← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 60

Sashe 45

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko yan uwan ta su Hindu dake takalar ta da fada tuni ta dena shiga shirgin su ta baiwa bola ajiyar su. Ta tataro kayanta ma ta bar musu sashen su kadai suke dabdalar su tana wajen mahaifiyar ta a zaune

Gashi duk bayan kwana biyu sai anyi mata gyaran jiki... Tamkar wadda zataje gasar sarauniyar kyau..

*ARDO KANDEMI INT. AIRPORT NUKAA*

Karfe sha bjyu na rana jirgin su ya sauka a filin sauka da tashi na farfajiyar filin iyapot na Ardo kandemi dake birnin Nukaa.

Aaayan ne yaje daukar sa tun wajen sha daya yake jiran sa a mota... Suna sauka kuwa yana fitowa ya hango motar Aayan din ya nufi motar da sauri dauke da akwatin sa.

Aayan din ya futo yana dashare masa hakora,

"Ango.... Ga ango... Ango ..."

"Dan wahala kawai. Dalla dena kira na da wani ango. "

"Yo karya akayi maka? Wallahi an daura maka aure"

Al-mustapha ya tabe baki ya saka hannuwan sa ya dafa kan mota yana duban Aaayan yace,

"Labiba ce ko? Yarinyae nan ko mayya ce sai haka wallahi"

Aaayan ya tuntsire da daria. Al-mustapha ya zabga masa harara ya bude gaban mota ya shoga bayan ya zura akwatin sa a baya. Aayan ma ya shjga ya tashi motar yanata daria. Al-mustapha ya dube shi cike da takaici yace,

"Wai aka tsallake ka ba'ayi hadin auren nan da kai ba. Wallahi baa kyauta ba"

Aaayan ya dube shi yana grigiza kai yace,

"Wallahi baa kyauta mun ba. Narantse da Allah ban so zan sake wani azumin a kandemi estate ba. Agidah na nake so naci girkin matata. Mu rangwaje soyayya nake gaya maka. Amma wai aka ki ayimin auren nan such is life"

Al-mustapha ya dube shi ya tabe baki hadi da sakin tsaki yace,

"Kai fa ka dauka auren abunda ya kunsa komai kenan? "

"Abunda yake damuna kenan ni .. komai yabiyo baya"

"Ina tanbayar ka labiba ce ko?"

"To kai azaton ka wa za a baka Hindu?"

"Hindu? Amma Allah ya isa"

Aaayan tsabar daria sai da ya nemi gefen titi yayi parking ya shiga dariya harda rike ciki sosai yace,

"Hindun bata isa bane ko bata kai ba?"

"Dan wahala. Kai a aura maka ita mana"

Aaayan yayi murmushi yace

"Hindu kan akwai kaya ba lefi zan iya maneji yasin"

Al-mustapha ya sake jan wani tsakin yace,

"Kai fa gaba daya banza ne. Kai kssai structure din mace shine agaban ka?"

"To meye auren?"

"Uban ka ne."

"Dan wahala na labiba"

Al-mustapha ya dube shi yaja tsaki yace

"Duk Ina direbobin gidan ne za a turo ka dauke ni?"

"Yo da ka samu ma nazo na dauke ka. An gaya maka yanzu kanada sauran muhummanci ne a idon mu? Kai din daka tattara komai naka ka bar kasaar ba tare da masaniyar kowa ba. Dan wahala yasin da sede kayi bolt koka hau dan sahu ya dawo da kai gidah. "

Al-mustapha ya sake duban sa yaja dogon tsaki yana grigiza Kai yace,

"Dalla rufemun baki..."

"Kaga hotunan bikin kuwa?"

"Naga na Amaal da mijin ta"

"Perfect couples nake gaya maka...duk Nigeria ba wadan da suka dace da juna irin su.."

"Dan Allah kayi shiru. "

"Yo sai nayi shiru naki fadan gaskia? Baka ga na yusra ba da .......

"Wace yusran?"

"Yusra dai Fatima"

"Auren tayi itama.. Bangane ba meya faru ne haka aurar da kowa akayi ne?"

Aaayan yayi dariya yana grigiza Kai yace,

"Kai,yusra, amaal ku kenan kadai"

"Waya auri yusra to? I can recall yusra batada saurayi tun ex dinta da suka bata baata sake saurayi ba fa wata aura?"

"Itama hada ta akayi da da wani"

"Kan balai.. auren meye haka aka yiyyi ne? Auren dole fa kenan"

"Kusan haka. Amman dai ba wani dole dan ana cewa zaa hada ita a auren dana amaal atare ta amince dawanda aka bata caraf tace eh"

"Woah.. agaban kowa kenan akayi?"

"Kowa yana nan".

Al-mustapha ya sake zare idanu daya tuno batula me aikin su da mahaifiyar su ta mayar kamar yan gidan abu kadan tace tana tausaya mata Kuma itace zata aurar da ita inshaa Allah,

"Ko Batula aka aura nun please?"

Aayan ya sake fashewa da dariya yana girgiza kai yace,

"Watace daban fa. Kuma wallahi mekyau ce. Ni fa da har zance dan Allah aha dani da ita sai kuma nayi shiru kawai. Amma wallahi zaka ji dadin zamantowar ta matar ka yarinyar batada hayanjya ga nutsuwa."

Mtscew.. Al-mustapha yaja tsaki cike da takaicin maganar aaayan yace,

"Kai na cuwo yake. Danyi shiru please."

