Sashe 37
Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu murdaddun maza katti har biyu ne daga gefe can a zaune sun seta ta, Daya da kulqi a hannun sa dayan kuma wani abu ne a paper a nannade yanata busawa kana kallon sa kasan na bugarwa ne . Saboda yadda yake jin sa a duniyar sama ta mashaya yana ife-ife....
Dayan da ke busa sigari me kulqi a hannu ya mike daga zaunen da yake ya nufi inda Amaal take a 'daure a kujera...
Ya sanya hannun sa akan gefen fuskar ta yana tafiyar tsutsa da shi. ... Sai mutsu mutsu ta keyi tanason ta kwace kanta, hawaye na ambaliyar kwarara daga idanun ta . Ga hayakin tabar da ke dayan hannun sa na damun ta sai hawa mata kai yake yi.
Cikin muryar sa marar dadin sauraro mai tattare da doyin tabar da yake afawa yace,
"Bamu da damaar mallakar ire iren ku sai dai kallo daga nesa .. ko a talabijin amman yau ga aljannar duniya agaba na... Dole na fanshe tarin kwadayi na akan ki yammata...."
Ya saka hannun sa ya yage hijabin da ke jikin ta tun daga farkon sa har karshe ji kake kyet ya raba shi biyu... Ya tuge hular kanta ya wullar a gefe itama..
Ya rankwafa yana sunsunar gefen wuyan ta .. ya daga yaja numfashi yana lumshe idanun sa...
"Yammata.... Kin gama haduwa... Maza zo ka sunsuna daddadan kamshin dake tashi daga jikin ta." Ya sake saka kofofin hancin sa akan gashin ta yana sunsuna.. tare da saka hannun sa akan belt din jikin sa yana kuncewa ahankali..
Hawaye nata kwarara a idanun Amaal.. sai kokarin kwance wa take ta kasa. Dayan da ke zukar abun shaye shaye ya mike yana tangadi saura kadan ya faada kan Amaal.
Ya saka hancin sa yana sunsunar gefen kunnuwan ta da gashin nata... Ya saka hannun sa a tsakiyar wuyan ta yana wani tafiya dashi ahankali ya kusa kai tsakiyar kirjin ta kenan aka bugo kofar da karfi..
Al-mustapha ne ya fara shigowa sauran na biye da shi. Da alamar ma shi ya bugo kofar ta fado kasa.
Dai dai lokacin da idanun sa suka kai kan gardayen da ke tsaye kan Amaal din. Daya hannun sa kusa da kirjin ta. Dayan kuma ya saka hancin sa akan gashin ta.
Cikin zafin nama ya karasa ya saka hannu ya wanke fuskar wanda yasa hancin sa akan gashin Amaal da marika lafiyayyu guda biyu. Tare da saka kafa ya shure dayan da hannun sa ke wuyan ta.
Ya shiga dukan sa da iya karfin sa.. Aayan ma ya kamo dayan ya fara dukan sa.. Hajiya jamila ta fashe da kuka ta karasa kusa da Amaal din jikin ta nata rawa ta saka hannu ta yage abunda aka nane bakin ta da shi,
"Ha... Ya.. Teey" Ta fada a wahale a kuma rarrabe tare da fashewa cikin matsanancin kuka.
Al-mustapha ya zare suit din dake jikin sa ya runtse idanun sa ya sakata akan kirjin Amaal din dake daga ita sai doguwar riga mai gajeren hannu. Wuyan v style... Tunda dan shaye shayen ya yage mata hijabi ya wullar da hular kanta.
