← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 60

Sashe 59

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka Hadisai sun bayyana muhimmancin zumunci, kamar yadda Imam Bukhari da Muslim sun rawaito daga Sayyidina Jubairu dan Mud’im (R.A), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba...MUSULUNCI
‘Yan uwantaka da kaunar juna a musulunci babbar ni’ima ce mai tarin muhimmanci kuma wata babbar hanya ce wacce take kiyaye al’umma daga dukkan nau’oi na cutarwa da rarrabuwa, domin za mu ga cewa ta hanyar ne a kan samu hadin kai mai karfi, kuma a kan kasance tare har a yi aiki domin bunkasa addini da warware matsaloli da bukatun al’umma, wanda hakan zai kara taimakawa al’umma su samu yalwatar arziki, dankon-zumunci da kyakkyawar alaka da tarbiyya, kuma su nisanta daga dukkan kaidin makiya na ciki da na waje. Kamar dai yadda za mu iya ganin haka a cikin nassosi na Qur’ani da hadisan Ma’asumai (as).... Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Allah ya karfafa mana zumuntar mu, ya kara hade kawunan ahalin marigayi Bappah Ardo kandemi gaba daya cikin lumana da kaunar juna da kuma kwanciyar hankula da wadatar zuciya Amin..."

Bayan ta karasa, sauran bappanin kowannen su ya shiga karin haske akan abubuwan da Hajiya ta fadaa. Akaci aka sha har hotuna akayi kamar wani biki. Baki daya kawunan su sun hade babu wata sauran baraaka.

Aka saka shagalin bukukuwan nan da sati biyu masu zuwa.. Akayi bukukuwan na gani na fada a dangi da kasa baki daya... Angwaye da Amare kowanne ya tare a muhallinsa...

Bayan bikin da sati bjyu Al-mustapha da Amaal ma suka tare a sabon gidan su kasancewar an gama ginin gidan yayi kyau sosai, ginin zamani na 3d sama da kasa komai yaji dukiya tayi ta'adi agidan.. suka cigaba da zaman su cikin lumana da kaunar junan su gwanin ban sha'awa....

Tana zaune a sashen Hajiya... Tun da driver ya dakkota a school ta wuce kandem estate wajen Hajiya Maryam anan ta sake yin wanka, taci abinci, ta kwanta a dakin Hajiya abunta har da yin bacci ..

Wayar tace ta fara kara ta dauka da sauri ta kara a kunnenta,

"Ki shirya nazo na dauke ki ..."

"Babes yau daya dai ka bar ni na kwana mana anan please, har na kwanta fa a dakin Hajiya"

"Kinsan dai sarai bazan iya bacci ba idan banji dumin jikin ki ha ko? Gani nan zan karaso mu tafi"

"Ni! Ni! Ni...gaskia anan zan kwana.."

Al-mustapha ya gigice ya kashe wayar ya kara gudun da yake a mota ya nufi kandem estate. Tun a mota ya kira Hajiya Maryam bayan sun gaysa yace da ita,

"Bana samun Amaal a waya, Hajiya kice ta karasa shiryawa gani nan na zo daukar ta"

"To dan yaye, Amma har ta kwanta ma fa, Amma bari a taso ta"

Ko kadan baiji kunya ba, ya murje idanun sa da kasa yace

"To Hajiya a gaya matan nagode"..

Murmushi hajiyan tayi data ajiye wayar tasa safiya mai aiki taje ta taso Amaal din. Amaal ta zura hijabin ta tanata kunkuni ta fita parlorn,

"Hajiya dan Allah kice masa yabar ni nayi bacci"

"Banason rigimar dan yaye takwara, Yace yazo daukar taki ma fa, daure ku tafi kinji Allah ya miki albarka"

Don ma kar ya shiga hajiyan tace ya kyale Amaal din. Sai yayi zaman sa amota bayan ya kira Amaal yace ta futo su tafi. Amaal tayiwa Hajiya sallama ta fita

Ya bude mata motar ta shiga ta zauna tanata muzurai. Ruwan daya taho dashi me sanyi ya mika mata yana kanne dariyar dake shirin fita

"Sha ki sanyaya zuciyar ki Maryam"

"Bana sha"

"Haba kyakkyawa ta.... Kiyi mun afuwa kinji...Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan ta’ba mantawa da su ba har abada a rayuwata.... Sha ruwan nan zuciyar ki ta samu saalama kinji tawaje na.?"

"Na koshi... "

Ya danyi kasa da kansa yana dariya daman yasan zasu kwashe haka. Don haka ya juya kan motar sa suka dauki hanyar gidan su dake wata unguwa ta daban ba dai nisa can sosai da kandem estate.

Suna zuwa ta wuce sama fuuu. Ta shige dakin ta . Bandaki ta shiga ta sake yin wanka ta zura kayan bacci tabi lafiyar gado ta kwanta taja bargo ta lullube kanta

Al-mustapha ma dakinsa ya shige yayi wanka ya sake kayan bacci ya nufi dakin nata dauke da wata 🌹 flower a hannun sa.. ya shiga bakinsa dauke da sallama Amaal dake cikin bargo ta amsa masa.

Ya sadaada ya shige cikin bargon jikin sa har yana rawa,

"Maaaryam"

"Ya akai?"

"Dan Allah dan girman Allah dan ALLAH tashi muyi magana"

Sunan Allah da yaketa hadata dashi yasa ta tashi zaune tana kallon gefe,

"Ni me lefi ne awajen ki, Dan Allah kiyafe mun. Allah bazan iya kwana bake a kusa dani ba shiyasa... Kinji?"

"Naji"

"Ki yafemun, Dan Allah... Ga flower din ban hakuri ta soyayya kinji? Rose flower ce "

"Madalla.. ka gama?"

