← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 60

Sashe 39

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki gaya mata me Yusra? Kyale ta.. Aure fa zatayi ma an kusa. Ita da shi suna kaunar juna tuntuni bazan yi silar batawar bappah Junaid da aminin sa ba. Ba kuma zan sa a daura mata sure dani ba na dole"

"Lalle Hamma ba sonta kake sosai ba."

Kallon ta yayi yana girgiza kai yache,

"Fita mun a daki... Kuma kar ki kuskure naji maganar nan awani waje wallahi sai ranki ya baci ko da wajen su Bappah ne da Mami...."

"Shikenan... Sai da safe" ta fada a sanyaye ta fita daga dakin

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi ya ko koma kan gado ya zauna ya ciro wayar sa .. Yana shiga chat message dinta ya shigo...

"Hey... Na dawo"

"Barka da dawowa... Habibty! I think of you a thousand times a day. Believe me when I say your love is more than a world to me. .....Maryam! My heart recognized you as my wife the moment it heard you speak. Please tell me it was right and say yes...."

Amaal a nata bangaren tana zaune reply din Arc. N ya shigo wayar ta. Tayi murmushi ma kafin ya bude.. Tana karantawa tana murmushi tache da shi,

"I'm out of words.... I just wish I met you earlier.... Bazan iya cewa agidah ba zan aura Yaya Hisham ba... Nurayn"

"Maryaam! I know what I want out of life and it’s you. Nothing but you. please say you’ll marry me, beautiful girl. My heart can only love you, and my soul only recognizes your voice. Let me hold you close forever as my beautiful wife..."

Amaal da ke kwance ta saka hannu ta runtse idanun ta. Kalaman sa na mata yawo a magudanar jiki gashi bayason shirin sa yayi nasara akanta ta bijere alkawarin da tayi tache dashi,

"Mu dena maganar ma please .. Allah anbadani an kusa aure na. Thanks .. night night"

Yanada kwance akan gado sai birgina yake ya koma can ya juya can ya lula duniyar kauna... Ya samu kansa da kasa kyaleta duk da shi kansa yasan auren zatayi amman nutsuwar hakan taki samuwa agare shi.. Ya sake rubuta mata,

"Maryam soyayyar ki tazamo abu mai matukar muhimmanci a rayuwa ta kin zamanto wani bangare na jikina da idan bake rayuwata zata shiga mawuyacin hali, shigowarki a a rayuwata sun zamanta sanadiyar dawwamar murmushi a fuskata, Maryam so shine abu mafi tasirin warkar da kowane irin ciwo.ma kullum zuciyata kan samu nutsuwa idan ta tuna dake.. ina miki fatan alkhairi Ina kuma tabbatar miki da cewa kaunar ki daga Allah take a zuciya ta, rai na da kuma gangar jiki na baki daya... Ki huta lafiya♥️"

Yana karasa rubuta mata ya ajiye wayar ya mike kenan zai shiga bandaki wayar tasa ta fara kara ya dauka mahaifiyar sa ce,

"Al-mustapha tun dazu nasa yusra ta kirawo mun kai shiru ba kazo ba. Dan Allah zo sako zaka karbo mun agidan antyn ku. Ba direba a kusa. Yusra Kuma saboda idonta ba zaata iya driving ba"

"Okay Mami gani nan bari na dan watsa ruwa."

"Kai sauri to"

"Inshaa Allah."

Bandaki ya shiga bakinsa dauke da addua yayi wanka hadi da dauro alwala ya sauya kayan sa zuwa jallabiya ya faffesa turarukan ya zura wayar sa a aljihu ya fita....

Ko bayan data ajiye wayar bayan ta karanta sakon daya turo samun kanta tayi da juyar da kanta gefe..Hawaye suka shiga diga idanun ta. Tabbas itama tana kaunar Arc. N da suka hadu a manhajar Instagram..

Tun bata san neye so ba shi ne ya koya mata ya Kuma chusa mata kaunar sa a ranta. Duk kuwa da bata taba ganin sa ba.. Amman suna matukar son junan su. Gashi da maganar auren wani akanta.

Ta ja kasan leben ta tana taunawa... Ta daga Kai ta dubi gefe su Hindu kowacce tana harkar gabanta ba abunda ya dame su.Wani lottafi ta janyo ta shiga karantawa..

