← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na dawo Hayateey.... Washh! na gaji"

"Sannu... Ga abinci can an gama ai, Na zubo miki?"

"Dan kadan amma ba yunwa nake ji sosai ba munci gurasa."

"Tohm.."

"Yaya ya dawo?"

"Ya dawo..Amma ya sake fita"

"Oh okay...."

"Yi sauri ki gama zamuje kasuwa"

"Kasuwa?"

"Eh sayayyar abubuwan da zaa dafa wa baki... Da zan aika iya kuma kar na manta dawasu abubuwan"

"Baki kuma?"

"Oh eh... Aminin abbiey dinku ne zasu zo da matar sa inaga da hisham ma."

"Okay ALLAH sarki... Zuwan me kuma?"

"Ai wai Nukaa zasu dawo gaba daya... Kuma akwai maganar da zasuyi wai muhimmiya.... Abbiey din naku yace shima bai san maganar meye ba dai... It shall be well"

"Da zama gaba daya a Nukaa ?" Ta fada tana gwalalo idanu

"Eh......"

"Allah sarki..."

"Yi sauri ki ci abinci.... Ki gama dai komai kizo mutafi"

"Tohm..."

Haka dai ta karasa dukkanin abubuwan da zatayi... Suka tafi kasuwar.. Suna dawowa suka fara abubuwan dik da suka dache na daga girkuna, gyaran gidan da sauran su....

Yamma lis sai ga shigowar motocin su gidan cikin convoy....
___

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/13, 11:37 AM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 30_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

   A jere motocin suka shiga cikin kandem estate... Kai tsaye suka nufi faada inda za'a sauke su... Ranar daman ba'ayi zaman faada ba saboda mai martaba na da manyan baki... Kwana biyu kuma baya jin dadi sai wazirin sa ne ke zama...

Suka bubbude motocin suka furfuto...Harda masu aiki da matemaka na farin kaya..

Suka furfuto daga shiga cikin motocin bakin su dauke da sallama... Aka shiga amsa musu ana musu lale marhaba

Sunyi kyau cikin kayan da su kayi matukar dacewa da su....

Mahaifiyar Hisham tayi shiga ta alfarma cikin wani dandatsetsen lace daya sha kudi ya koshi.. Ya sha uban su stones da suka kara masa kyau da kyalkyali...

Da ma'aikatan ta na biye da ita ..  Sai Hisham dake sanye cikin manyan kaya da sukayi matukar karbar jikin sa..

Zatin haibar sa ya sake futowa. Tamkar an kara masa kyau saboda yadda ya sake wani irin kyau lokaci daya..

Alhaji Abubakhar yana gaba suna biye da shi da da sauran maaikata suka shjga cikin faadar da aka yo musu iso..

Cike da farin ciki marar misaltuwa sarki junaid ya fara murmushi zai mike daga zaunen da yake Alhaji Abubakhar ya tare shi yana rissina masa,

"Wane mutum.. ranka ya dade... Allah ya jya maka..." Ya durkusa yana sara masa..

Sarki Junaid ya dawo kusa da shi ya zauna yana mai bashi hannu suka gaysa,

"Godiya nake yallabai.. Allah yakara lafiya da nisan kwana... Mai Nukaa gaba dayan ta

Sarki Junaid yayi murmushin kalaman da Alhaji Abubakhar yake gaya masa yace,

"Tare da kai aminin kwarai... Alkhairin Allah ya bi maka a duk inda kake.."

"Allahumma Aameen..",

Nan take aka fara gayshe gayshe a fadaar cikin girmamawa da sanin ya kamata..

"Ah harda babban pilot...?" Sarki Junaid ya fada yana kallon Hisham,

Hisham din ya matsa kusa da shi yana murmushi hadi da sosa keyar sa yace

"Eh ranka ya dade. ... Ban koma hutu ba tukun"

"Ma shaa Allah... Allah ya bada sa'a ya kara tsarewa."

"Allahumma Aaameen.."

Nan da nan maaikatan suka fara cika gaban su da kayayyakin motsa baki kala kala da abun sha.. lamarin sai wanda yake wajen kawai..

Hisham sai dan waige waigen fadaar yake yi. An sake kawaata ta da kayan more rayuwa yan waje.

Hajia Aisha mai dakin Alhaji Abubakhar yana gefe tare da su Hajiya Ruwaida... An zuzzuba mata komai a plates a gabanta.

"Ina sauran yaran ne.... Wannan ne bansani ba?"Cewar Alhaji abubukahr hadi da nuna Al-mustapha daya shiga faadar ba dadewa.

"Barka da yammaci."

"Barka dai..."

"Al-mustapha ne... Babban 'dan mu .. shine na fari awajen Yaya jalaludden sai kanwar sa Fatima Yusra."

"Allah sarki... Ga kamar nan kuwa... Ai ku da yake ma shaa Allah ana debo kamanni."

Shi dai Al-mustapha yana gefe sai kakaro murmushi kawai yake.. Hajia maryam ce tasa shi agaba lalle ya tashi ya shiga cikin mutane yan uwa ya dena raraa gefe yana komawa baya.. don sam Al-mustapha bayason hayaniya. Dik inda aka cika waje to fa tashi yake yi ya bar wajen kome akeyi.

