← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 60

Sashe 24

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Drawer din jikin dressing mirror ta janyo ta zura ledar aciki, zuciyar ta na sak'a mata abubuwa da dama na yadda zatayi da kayan data dauke..

     Karasa shiga sukayi. Bappah Jalaludden ne agaba Al-mustapha na biye masa a baya. Sai Alhaji Nuraddeen daga baya... Aayaan kuma ya tsaya yana duba wayar sa bakin gate kafin ya mayar da its aljihu ya bi bayan su..

Da sallama Alhaji jalaludden ya bude kofar dakin da mahaifin nasu yake ciki,

Gyaran murya yayi daga cikin dakin..

"Waye. Ko kawu ne?" Alhaji jalaludden ya lekar da kansa ciki azaton sa Kawu Adamu ne ya amsa da gyaran muryar...

Yana karasa shiga ya tarar da mahaifin su a tsaye yana linke rigar jikin sa daya cire,

"Babaaa???" Bakin sa a bude cike da mamaki.

Su Alhaji Nuraddeen suma suka shiga dakin.. dukkanin su suka tsaya chan suna mamaki marar misaltuwa

"Babaa.."

"Kakaaaa."

"Kakaaaa"

Suka shiga kiran sunan sa... Kowanne da mamaki dabaibaye a fuskar su..

Aayaan ya karasa da sauri ya rungume kakan nasa..

"Alhamdulillah! Alhamdulillah..."

"Babaaa" Alhaji Nuraddeen ya fada hade da kamo kafadar mahaifin na sa ya zaunar da shi akan kujera ya durkusa agaban sa yana kallon sa cike da kulawa yace,

"Babaaa.."

Alhaji Muhammd ya daga masa kai yana murmushin shima

Jalaludden ya karasa da sauri shima ya zauna a kusa da mahaifin na su,

"Baabaa... Ka gane mu?"

Alhaji Muhammd ya daga kansa kawai yana murmushi

"Kakaa baka iya magana?" Al-mustapha ya tanbaye shi. Ya yinda Aayan ya koma kusa da su shima yana bin kakan na su da kallo

"Ina ga fa kaman baya magana..." Aayaan ya fada cikin tabbatarwa,

"Ku kira bappanin ku... Jalaludden dan kira su Kawu Adamu kai ma . A kiraa kowa dai."

"Tohm"

"Tohm Bappah"

Shi dai Alhaji Muhammd sai bin su yake da kallo kawai...

Sukaa kikkira wayar cikin kankakin lokaci kuwa sashen ya cika taf. Kowa ya hallara. Amaal ma ta karasa tana kallon kakan na su. Itama ita yake kallo

"Ko da yake ke ai kin gan shi ko fave...." Aayaan ya jeho mata tanbayar yana nuna kakan na su.

"A...a" Ta amsa a ararrabe tana raba idanu.

Alhaji Muhammad ya girgiza kai alamun bata gan shi ba...

Haka dai yan uwan gaba daya akaita murna da farin ciki samuwar warakar jikin na Alhaji Muhammad.

Aka sake gyarr sashen Hajiya Maryam akai fleeting na maganin sauro ko'ina na cikin gidan. Bayan ya futa aka bulala turarukan wutan yerwa incense and more.

Sai bayan ishai tukun sannan aka rankaya sashen gaba daya. Nan ma wano sabon zaman akai. Shi dai Alhaji Muhammad ba bakin magana sai dai idan wani ya fadi wani abun ya juya ya kalle shi maana yana ji, Amma baya iya mayarwa...

_-_-_-_-_-_-

Amaal na zaune a parlorn hajiya jamila sai ga shigowar mahaifan nata. Hayateey ce agaba sai abbiey din nasu a baya.. yasha jallabiya da hula fara irin ta larabawa dinnan.

Amaal ta zube a kasa ta gayshe da su gaba daya cikin girmamawa sika amsa.

"Amaal...." Ta jiyo mahaifin nata ya kira sunan ta

"Na'am Abbiey"

"Dazu naji Aayan na cewa ke kika fara ganin fardowar baba... Ina son sanin gaskiyar lamarin duk kuwa da kince a'ah..."

