← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 60

Sashe 46

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/25, 6:47 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 43_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

*WASHE--GARI*

*Yusra* da kanta ta kira Al-mustapha tace za'ayowa amarya rakiya yaje yasiyo dukkanin abun bukata. Bai amsa taba ya kashe wayar saboda tsabar takaici...

Yana fita parking space yaci karo da Aaayan zai shiga mota. Yayi sauri ya bude gidan gaba ya zauna

Aayan ya dube shi yana kallon sa shakeke yace,

"Malam meye haka?"

"Yi hakuri.. me da me ake kai wa amarya ne?"

Aaayan ya tuntsire da dariya ya dube shi yace,

"Ni magidanci ne?"

"Be serious please.."

"Kaji, drinks, snacks, fruits, da sauran su"

"Muje ka raka ni please"

Aayan ya tabe baki yaja motar suka fita daga gidan. Suka biya tukubar kaji suka siyo gasassu sannan suka siyo sauran abubuwan da zasu saya suka koma gidah lokacin dama an idar da sallar ishai...

Aaayan da Al-mustapha na zaune a sashen Al-mustapha da aka bashi da amaryar sa kafin a karasa nasa gini. Muryoyin su suka daki kofofin kunnen sa.

Kamar ya tashi ya gudu yake jin sa shi wallahi bai shiryawa auren nan ba. Aaayan ya daga murya ya amsa musu. Al-mustapha ma ya amsa kasa kasa.

Yusra ce ta fara shigowa suka gaysa. Sai kuma Amaal da Hisham daga baya. Al-mustapha ya dube su da mamaki ko meye abun zuwa wajen sa oho.

Hisham ya bashi hannu suka gaysa. Amaal ma ta gayshe su . Aaayan ne kawai ya amsa. Al-mustapha ya kalli gefe saboda ya kasa furta komai bakinsa ya masa nauyi. Shi akwai so yake su tashi su futar masa daga gidan....

"Hamma ango ka sha kamshi."

"Amarya yusra... Ina angon na ki?"

"Wait aunty amarya bata karaso ba? Ashe mu uan zumudi mumu kayo gaba.",

Al-mustapha ya tabe baki yace,

"Labiba ce ko?"

Yusra ta tuntsire da dariya tace,

"Ba zakaji mutuwar sarki a baki na ba"

"Koma wacece she's welcome to hell.... Kuma ana kwana biyu zan kara aure. Kingan ta?"

Ya karasa fada yana nuna mata hotan fuskar wata a wayar sa. A Instagram fa ya ganta yaje wucewa ta reels. Yusra ta kanne dariyar datazo mata tace,

"Kowa ya san bakada budurwa"

"A Manchester muka hadu",

Amaal ta danne bacin ran daya taso mata. Wato yana ma da wadfa zai karo nan gaba kenan... Allah ya temaka ba son juna suke ba. ...

Aayan ya mike yana shafo kasan keyar sa yace,

"Na tafi daki ba ni za'ai oppressing ba, Wato ni da banda aure. Amare da angwaye Allah ya bada zaman lafiya"

"Ka ballo ruwa hamma" yusra ta fada tana dariya

Al-mustapha ya yamutsa fuska yace,

"Nagode... Sai da safen ku"

"Korar mu kake?" Hisham ya fada yana dariya.

"Kusan haka" Al-mustapha ya bashi amsa yana yamutsa fuska. Saboda haushi Hisham yake bashi na aure masa Amaal da yayi.

Duk suka mike suka fita har Amaal din. Kamar yadda yusra ta tsara. Al-mustapha yaja tsaki bayan futar sa. Yasaka hannu ya dafe kansa.. ganin Amaal dinnan da yayi ya taso masa da radadin ciwon .

Sake buga kofar parlorn akayi. Ya tashi dakyar ya mike.... Yusra ce ta sake shigowa tana janye da hannun Amaal..

"Meye haka? Dan Allah ku fita"

Yusra tayi murmushi tace,

"Ka dena korar mu hamma ai dole zamu tafi ... Amma kafin sannan ga amanar amaryar ka nan mun bar maka.. ka sani Allah yayi Amaal itace matar ka. Ni kuma Yaya Hisham shine ya zamo miji agare ni." Tana karasa fada ta janyo hannun Al-mustapha ta hada dana amaal ta rufe kofar da sauri ta fuce..

Al-mustapha ya bude baki. Yama rasa abunda zai yi. Aamaal ta funcike hannun ta ta koma kan kujera ta zauna..

Jikin sa ya fara masa rawa... Ya karasa kusa da ita ya tsugunna cikin rawar baki yace,

"Amaal!!! Kece matata dagaske?"

"Bakar kaddara ta ba" Amaal ta amsa shi tana goge hawayen da ya fara zuba daga fuskar ta.

Neman gabas yayi yayi sujjaada ya daga hannu yana godewa Allah..

Hawaye na zuba daga idanun sa yace,

"Ki dena cewa bakar kaddara. Wallahi wallahi duk duniya ke nake kauna"

Ta dube shi ta yamutsa fuska tace, Cikin kwaikwayon yadda yayi maganar a lokacin tace,

"Yauwa karki dauka nima ko itin Aayan ne me rawar jiki akan ki... Ko a kafa aka dauramun ke sai na kunche..You're not my type, not even close... gwara ki sani don renin na ki yayi yawa... Ko mata sun kare ni Al-mustapha ba zan taba iya soyayya da ke ba.... Baki da abunda nake so a mace ke baki ma cika macen ba. Yanzu kike tasowa. Kina eani ji da kan ki..."

