← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 60

Sashe 19

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai aka cigaba da liyafa aka kare. Mutane suka fara watsewa … jirgi ya shiga jigilar mayar da nesa garuruwan su.

Wanda suke a gidah birnin nukaa kuma suka tattafi gidajen su. Yayinda wadanda suke a wasu kasashen suka tattafi airport.

KANDEM estate ta zama sai yan uwa da abokan arziki tsirari kawai.

Tunda suka fara hotuna har suka gama idanuwan sa akanta suke. Haka ta sake girma? Ya tanbayi zuciyar sa.

Kasa hak’uri yayi saboda BAKON yanayin da ya samu kansa aciki na so yayi mata magana.

Ai kuwa tana futa yabi bayanta da sauri yana kiran sunan ta,

“Amaal…”

Da sauri ta juya don ganin me kiran sunan nata. Hasken wutar kantarki ya haskaka ko'ina da gauraye…

Duk suka tsaya suna fuskantar juna. Gashi ya kafeta da idanu . Dakyar ta iya cewa,

.”Ina wuni? Yaya hisham.?”

“Lafiya kalau….. Kwana da yawa.”

Dan murmushi tayi kawai. Tana lankwasa hannuwan ta.

“Sai anjima” ta fada batare da ta sake cewa komai ba ta juya zata tafi,

Ya bu bayanta da sauri,

“Korata kike?”

“zanje na kwanta ne,. Akwai sch gobe.”

"Kina da waya?”

“Uhm… what about it?”

“Number ki zaki ban”

Tayi saurin girgiza kanta

,”Meyasa?”

"Saboda wayar karatu ce kawai bata amsa waya ba…An hana mu magana da maza"

“Ni ba yayan bane ba… ko kin manta?”

Ta kada kanta. Yayi murmushi ganin ya mata wayo ya sosa keyar sa yace,

“Ban number din to… zan zama online coach dinki, Duk abunda baki sani ba akan studies dinki don’t hesitate to ask me…”

“In shaa Allah”

“Fadi Ina jin ki…. Ga wayan dai”

Ya mika mata wayar tasa. Wallpaper din hotan sa ne agaban rigar tasa an saka hisham07

Ta shiga ta rubuta masa number ta mika masa. Yana karba tayi gaba da sauri har tana hadawa da gudu.

Shi dariya ma abun ya bashi… Ya kuma sake yabawa da nutsuwar ta sosai.

Ya girgiza kai kawai ya juya ya nufi sashen da aka sauke su…

::::::::::::::::::::::

Haka dai rayuwa ta cigaba da garawa.. Abubuwa na dad'i da akasin haka sun faffaru...

BAKON MUNAFIKI na cigaba da bibiyar zuriyar kandemi.

Gefe daya kuma su Amaal sun kammala makarantar secondary har sunyi jamb ma. Sun samu gurbin karatu a jami'ar.

ARDO K UNIVERSITY NUKAA (AUN)..

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[8/30, 2:21 PM] Hafsaat💞: _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 21_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

   *ARDO K UNIVERSITY NUKAA*
                (A U N)

   Tana zaune a kofar twin theater lecture hall dinsu da ke department din da take na architecture. Direba take jira yazo ya dauke ta don ta gama lectures dinta na ranar...

Shiru shiru lokaci yanata ja dai taga ya kamata ache yazo ya dauke ta. Don haka ta mike daga zaunen da take ta karkade rigar jikin ta samfarin doguwar riga kirar Egypt. Navy blue color data sha kawaatuwa da wasu duwatsu masu kyalkyali.

Ta yane kanta da mayafin rigar ba kadan ba tayi kyau .. gefen kafadar ta kuma jaka ce blue colo,r zip din ma a zuge yake sakamakon littafai da suka cika jakar da laptop. Ga handsout ta rike a hannun ta.

Ba kadan ba ta kara wani irin musulmin kyawu me tafiya da duk wanda ya daga idanun sa ya dora akan ta..

Ta sake zama cikakkiyar budurwa, kyawun ta ya dada karuwa. Jikin ta ya kara murmurewa da cika sosai.

Hakika dik wanda ya dora idanun sa akan ta ya janye sai ya kara dauka ya dora akanta a a karo na ba adadi saboda zatin halittar da Allah ya azurta ta da shi...

    Takawa ta farayi zata fita daga cikin department din zuwa waje.... Malamin su ya futo daga cikin ofishin sa yanata sauri da alama fita zai yi shima

Ta dan ja baya ta bashi dama ya shige. Har ya wuce sai kuma ya juya ya kalleta...

"Ina wuno?" Ta gayshe shi kanta a gefe.

Tsayawa yayi.. Ya dan saci kallon ta... Yadda take lankwasa yatsun hannun ta da suka sha jan lalle da zanen baki ya masa kyau kwarai matuka.

Shima matashin saurayin malami ne da yake ji da kyau da kuma kambun ilimi.. sanye yake cikin riga da wando yan kanti da suka sake bayyana kyawun sa na fulanin usul.