"Kin yafemun?"

"Uhm"

"To kiyi dariya"

"Banajin yi"

"Ba kyajin yin dariyar?"

"Uhm"

"Tohm kwanta habibty"

Kwanciya tayi ta dakko pillow ta jera a tsakanin su. Al-mustapha yayi dariya yana kallon ta. Ta kwanta tana juya masa baya hade da kashe futilun side lamp.

Sai da yabari ta kwanta zata fara bacci ya sadaada jikin ta ya rungumeta, duk yadda tayi ta kwace ya hanata ya kashe mata jiki gaba daya, da zafafan sumbar da yake bawa duk wani sashe na jikin ta. A dole ta hakura ta saki jikinta suka gwangwaje daren ranar da soyayyar su...

_____

BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA:

Haka rayuwar ta cigaba da garawa kwanakin mu nata karewa... Lalle rayuwar dan Adam ba a bakin komai take ba.. An samu karuwa a zuriyar ardo kandemi an kuma samu tarin rashe rashen rayuka na daga cikin wasu yan uwan ..

Allah ya azurta Fatima Yusra da haihuwar ya mace ta biyu bayan wadda ta haifa shekaru biyu da suka wuce. Tubarkallah kyakkyawa tamkar Hisham yayi kaki ya tofar saboda tsananin kamar su... Sannan su hamid da Hindu da su Aayan da sauran su yawanci duk matayen su sun hayayyafa. Amaal ce dai bata taba ko da bari ba.

Lamarin rashin haihuwar nan ya fara damun Amaal tun a karancin shekarun ta. Wasu daga cikin dangi magulmata na ta tsegumun kar dai ta dakko irin rashin haihuwar mahaifiyar ta, Ranar Amaal har hawaye ta zubar saboda tsananin bacin rai.

Bayan har asibiti sunje har a turai an sheda musu babu wata matsala. Dukkanin su su biyun suna cikin koshin lafiya Allah ne kawai bai kawo haihuwar kan su ba.

Al-mustapha shi sam bai damu ba. Amma Amaal ta damu sosai kasancewar ta mace mai rauni.

Tana zaune agaban mudubi tana shafa kulaccam din kamfanin yerwa incense and more.. Al-mustapha ya shiga dakin. Har ya shiga yana sallama bata sani ba. Tatafi tunani kanta akan madubi yayin da hawaye daya bayan daya ke yar tsere a fuskar ta.

Ya karasa kusada ita ya tsugunna. Ya kamo hannayenta ya hade su waje daya dana sa,

"Maryaam"

Ta daga kai da sauri jin ya kirata, Sam batasan yazo wajen ba. Ta kakaro murmushi tana goge hawayen ta da sauri,

"Kuka kike?"

"A'a fa, wani abu ne fa ya fadamun idanun"

"Okay muje acire"

Ya dauke ta chak ya dorata akan gado yayi mata rumfa da jikinsa, yana busar mata idanun hade da sumbatar kowanne yace,

"Maryaamu tah, there is no one else in this world that I would rather spend the rest of my life with than you. You are my everything, my whole entire world. I love you beyond words..." Ya karasa fada yana balle botiran gaban rigar baccin ta.

"Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin ciki na, ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsarki... Maryam kice wani abu" Ya sakar mata rantsattsiyar sunba a bayan kunnenta yana jan fatar kunnen ahankali..

"Uhm..." Ta kasa cewa komai duk wasu kofofin jikinta na maraba da abubuwan da Al-mustapha keyi mata sai jan kasan lebenta take tana taunewa,

"Ke nake so nake kuma kauna... Damuwa bata mu bace maryaam. Komai mukaddari ne daga Allah kinji? Haihuwa, arziki, aure kai komai da komai ma sai Allah yayi maryaam... Nana Aisha matar manzo SAW har ta koma ga mahaliccin ta bata taba haihuwa ba .... Shin Maryaam kin kuwa lura da cewa ina neman na zama zautacce a cikin soyayyar ki? Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan iya fita ba.Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki. Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta....Every time I see your face, I cannot help but feel so blessed that you have graced me with your love. You are my dream come true, and I will always cherish you forever..."

Ya karasa fada yana fatali da yar rigar baccin tata. Yaja duvet ya rufe su yana sumbatar ko'ina na jikin ta. Sai suratai yake mata yana sake gaya mata kalamai masu ratsa jiki..

"Sometimes it feels like I’m having a dream, but then I realise it’s all real. I’m one lucky woman in this beautiful world. Thank you for being mine!.. Yaya Al-mustapha na..."

Al-mustapha ya daga kai ya dubeta yana murmushi yace,

"Karki sake cemun wani Yaya. Ni ba yayan ki bane gamu a gado daya kwance, A tube muna sharholiyar mu zaki kira ni da Yaya?"

Dariya ce ta kufcewa Amaal, Ya daga kai yana bata light kiss yace,

"Ai gaskiya ne wifey... Kar ki sake mun haka kinji gimbiya?"

"Tohm yareemah na...."

Hade bakin su yayi waje daya ya shiga nuna mata tsantsar kauna itama ta biye masa suka shiga raya sunnah...

Bayan sati bjyu maryaam Amaal ta tashi da wani irin zazzabi tayi ta amai. Ta sha anti malaria bata dai na ba, Al-mustapha ya kwasheta suka nufi asibiti gwajin farko likita yace Amaal din na dauke da juna biyu kimanin satittika.

Al-mustapha ya dubi gabas ya yi sujjada yana godewa Allah. Hakama Amaal data fara hawaye sharrr kaman ruwan famfo.
Chapter 59 · 0% Book details