Ya fara kokarin kwance daurin da akayi mata Hamid na taya shi. Gwaggon court ta zare babban dankwalin ta ta yafawa Amaal din. Itama hawaye tuni suka fara zuba a fuskar ta,
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Wallahi Adamu sai Allah ya tambaye ka.... Amaal jika ce fa awajen ka. Wannan wane irin wulakanci ne? Ka kawo ta nan hakan bai isa ba. Kasa akayi mata wannan mugayen kullewar a hannuwa da kafa. Aka kuma rufe mata baki sai kace a film? Tsabar mugunta? Hakan bai isheka ba kuma ka hadaata da maza gardaye yan shaye shaye suka a tare da ita a daki daya. Kalli yadda muka shiga muka sameta a halin da suka sanya ta? Kaicon ka Adamu kaicon ka. Allah ubangiji yayi maka yadda ka mata." Bappah Usayn ya fada yana girgiza kai.
Bappah Maher ya kasa cewa komai saboda tsabar dimaucewa. Ya juya ya cukumi wuyan Kawu Adamu. Ya saka hannu ya zabga masa mari yana hawaye yace,
"Allah ya isa... Allah ya isar mata, Allah yabi mata hakkin ta akan ka. Ka nada jikoki ai ka sani zaa yiwa naka gwargwadon yadda kayiwa wannan yarinyar koma fiye da haka.. Ka sani wallahi sai Allah ya wulakanta ka."
Haka dai kowanne ya shiga aibata shi yana fadar albarkacin bakin sa. Sarki Junaid ya koma can gaban bango ya jingina. Ya kasa cewa komai.. sai hawaye da ke futa daga idanun sa.. ya saka kasan rigar sa ya goge.. Gaba daya yama kasa sanin abunda zai yi.
Aka kunce Amaal ta kasa takawa saboda rawar da jikin ta yake ba karfi kwata kwata a tattare da ita.. Gwaggo Aisha da gwaggon court ne sika rirriketa gefe da gefe..
A wahala tace,
"Ruwa..."
Aayan ya fita da sauri sai gashi ya dawo da robar ruwa guda daya ya bude ya mika mata, tanata kokarin zama Gwaggon court tace da ita,
"Sha mana amaal"
"Zama zan bakyau shan ruwa a tsaye"
"Allah sarki yairnya mai hankali.... Allah ya miki albarka. Tabbas annabi yace ko kasha ka amayar."
Dss Bappah Hassan ya bawa dama suka shiga ciki da handcuffs suka daddaure hannuwan gardawan,
"Har na wannan matsiyaciyan... Allah wadaran naka ya lalace. " Bappah Usayn ya fada yana mai nuni da Kawu Adamu
Aka garkame hannuwan sa shima aka tasa keyar su suka fita wajen gaba daya.. sarki junaid ya rungume Amaal tsaf ajikin sa yana hawaye itama tana.yi. hajia jamila na gefen su tana hawayen itama.
" A wuce asibiti da ita tukun" Bappah maheer ya fada yana shiga gaban mota
Duk suka shisshiga motocin su... Aayan sai hakuri da sannu yake bawa Amaal ya bude mata mota ta shiga. Al-mustapha nata kallon su ya kasa ce mata komai shi kansa bai san dalilin hakan da yayi ba..
Suka dunguma sukayi wani babban asibitin kudi da ake ji dashi a kandemi... Nan da nan likitoci suka karbeta, bappah maheer yace ayi mata general checkup. Aka fara yi hadi da saka mata karin ruwa saboda rashin kuzarin jikin ta.
Yayin da su kuma suka tsaya carko carko wasun su a zazzaune suna jiran agama yi mata dukkanin abubuwan da suka dache,
"Allah ubangiji ya tsine maka albarka Adamu. Allah ya la'ance ka ya 'dai'dai ta ka..." Bappah Maher ya fada yana mai nuni da Kawu Adamu da yatsa cikin dana sani da dimbin damuwa..
Yanata doka tsaki idanuwan sa na kan gardayen da Kawu Adamun ya sasu tsaron Amaal.
Kawu Adamu da alama zuciyar sa a kekashe take. Don chingam ma yake taunawa tamkar tsohuwar karuwa..
Dik wasu gwaje gwaje anyi mata su... Babban abunda suke fargaba bai faru ba. Martabar ta na nan kaman kowacce nutsattsiyar 'ya mace.