"Lafiya kalau..... A department din ecology kike?" Ya tanbayeta kai kache dagaske yake..sarai yasan a department dinsu take student dinsa ce amma ya samu kansa da zolayar ta,

"A'a..." Ta amsa shi kanta a kasa dai bata dago ba.

"Wane department?"

"Anan department din"

"Architecture ko linguistic da yake baya?"

"Architecture.."

"Oh really...level nawa?"

"Level one na ke.."

"Ahh fresher.... Jambito... Jolly just come jjc"

Ita dai Amaal murmushi kawai tayi. Wanda ya sake sanya shi sake ce mata,

"Amma ai kun gama lectures ko?"

"Eh."

"Karatu kike baki tafi gidah ba?"

"Ina jiran azo dauka na ne..."

"Okay Allah sarki.... Kingane ni ?"

Ta gane shi sarai. Amman ta grigiza kai alamun a'ah.. Yayi mamaki sosai yace,

"Ni din?"

"Eh.."

"Lalle bakya shiga lectures.."

"Ina shiga"

"Amma baki sanni ba a Malaman ku? Ni me daukar 1301.... "

"Oh okay"

Ya sake satar kallon ta. Wannan karon ta daga kanta tana kallon daya bangaren. Wai shi da students mata ke tururuwar son ganin sa da magana da shi har yan level 4 amman yau yar level one karamar yarinya yanata jan ta da hira amman tana sha masa kamshi

Ya samu kansa da jin haushin kansa. Duk da haka dai bai hakura ba ya sake ce mata,

"Care for a free ride?"

Tayi hanzarin girgiza masa kanta.. cikin sanyin murya tace,

"Nagode..... Za'a zo a dauke ni"

"Ya sunan ki?"

"Amaal...."

"Amaal..." Ya maimaita sunan yana jan sa.

Kada masa kai kawai tayi. Ta dan ketare ta gefen sa saboda yadda wayar ta tafara ringing ,

"An zo dauka na." Ta fada tayi gaba abunta

Juyawa yayi yana bin bayan ta da kallo. Wai yau abunda yake wa wadan su shi ake yiwa,

Don haka ya girgiza kai kawai yana murmushi yayi wajen shima. Yanata sauri zai je airport ya dakko babban aminin sa.

Mota ta bude ta shiga da sauri tana ajiyar zuciya. Gaba daya a tsorace take tunda malamin nasu ya tsaya yana mata magana har kawowar tafiyar sa.
Ta dan juya ta kalle shi ta mudubin baya alokacin dayayi reverse ya haye kan tigi.

"Ranki ya dade wanj abun kike so? " Direban ya tambayeta alokacin daya ga ta bawa mudubin baya nutsuwar ta baki daya tana kallo,

"Bakomai..." 

"Muje?"

"Eh.... Muje"

Kai tsaye direban ya dauki hanya daga department dinsu na architecture zuwa kandemi..

Yana kai wa gidah ta nufi sashen su ta ajiye kayan ta. Ta shiga bandaki tayi wanka jadi da dauro alwala.

Kayan ta ta sauya zuwa doguwar riga ta atamfa.. Bata daura dankwali ba sai ta yafe kanta da mayafin karami irin na abaya.

"Ke Dr. Habibi Talba ya fara muku lectures kuwa?" Hindu ta tanbayi Amaal datayai hanyar kofa zata fita,

"Habibi Talba?" Ta maimaita sunan tanason tunowa,

Kanta a sama dai tanata son ta tunano inda taji sunan ta kasa ,

"Eh... Wani gaye me tsawo"

"Gaskia ban gane shi ba"

"Ke banason wasa.

"ko wani ne daya mun magana yau..."

Hindu ta tuntsire da dariya daga karshe taja dogon tsaki

"Habibi ne ze miki magana? Whole habjbj Talba ..gurl stop lying. Ba shi bane gaskia. Shi mata ma basa gaban sa. Baya ma tsayawa yayi magana da mace ko malama ce balle ke level one student. Da yake daukar ku ku wajen dari... Har zai tsame ki ya miki magana ke kadai .."

"Inaga wani ne malaman da yawa.."

Da hannu Hindu ta alamae dataje. Ta koma ta mayar da kanta ta kan pillow tana waka.

Amaal ta fita daga bangaren nasu tayi na mahaifiyar ta.

Suna zaune ita da Hamid dake aiki a computer dake gaban sa...

Ta gayshe da su duka. Suka amsa suna sakar mata murmushi.

"Hirar me ake Hayateey?"

"Hirar farin ciki"

"Akan meye"

"Abbiey dinku ne yace yana son ya dora yayan ki akan wani aiki"

"Ma shaa Allah aikin me?"

"Bai fadw ba tukun "

"Allah sa muji alkhairi"

"Aamin"

"Bari naje na gayshe da Hajiya"

"To sai kin dawo"

Mikewa tayi yar wayat ta a hannun ta ta fita. Har tayi bangaren hajjya sai kuma ta fasa..

Sashen da aka kwantar da kakan nasu ta ta shiga

Shiru ba kowa sai karar sautin al- Quran ni ke tashi ahankali.

Tanata sallama.ba amsa ba. Duk azaton ta ma ko suna can cikin dakin marar lafiyar.
Chapter 19 · 0% Book details