Katiwar ajiyar zuciya ta sauke... Kafin tache,

"Abbiey kayi hakuri... Nayi maka babban lefi. "

"Na yafe miki... Da wanda na sani da wanda bansani bada Wanda zaki aikata Nan gaba.."

Murmushi tayi. Wanda kyakkywarn hakoranta a jajjere sika bayyana tache,

"Yau ma dai wajen Hajiya zani sai na fasa nayi bangaren kakaa saboda motar dana gani irin ta rannan da wadannan doctors din biyu... "

"Ina sauraron ki."

"Tohm... Danaga sun ja motar sun tafi sai naje ba kowa dai kaman ko da yaushe. Ina shiga sai na ganshi a kwance.m Amma idanun sa bude. Na kira sunan sa dai baya magana.Kawai sai na bude drawer dinnan na dakko allurai da sirinjin dana gani duka na zuba a wata bakar leda dana gani a gefen gadon... "

"Tohm... Ina jin ki uwata"

Shiru tayi kanta a kasa tace,

"Na dakko ledar?"

"Je ki dako"

Mikewa tayi ta hau sama.. sarki junaid da Hajiya jamila suka kalli juna. Fuskokin su na tu'ajjabin labarin da amaal ke gaya musu...

Can sai ga ta sakko da leda a hannun ta ta ajiye agaban mahaifin nata,

"Ga su"

"To cigaba Ina Jin ki"

"Tohm bayan na saka a ledar ne naje kusa da shi saboda yadda naga idanun sa na yi nake tanbayar sa da ko ciwo suke sai ya rufee idanun ya bude. Ni Bangane ba. Sai da ga baya naga ya zaro harshen sa dakyar yana mai mun nuni da Karin ruwan da ke shjga jikin sa... Dubawar da zanyi sai naga ruwan da yake shiga Kalar sa Baki da wasu abubuwa acikin harda karare. Nayi sauri na zare na cure gaba daya... Na saka ledar na fito bakin gate sai ga bappah jalaludden da ballah Nuraddeen da Yaya Aayaan da Yaya Al-mustapha.. sai kawai na durkusa akan ledar na gayshe su bayan sun shige ne sai na taho nan. Amma bappah jalaludden da Yaya Al-mustapha ma bssu amsa gaysuwata ba.."

"Amma meyasa baa ki gaya mun ba eh?"

"Hayateey da nazo bakya nan ki tanbayi iya."

Sarki Junaid ya sauke katuwar zuciya. Ya saka hannu yana daddaga allurorin....

"Toh Alhamdulillah....Allah yasa karshen wahalar kenan. Allah kuma ya kara masa lafiya mai dorewa ya Kuma bude masa bakin sa da baya magana.."

"Allahumma Aameen"

"Kinyi kokari... Kin Kuma kyauta da kika ceto rayuwar sa da ga fadawa kogin halaka. Sai dai ko nan gaba idan zaki abu ki dinga bi ta kan manya.. Yanzu da kin samu abun ki awajen da ya kenan? Irin wannan abun ba masu irin shekarun ki ne keyi ba amaal... Kinyi matukar kokari da hazaka.. Allah kuma ya Kare ki da kariyar Sa. Ko da wasa kada ki bari wannan zancen ya futa kina ji ko kin gayawa wasu bayan mu?"

"A'ah abbiey"

"Toh kada ki kuskura ki bari wannan zancen ya futa waje... Daga ni sai ke sai mahaifiyar ki sai mahaliccin mu gaba daya"

"In shaa Allah Abbiey"

"Allah ya miki albarka.. Allah ya miki albarka... Allah ya miki alnatka"

"Aameen Abbiey"

Wayar sa ya janyo a aljihun da ke gaban rjgar sa ya shiga wata number ya rubuta message can ya dauki hotan kayan cikin ledar ya cigaba da danna wayar tasa.

"Ki saka a akwatin nan ki nannade da sealtape ki bawa isa direba zan aika shi inda zai Kai .. zaayi bincike akannsu da duk ma abubuwan da suka dache"

"Inshaa Allah Abbieyn su.. Allah ya bada Iko"

"Allahumma Aameen."

HajiyaJamila ta mike ta dauki ledar da kayan ciki tayi karamin parlor ta hau sama ta dakko duk abjbuwan da zata bukata ta shiga shirya kayan tana nade su...

