsame hadiza da iyalan ta da kuma ruwaida da nata yaran da ke ta kumbura zasu fashe...

Wayar sache tayi kara. Ya janyota da sauri ya shiga wajen sakonni. Dubada ko da yaushe sai an ajiye masa saqo kala kala ta kafafai da dama na social media da ma text message ta ainihin number sa.

Amma duk da tarin lokutan da aka diba bai taba ko sai daya ba zuwa dan a bincika masa mai bibiyar tasa ba, Ya dai barwa kansa sanin koma wanene, BAKON MUNAFIKI!! ne wanda (BANA MUTUM DAYA BANE)

Dubada yan uwa da dama sun juya masa baya ciki harda wadanda suka fito ciki daya wato uwa daya uba daya ..Ya Kuma tabbatar wa kansa BAKON MUNAFIKIn ne ke qissima komai. Amman koma wanene ko ma wacece da sannu gaskiya zata bayyana.. Domin komai nisan dare gari zai waye. Allah zai bayyana mai gaskia .

Sakon ma dariya ya bashi alokacin daya kai karshen karantawar. Ya sake karantawa daga farko yana girgiza kai kawai cike da rashin bacin rai,

"Ban hane ka da kada ka waiwayo zuriyar kandem ba? Ba ka ji ba sai da ka dawo gidah ko? To ka sani cewa ka debo ruwan dafa kan ka.... Ka jira ka ga abubuwan da zasu biyo baya....."

Kashe wayar yayi baki daya ya zurata a aljihu. Ya saka hannun sa duka biyun ya janyo kafar mahaifiyar sa daya ya dora akan cinyar sa. Ya yinda amaal ke matsa mata daya kafar.

Heat Balm din da ke hannun sa ya bude ya lakuta ya shafe kafar hajiyan da ita ya shiga matsa mata ahankali. Yana ta mata hira..

Tuni maaikatan suka shiga kawo musu abinci da sauran abubuwan sha dana motsa baki. Suka cikata gaban su da shi....

Kowanne ya shjga diba yana ci yana korawa da lemo da ruwa mai sanyi... Yayin da maaikatan ke ta kai kawo akan su sunata hidima akan su......

_Afuwan abisa rashin ganin cigaban paid pages na littafai biyu daga cikin ZAFAFA BIYAR. Hakan ya faru ne sanadiyar rashin lafiya da ta riske mu. Muna baku hakuri dan Allah. In shaa Allahu da mun karasa samun sauki zaku ji mu duka da yardar Allah.... Mungode da zabin litattafan zafafa biyar. Allah ya kara budi_

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[8/7, 7:27 PM] Hafsaat💞: _*BAKON MUNAFIKI!!!*_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
_👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

__AREWABOOKS:MSSXOXO_
_WATTPAD:MISSXOXO00_

_PAID PAGE:07_

_________
     Sai sha biyu saura kwata na dare tukun sannan suka fara yiwa Hajiya sai da safe suka nufi sashen su.

Amb. Junaid ya gyara zaman sa sosai a gefen Hajiya daga kasa. Ya cigaba da matsa mata kafafun nata ... Tana ta shi masa albarka.

"Allah yayi maka albarka.... Nagode nagode nagode. Ka je ka huta."

"Ai ban gaji ba hajjaju. Ko dai bacci kike ji?"

"Baccin ma ina jin sa.. Kun shisshhga wajen yan uwan kuwa?"

"Wallahi bamu zazzagaya ba Hajiya. Nan kawai muka yada zango..Da safe in shaa ALLAHU zamu jajje. Da ke sanda muka zo din nasan yawanci suna wajen aiki. Basu dawo ba da yawan su shi yasa."

"Toh Allah ya temaka... Idan Allah ya kai mu goben sai ku shisshhga."..

"Aameen hajjaju"

Dan gyangyadi ta fara yi. Charbin hannun ta da take ja har ya fadi kasa, da sauri amb junaid ya sanya nasa hannun ya gyara mata natan da kuma carbun daya fadi a kasa yadakko ya ajiye mata a gefen ta.

Ta farko da sauri tana sosa gefen idon ta na dama,

"Junaidu.."

"Naam Hajiya..."

"Ba dai bacci ka fara ba ko.?"

Dan murmushi kawai yayi ya girgiza kansa cike da girmamawa.

"Kaje ka kwanta dare ya ja."

"Toh Hajiya in shaa ALLAHU..."

"Kunyi magana da yan uwan na ka kuwa?"

"Eh munyi a group chat."

"Na'am.. Guru me?"

"Afuwan... A kafar sadarwa ta yanar gizo dinnan da ake yanzu.."

"Ma shaa Allah! Allah ya kara hade kawunan ku Amin."

"Amin Hajiya... Kuna samun su baba kuwa a waya ko har yanzu?"

"Ana samun su mana... Dazu ma nan an kira sadiya ta kawo mun muka gaisa. Wani abun ya faru ne? Kar ka boye mun"

Yayi saurin girgiza Kansa. Don ba yaso ko kadan ya sanyata cikin damuwa.

"Babu abunda ya faru hajiyar mu...Allah ya dawo dasu lafiya Amin."

"Allahumma Aameen."

Ya sake gyara zaman sa cike da girmamawa ya ce,

"Hajiya bari naje.... Kema gwara ki kwanta. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana da imanin Allah."

"Allahumma Aameen... Junaidu. Tare da ku duka. Allah ya tashe mu lafiya."

"Allahumma Aameen.."

Mikewa tayi ahankali da ga kishingiden da take... Tashi yayi ya dakko sandarta da ke gefen tv..

"Hajiya muje ko?"

"Da ka bari sadiya ta mun rakiyar ai."

"A'a Hajiya ... Bari nima na yau samu ladan."
Chapter 6 · 0% Book details