Bude baki yayi jin kalaman sa data fada tiryan tiryan... tabbas shi yayi su lokacin a jami'ar su daya je wajen abokin sa Habibi Talba. Dama bata manta ba? Shi fa guguwar so ce ta rufe masa ido Hisham na kiranta kishi ya turnukeshi ya fadi hada,

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...." Ya fada yana dafe kansa

Mikewa tayi da sauri zata bar wajen ya riko ta. Mayafin jikin ya zame ya fadi a kasa. Doguwar riga ce ajikin ta ta atamfa data sha dinki.. gaban rigar a dan bude yake ana ganin kirjin ta kadan..

Kitson ta kanana jelar su ta zubo ta gadon bayan ta. Ga wani kamshi dake tashi daga jikin nata. Ji yake kamar ya suma don dadi.

Hannun sa na rawa ya kamo hannun ta ya saka a setin zuciyar sa.

"Wallahi Ina kaunar ki, kaunar ma da'daddiya ce.. I've fallen for you... I fell in love with you"

"Another one of your lie's.... "

"Yaa SubhanAllahi... Maryam ki yarda da ni believe my words..."

"Impossible... Har abada"

Wasu zafafan hawaye ne dake bayyana adadin kaunar da yake mata suka fara zubo masa yace,

"Ya Salam! Hear me out Maryam... Bansan meye so ba sai akan ki...."

Yaja hanunta ahankali ya sake kai saitin zuciyar sa, dake bugawa tamkar zata fado don zillo...

"Saurari bugun zuciya ta kiji.... Maryam wallahi Ina kaunar ki fiye da yadda kalamai zasu bayyana"

Ta dan daga kai ta dube shi ta janye da sauri. Ya rankwafa yana duban idanun ta ta janye kallon ta daga gare shi...

Ta bude baki zatayi magana Al-mustapha ya samu kansa da saka dan yatsa akan labbanta,

"Maryam please ..... Nasan bakya kaunata. Amma da sannu zan bayyana miki adadin irin kaunar da nake miki... Zaki amince"

Murmushi tayi irin na karena mun hankali dinnan,

"Cika mun hannu....

Bata karasa ba Al-mustapha ya samu kansa ta janyota jikin sa gaba daya.. wata kyakkyawar runguma ya mata tamkar zaa kwace masa itaa.. Yana shakar ni'imataccen kamshin scented hair spray din data fesa a kanta na kamfanin turarukan yerwa incense and more..

Samun kansa yayi da gangaro da fuskar sa kan labban ta dake kyalli... Ya sanya labbansa akan nata ahankali ya shiga bata runtsattsiyar sumba... Sweet and passionate mai bin magudanar jiki da tsoka. Duk yadda taso ta kwace kanta ta kasa.

Tana hawaye yana yi... Sakon sumbar da yake aika mata na kaunar da yake mata ne. Ita kuma wanda take amsa aganinta renin hankali ne kawai...

Ta janye bakin ta dakyar tana cewa,

"Dan Allah kyale ni..." Ta fashe da matsanancin kuka..

Ya saka hannuwan sa duka biyu ya tallaabo fuskar ta yache,

"Kaunar da nake miki babu algus wallahi...nasan ba zaki yadda ba saboda abubuwan da na aikata miki a baya amma ki yarda da ni wallahi kaunar ki ce sanadi.. Maryam I love you pass my mind beyond my soul" Bai bari ta ce komai ba ya sake tallabo fuskar ta ya bata wasu zafafan sumbar akan hancin ta da gefen wuyan ta da saman goshin ta. Da kan kirjin ta..

Wani karfi yazo mata tatattake ta ture shi.. ta zuba masa harara ta shige daki da sauri ta murza mukulli.....

Bandaki ta shige ta kunna famfo ta shiga durje bakin ta tana kuka sosai...

Shi kuma da sauri ya karasa bakin kofar yana cewa,

"Maryam please.... Ki yafemun dukkanin abubuwan da na miki a baya. Wallahi kaunar ki ce ta rufe mun idanu..."

Ya sake rankwafar da kan sa saitin kofar ya jinginar da shi... Ya saka hannun sa ya dafa kofar yana kwankwasa a hankali..

"Maryam...I belong to you... I belong to your love. Take me as I am and do to me as you wish. Let your love control my breath and make me yours only that I would go nowhere but stay and love you forever...."

"Kaje ma ka auri wadda kace zaka auro din.... Kamar yadda ka fada tabbas i am welcome to hell.. "

Hannun sa yasa ka ya dafe goshin sa..

"Maryaam... Fada fa kawai nayi. Ni wallahi bantaba wata budurwa ta daban ba. Na shiga Instagram ne fa na ganta nake tsokanar Yusra... Maryam da kaunar ki Allah ya halicce ni tun kina zanin goyo fa..Duk wata mace bata gaba na sai ke.... Maryam... Hear me out!!!!

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
Chapter 46 · 0% Book details