Sai dai hayakin da aka sa ta shaka a kandemi da za'a sace ta ya janyo mata severe allergy dinta ya tashi na sinuses sannan mura ta kamata da zazzafan zazzabi.
Gefe daya yunwar da ta sha na awayoyin da babu abinci chronic ulcer dinta ta tashi... Sannan daddauretan da akayi ya sanya mata samuwar muscles spasm.
Ta sha karin ruwa sosai na kwarin jiki dana antibiotics saboda infection na rashin tsaftar wajen da aka sanyata. Sai na abinci da ba zata iyaci ba. Gefe daya kuma allurori ta sha. Sannan aka sallame su bayan awowi da tulin magunguna dazata shassha da na shafawa a jiki.
Suka rankaya gaba daya suka nufi kandem estate bayan Bappah Nuraddeen ya kira yace a tanadar da abinci gasunan tare da Amaal..
**KANDEM ESTATE**
Masu gadi suka bude tangamemen babban gate din motocin suka shige ciki. Sashen Hajiya Maryam sika dunguma sika yi baki dayan su..
Amaal ta wartsake don da kafafin ta ma ta taka tun daga asibitin ta shiga mota haka da suka dawo kandemi ma sashen Hajiya Maryam. Sai dai kallo daya za kai mata ka dauka ta shekara a kwance ba lafiya ne. Saboda yadda ta tame lokaci daya. Fuskar ta tayi fayau. Manyan idanun ta suka sake fitowa furfutowa waje tubarkallah..
Abinci aka zuzzuba aka ajiye mata a gaban ta. Hayateey dinta na gefen ta ta sa Amaal din ta fara ci tana korawa da ruwa. Kadan ta ci saboda ba yunwa ajikinta sosai sakamakon karin ruwan da aka yiyyi mata.
Bappah maheer ya sanarwa su Alhaji Muhammd komai tun daga kan titin da suka dauka zuwa inda amaal din take. Har sanda sika shiga kangon makarantar. da dai duk abunda ya faru.
Bappah Abdullahi dayayi recording komai da ya faru ya mikawa su hajia Maryam ipad din nasa suka gani. Da sauran mutanen da ke parlorn.
Haka dai akayi ta mayar da zancen. Suka zuzzuba abinci suka ci.. Kawu Adamu da yaran sa Suma aka mika musu yache bazai ci ba. Su kuma yan shaye shayen kamar zasu hadiye plates din suka cinye abincin tas.
Daga nan tambayoyi suka fara biyo baya... Daya daga cikin masu shaye shayen yace,
"Wallahi mu kudi kawai yake bamu ko fuskar sa bamu taba sani ba sai yau. Ya saya mana wayoyi tanan yake kira ya gaya maana abunda zamu aiwatar. Yace ga sakon da zamu turawa lambobi kaza na tsoratarwa ko mu sauya murya mu kira wasu daga ciki. Komai dai shi yake shiryawa."
"Kuma ko da yasa aka kawo wannan bebyn🤣 wasu matane suka kawo ta su uku.... Ya kirawo mu a waya yache zamu ji shi ya sanya mana kudaden aikin mu. Da ke gasiya baya wasa da kudin aiki nan da nan ya sallame mu. Yana kuma saya mana eh yane muna korawa..." Ya karasa fada yana gwadawa da kwalbar shaye shaye
"Mata kuma.... ?" Bappah Usayn ya tambaye shi...
"Bappah...... Eh mata ne Bappah su suka kamani sika shigar da ni motar amman bangs fuskokin su ba saboda wani hayaki ne marar dadi ya kewaye wajen daga nan ban sake sanin inda kai na yake ba " Amaal ta fada muryarta a sanyaye..
"Saka cctv footage dinnan Nuraddeen."
Nan da nan bappah Nuraddeen ya saka suka fara ganun komai tiryan tiryan abun mamaki mata ma'aikatan cikin estate dinne Kawu Adamu yayi amfani da su.