"Ai ma shaa Allahu kam... Ana debo kamanni." Jamila Ina yaran nan ne?"

"shiryawa suke... Zasu zo in shaa Allahu..",

Tana fada Hisham ya samu kansa da sauke katuwar ajiyar zuciya.. Daman so yake kawai yayi tozali da Amaal sahibar sa..

     ×××××.   

Amaal na daga zaune akan gadon ta tana gyara zaman agogon ta data saka shi a wutsiyar hannun ta ..

Ta dan dauki wayar ta tana kallon fuskar ta ta camera.... Ta gama gyara komai ta dakko mild turaren ta (marasa karfi) ta faffesa..

Hindu dake tsaye awajen closet dinta tun dazu rike da wayar a hannun ta. Lokaci zuwa lokaci takan saki tsaki tana sake duba fuskar wayar da alama.. Sako take jira ya shigo. Domin tun jiya batada sukuni. Amaal na jiyo Hindun da daddare tana gayawa su ikhram saurayin ta Habibi Talba bai neme ta ba. Ta kira shi baya dauka ta kuma masa magana ta WhatsApp nanma beyi responding ba..

Ji kake taratststs... Wayar hannun Hindu ta fadi a kasa dai dai lokacin da amaal ta mike zata futa... Ita kuma Hajiya hadiza tayi sallama dakin nasu tana,

"Ku futo abbiyen ku yana tanbayar ku bakin sun zo...",

"Kan babban balain can....." Hindu tayi kukan kuraa ta cafki wuyan Amaal.

Amaal ta shiga neman kwacewa tana,

"Meye haka? Mena miki.."

"Menene Hindu .?" Hajjya hadiza ta tanbayeta tana kokarin raba su

Hindu ta fashe da kuka tana mai nuni da Amaal.

"Allah ya isa tsakani na da ke... Allah ya isar mun Allah ya miki abunda kika mun... Wayyo Allah na"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Yaya Hindu? Me zan miki? Wallahi ba abunda na miki.. Meya faru dan Allah?"

Hajiya hadiza ta buga mata harara ta karasa kusa da Hindu ta riko ta tana janyo ta jikin ta cikin muryar lallashi tache,

"Wani sharrin ta miki? Me ta hada miki? Halin uwar ta ta dakko ai... Mamugunta masu mugun baki."

"Ta rabani da shi Mama.. ta raba mu"

Amaal ta saka hannuwan ta dafe kirji don batada masaniyar lefin da take ikirarin tayi mata shi,

"Da wa ta raba ki Hindu? "

"Kinsan rannan tare mukaje school da ita ai... Malamin su ne... Muna fa wayar mu bakiga hirar da mukeyi da shi ba.... Mun fuskanci juna sosai ..Tunda muka rabu na dawo gidah naga be neme ni ba ba waya ba ba magana, Dana kira shi baya dauka.. beyi responding to messages din da na tuttura masa da su ba.... Shikenan innalillahi wa inna ilaihi rajiun.."

"Hindu ki nutsu ki gaya mun meya faru... Wani sharrin ta kulla miki haka?"

Hindu taja hanci tana cigaba da tsiyayar da hawayen fuskar ta tache,

"Yace mun shi Amaal dinnan yake kauna yake kuma burin ya aura... Wai shi da yan gidan su zasu zo wajen abbiey su nemi auren ta... Harda cemun dan Allah na fada agidah shi dagaske yake ba da wasa ba ya kamu da kaunar ta... Wannan wacce iriyar musiba ce? Wane irin bakin asiri ne sukayi haka suka raba mu farkon haduwar mu da shi?'

Amaal na tsaye sai ta zube akan gado tana dafe kirji.... Idanuwan ta sun fuffuto waje,

"Shegjya algunguma me raba soyayya..." Ikhram ta fada tana banka mata harara,

"Makira dangin asiri ba.." cewar Ikhlas tana tabe baki..

"Dama wallahi tun ba yau ba nasan farin jinin yarinyar nan bana Allah bane... Har muka gama school duk mazan ajin mu son ta suke.. kowa yace itace crush dinsa..." Najwa ta fada itama tana kallon amaal din hade da tabe baki..

"Har teachers kin manta? Abun da zai sake daure miki kai kowa fa? Duka mazan don balain bakin asiri..." Na'eelah dake gefen su ta fada itama..

Ita dai Amal hawaye ne take masu zafi suka fara zubowa daga idanun ta.. maganganun su na dada daga nata hankali.... Ita dai tasan tunda take bata taso taga Hayateey dinta na asiri ba.. kusan su aka tsana a dangin gaba daya ma sai yan shekarun da basu wuce biyar ba komai ya fara warwarewa akeyi da su..

Farin jinin kuma tun tana karama tasan haka kowa yake cewa yana sonta. har tayi ta kuka tana gayawa Hayateey ita ta gaji...

"Kina che me?" Hajiya hadiza ta tanbayi Hindu tana jujjigata idanunta tamkar zasu fadi kasa saboda tsabar tashin hankali sai zaro su take.
Chapter 30 · 0% Book details