"Nayi shiru fa kace? Ni da baki na, motata ta, har zaka dinga yanka mun dokoki. Bazan ba"

Bai sake tanka shi ba. Ya sa hannu ya kwantar da kujerar da yake kai ya lumshe idanun sa,

"Ka zauna muyi magana mana"

Al-mustapha ya girgiza masa Kai alamun a'ah. Yaja pcao din kansa ma ya rufe fuskar sa da ita,

"Wato ga mahaukaci ko? Ka bawa banza ajiyata ba"

Kanzil Al-mustapha bai ce masa ba... Aayaan ya cjgaba da Jan motar sa kawai har suka karasa gidah.

*KaNdEm EsTaTe*

Aaayan ya shige da motar sa cikin gidan har farfajiyar parking space din sashen Hajiya Maryam.

Masu kula da sashen suka taso da sauri sunayi musu sannu da zuwa.

"Ranka ya dade Ina kayan?"

"Ai ba wasu kaya bane Alhasan...."

"Zan dauka a haka ranka ya dade"

Alhasan ya bude gidan baya ya curo akwati da hand luggage din Al-mustapha ya shigar masa da ita sashen Hajiya Maryam

Bakunan su dauke da sallama suka shiga ciki.. kan Al-mustapha a kasa cike da kunya ya karasa ciki ya zauna agefen hajiyan daga kasa

Suka gayshe su cikin girmamawa. Hajiyan da Alhaji Muhammmad da sauran bappanin su suka amsa fuskokin su a sake idan aka tsame bappah jalaludden aka ajiye a gefe.

Al-mustapha ya basu hakuri abisa tafiyar da yayi bai fada musu ba.

Hajia tasa aka kawo abinci aka jere. ya bubbude ya zuba kadan a plate ya fara ci,

"Har yanzuu danyaye baka son abinci dai?"

Murmushi kawai yayi yace

"Ina ci Hajiya"

"Ba wani baka ci, wannan abincin kamar Wanda zaa bawa husna?"

Yan parlorn suka saka dariya. Shima Al-mustapha murmushi kawai yayi.

Bayan ya karasa cin abincin ya shiga bandaki yayi awala ya fita masallacin cikin gidan yayi sallah sannan ya sake komawa sashen Hajiyan

Su Bappah Nuraddeen ne suka fara maganar auren da akayi masa. Kan ya rike wadda aka hadasu auren da daraja yayi biyayya sai Allah ya saka musu albarka. Kansa akasa yace,

"In shaa Allahu"

"Allah ya maka albarka kaji?"

"Aamin Bappah..."

"Akwai ginin da kake yi wanda ka zana mahaifin ka ya cigaba da karasa maka shi. Ya kumayi maka lefe an Kai gidan su matar ta ka. Kafin akarasaa ginin, Wannan sashen bayan na hajia da bakowa sai ku fara zama anan din. Can din kuma ya kusa kammalluwa sai ka dauki matar ka ku koma idan an karasa"

Ji yake tamkar ya bude baki ya zunduma ihu. Shikenan wai shi dinnan da yake a zaune a haka mijin aure ne? Au yanzu nan shidin yanada mata ? Allah me iko a a duk sanda ya so ..

"Ko bakaji ba?"

"Naji Bappah. In shaa Allah..." Bayan ya bawa bappah Nuraddeen amsa, ya amsa ya sake juyawa saitin mahaifin sa yace,

"Bappah nagode Allah yakara arziki ya saka da alkhairi "

"Aameen" kawai Bappah Jalaludden ya fada.

Dik suka mike suka firfita. Bai wani jima ba shima ya nufi sashen su ya gayshe da mahaifiyar sa. Ya Kuma bata hakuri a bisa laifin da yayi..

Aayan ya kira yusra ya sheda mata Al-mustapha ya dawo.. Nan da nan ta kira su hajiya Maryam tace dan Allah kar akai masa Amaal abari zatazo da kanta tukun sai ta tsokane shi.

Ta Kuma kira Hajiya jamila ta ce mata Al-mustapha ya dawo ta turo me gyaran jiki ta sake yiwa Amaal na kwana daya. Amaal kamar tayi kuka saboda gyaran jikin nan har ta gaji da shi. Saboda ko'ina na jikin ta yayi kyau ta kuma sake cikowa sosai komai ya zauna... gyara yayi gyara.

Har ga Allah bataji dadin dawowaar da akace yayi ba.... Al-mustapha yana zaune a sashen mahaifiyar tasa ya saka hannu ya sosa keyar sa yace,

"Ina bintu?"

"Wani abun kake bukata?"

Ya girgiza kai yana lankwasa hannuwa. Ta dube shi ta tabe baki tace,

"Fadi abunda yake ran ka"

"Mami ita aka aura mun ko?"

Ta dau ruwa kenan zata sha ta ajiye tana kallon sa tayi murmushi kawai kafin tace,

"Ba ita bace... Mijin da bintu zata aura ma jiya yazo zance ya shigo ya gayshe ni"

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tunowa da labiba kuma sai yace,

"Ko labiba ce Mami?"

Hajia Jidda ta mike tabar masa wajen tana cewa,

"Idan ka fita ka rufemun kofar parlorn kasa"

Ya sake sauke wata ajiyar zuciyar ya kwantar da kansa akan kujera kawai yana tunane tunane. Gashi kowanne tunanin yake sai Amaal ta shigo ciki. Yaja tsaki yana dukan goshin sa cikin takaici..

Dakyar ya mike ya nufi dakin sa ya kwanta bayan yayi sallar nafila. Yanata rokon Allah ya sanya albarka a rayuwar auren dole da akayi masa...Allah kuma ya sanya masa hakuri da dangana da zama da matar da aka aura masa...

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Chapter 45 · 0% Book details