Sai wajen 12 saura kwata amaal tayi musu sallatama ta tafi sashen su. Zuciyar ta na mata dadi. Ranta fes tana jin ta cikin madaukakin farin cikin samuwar lafiyar kakan su Alhaji Muhammad....

/////////////////////////////////////////////

Tanata sauri ta shirya cikin wata riga kirar Caribbean kalar ja,. Saman rigar a dan tsuke kasan ta kuma ya bude..

Ta yane kanta da mayafin rigar ja shima. Batayi wata kwalliya ba ta dai shafa hoda ta goga kwalli.

Ta dan goga red lipstick kadan a bakin ta.. Ba kadan ba tayi kyau kamar wata balarabiya..

Ta janyo wayar ta.....Ta shiga daukan selfies tanata murmushi. Ta gama ta mayar da wayar ta cikin jaka,

"Jikin ki sai rawa yake kamar mazari zaaje gun maza ko?" Hindu ta ce da ita tana tabe naki..

Murmushi amaal tayi tana zura takalman ta tache,

"Wai su Yaya Aayan? Su ke bi na bani ke bin su ba.... Sai kun taho"

Ta fuce da sauri tana duba wayar ta dake ringing... Tabar Hindu da cizan yatsa

Wajen Hayateey taje suka gaysa...Daga nan ta wuce bangaren Hajiya . Ba kowa a parlorn sai kakan su Alhaji Muhammadu yana zaune da carbi a hannun sa tayi sallama ta shiga ta zauna,

"Kakaa Ina kwanaa? " Ta gayshe shi duk kuwa da tasan ba bakin magana

Dan juyawa yayi ya kakkali parlorn. Itada dai Amaal na bin sa da ido

"Kaka wani abun kake so ne?"

"A'ah..... Maryam! Nagode Allah yayi miki albarka."

Ta bude baki zatai magana ya saka yatsan sa akan nasa bakin yana mata alamar da tayi shiru...

Ta rufe bakinta da tafukan hannauen ta tana daga Kai... Mamaki ya cikata gefe daya kuma tausayin sa ya mamayeta.

"Salamu alaikum" aaayan da Al-mustapha suka shigo ciki..

Amaal ta amsa musu sallamar. Yayin da alhaji Muhamamd ya daga musu Kai. Labban sa suka motsa amsawar.

Gayshe da shi sukayi dik kuwa da da Kai yake daga musu yana murmushi...

Aayyan ya shiga cikin kananan kaya samfarin polo wear. Yayin da Al-mustapha ya ke shirue shirye cikin manyan kaya riga da wando na yadi me laushi ya saka hula data karbi aokin jikin kayan

"Kinga yadda kikai kyauu favorite. Wow wow wow...Dama ga ki me kyau.." Aaayan ya juya wajen Amaal yana yaba kyan da tayi.

"Thank you... Favorite Yayaa ayaan"

"Ina Hajiya?"

"Nima bangan taba inaga tana ciki.",

Cikin haka sai ga hajiyan ta futo daga daki tana dogara yar sandar ta ta karaso ta zauna suka shiga gayshe ta tana amsa musu daya bayan daya da faraa a fuskar ta

"To bari mu je"

"To Allah ya dawo ku lafiya. Allah yabar zumunci "

"Aamin Hajiya... Fave muje ko, Babaa Kai ma tashi muje" aayan yace da Al-mustapha.

Duk suka fita wajen harabar gidan bayan sun musu sallama.. Nukaa hills and garden zasu je gaba dayan su yaran zuriyar gidan.

Luxurious bus ce katuwa tazo daukar su wasunsu har sun fara shiga ciki. Al-mustapha na daga gefe yana jujjuya mukullin hannun sa.

Amaal na wajen wata bishiya tana amsa kiran Hisham daya kirata bayan yaga hotanta da ta saka a status na WhatsApp. Sai murmushi take tana amsa wayar. Hannunta daya na kan reshen bishiyar tana wasa da ganyen jiki...

Ya samu kansa da binta da kallo tun daga tafun kafarta zuwa fuskar ta. Ba karamin kyau tayi masa ba ..

"Fave muje ko?" Aayan. Ya fada yana nuna mata motar
Chapter 24 · 0% Book details