..
_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/20, 5:54 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 38_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

Haka dai rayuwar ta cigaba da garawa. Kamar yadda Alhaji Abubakhar yayi allawari kuma ya cika donma ya daga a alokacin da aka sache Amaal sai data wartsake gaba daya tukun sannan aka gama musu komai na tafiyar. Suka tafi makka

Amaal, Hajia maryam, Alhaji Muhamamd sai bappah Nuraddeen dayaje amadadin kujerar Kawu Adamu da a baya Alhaji abubakhar ya aminta.

Satin su biyu a saudiya, daya a Dubai suka waiwayo gidah bayan an dudduba jikin Alhaji Muhammad komai lafiya kalau...

Bayan sati biyu da dawowar su ne kuma sarki Junaid ya dawo da Hajiya hadiza da Hajiya Ruwaida dakunan su tare da jan kunnuwan su sosai. Shima sai da Hajiya maryam ta masa Jan ido tukun sanan ya ce su dawo dakunan su..

An kawo kudi da kayan lefen Amaal. Tsayawa bayyana adadin yawa da tsaruwar kayan ma bata lokaci ne. Domun kunsan wanene mahaifin Hisham da irin tarun dukiyar sa. Kuma dan sa ne daya jal a duniya basu da wasu yaran bayan shi. Don haka kayan da akayi masa ko karamar kasuwa aka bude sai haka..

Dangi sun taru sunata kallon kayan anata Allah ya sanya alkhairi. Don tuni har an fidda anko ma na wani royal blue lace... Aka sanya biki nan da sati bjyu masu zuwa.... Tuni aka kirawo madame yerwa me kamfanin turaren wutar yerwa incense and more ta fara gyaran ciki da wajen amarya.. da hada mata turaruwa masu matukar kyaawun gaske .

Anyi furnishing gidan amarya ciki da wajen sa. Dangi sunyi zumunci kwarai matuka wajen bada gudunmuwar su... Shagalin hidimar biki ce kawai tayi ragowa..

:;::::::

Da saafe ya shirya ya tafi office .. Anan aminin sa yazo ya same shi suna hira.

"Dan Allah wai bikin amaal saura yan kwanaki ko?"

"Uhm...aina kaji?"

'ka manta student dina ce? Naga bata zuwa ne na tanbayi kawayenta da suke tare sukace an kusa bikinta ne. Lalle an kasa mu"

Al-mustapha ya tabe baki ... Paper ce agaban sa ya rike biro yanata zana shirme..

"An kasa ka kam tabbas"

"Ni da kai dai... Garanbawul..!!!"

Al-mustapha ya daga kai da sauri ya dube shi,

Habibi Talba yayi murmushi yana jan kasan leben sa yace

"A jerin matan da nake so bata ciki...Ai idan nace maka Ina son waccen yarinyar to ka kirani da garanbawul....
Wanda zai yi reno don kwa reno zaka yi... Yarinya ce fa danya sharaf. Yo waccen idan nace ina sonta ma ai sai reni ya shiga tsakanin mu .. batada qualities din da nake so ajikin mace gaba daya.... Ko abu daya bata dakko
na."

"Meya haka? Wa kake magana akai ne... Ni kanwata ce kawai nothing more" Al-mustapha ya fada ganin habibi Talba na neman kure shi..

Habibi ya sake duban Al-mustapha yace,

"Yarinyar da tun muna high school kake yawo da hotunan ta kala kala kana cemun kanwar ka ce.... Kai long story short.. Maza meyasa kayiwa kanka babbar illa haka? Kana kaunar ta amman ka bari wani yayi maka shigar sauri kana forming hard guy. Banza garanbawul.."

"Tashi ka futa mun a office"

"Naqi na fita"

Mikewa yayi shi ya harhada abubuwan sa ya mike zai bar masa office din habibi dake zaune har Al-mustapha ya kai bakin kofa yace,

"Matsoraci wanda ba zai iya fuskantar macen da yake kauna ba tun tana zanin gayo..Yace yana son ta.. Allah wadaran naka ya kasance sullutu..To Allah ya baka wata tagari,, Me sadaukar wa wani soyayyar da yake wa wacce yake kulafucin so"

Yana gama fada ya mike ya dafa kafadar Al-mustapha ya fuce daga ofishin......

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Chapter 39 · 0% Book details