← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 60

Sashe 16

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin karya ne?"

"A'ah.."

"Okay muje an hada muku breakfast ai ke da yayan ki."

"Ah ya Hamid ya tashi ne?"

"Ya tashi ... Shi ya share kasa baki daya bayan da iya batai ba ya ki amincewa. Take gaya mun."

"Allah sarki Yaya."

Fita sukai daga parlorn suka nufi dinning area.

"Sannu da kokari iya."

"Sannun mu Hajiya."

"Hamid... Hamid... Ko ka koma baccin ne?" Cewar haj Jamila dake gyara zaman food flasks na abinci akan dinning

Da sauri ya jiyo maganar ta ya futo daga daki yana gyara zaman suit din jikin sa da botiran hannun rigar suit din jikin na sa.

"Har ka shirya?"

"Eh Hayateey"

"Tohm habiby zo ka ci abinci."

Murmushi suka sakarwa juna shi da amaal ya karasa ya zauna. Ta gayshe shi cikin girmamawa,

"Ya Hamid Ina kwana?"

"Alhamdulillah sissy.... Fatan kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah..."

"Ma shaa Allah.."

Haj Jamila tayi serving na su abincin. Itama ta zuba kadan tana ci

"Hayateey abbiey ya fita?"

"Bai tashi ba.." ta bata amsa.

"A gayshe shi tohm..."

"Yau zakuyi civic education test dinne?"

,"Eh"

"To Allah ya bada sa'a ya temaka."

"Aameen Hayateey."

"Hamid ya naga kana caccakunan abincin ne ko ba dadi? Ayi sauri a girka maka ko noodle ce?"

Da sauri ya girgiza kansa.

"A'a hayayeey.. da dadi sosai ma. Ciki na ne a cike ko dan na sha ruwa sosai ne."

"Ku temaka ku cinye komai dai please."

Hamid da amaal suka kall juna sukai murmishi

"Oh dariya ma kuke? To ki sani ko kun rage sai na sa shi a takeaay kun tafi da shi."

"Tuba muke Hayateey."

Dariya sika saki baki daya. A haka dai har sika karashe cinyewa. Haj Jamila ta mike ta shiga daki ta fito da kudi a kirge daya yafi daya yawa. Ta mikawa Hamid wanda yafi yawan

Ya saka hannun sa ya shafo keyar sa yana fadin,

"Na mehe wannan di Hayateey?"

"Rike dai... Hada da wannan ma" Hadi da dora masa da mukullin mota,

"Hayateey wannan fa?"

"Mukullin mota ta ne... Ka dinga zuwa aikin da ita kafin taka tazo in shaa Allah. "

Hawayen da yake ta rikewa ne suka shiga kwarara daga idanun sa.

"Nagode Allah ya saka da alkhairi... Allah ya biya ki da gidan aljanna. Allah ya jikan Umma ya m....

Bata jira ya karasa ba ta haye sama da sauri nata hawayen suna diga suma masu zafi.

Rukayya marigayiya kanwar su kawai ta shiga tunowa. Fuskar Hamid tamkar rukayya ce tayi kaki ta tofar

"Ya Hamid... "

Ya daga idanun sa da sukayi jawur ya dora akan ta.

Ta sakar masa murmushi hadi da mika masa tissue,

"Ka dena kuka .... Kaji?"

Karbar tissue din yayi yana mai goge hawayen nasa ya daga mata kai alamun toh.

Fita sukai wajen farfajiyar motocin sashen. Ya nufi wajen motar ya tsaya yana bin motar da kallo saboda tsananin kyawun ta, Kuma latest model ce.

Amaal ita dai sai murmushi take. Lokaci zuwa lokaci tana kallon agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta, jiran direban su kawai take..

"Shall we?"Hamid ya fada yana nuna mata motar

Ta girgiza kai tana masa murmushi,

"Akwai motan kai mu school..."

Wata zungureriyar mota ce mai matukar kyau ta Lincoln. Ta nufe su motar da ake kai su makaranta ce. Tayi mamakin da aka kawo motar har sashen Hayateey.

Aayaan ne ya futo daga mazaunin direba sanye cikin shadda fara riga da wando ba hula,

'ina kwana Yaya Aayaan.?"

"Lafjya kalau beautyn mu.... Muje ko?

Ya bawa Hamid hannu suka gaysa. Ya koma wajen motar .. Duk suna cikin kujerun baya Na'eelah da Najwa ne sai na tsakiya kuma Ikram da Ikhlas ne. Yayin da mazaunin gaba na kusa da direba ba kowa..

"Yaya Aayaan yau kai ne zaka kai mu?"

"Eh mai ku kai Hajiya ta aike shi .. "

Bude mata gidan gaba yayi sai kuma ya koma ya zauna a mazaunin sa.

Hamid yana tsaye yana bin su da kallo. Amaal ta karasa kusa da shi tana cewa,

"Ya Hamid mun tafi school... Allah yabada nasara"

"Wanene wannan din?"

"Yaya Aayaan ne.."

"Ba sunan sa nake tambaya ba alakar ku nake tambaya.."

"First cousin na ne... Dan gidan Bappah Nuruddeen yayan su Abbiey."

Horn Aayaan ya danna mata da karfi. Wanda yasa itada Hamid suka juya da sauri.

"Je ki.."

"Toh Yayaa sai ka dawo.,"

"Take care sissy... Allah uabara sa'a."

"Aamin"

Da sauri ta nufi motar ta shjga. Su najwa saura kadan su fashe. Saboda takaici. Dayaje daukar su ca yayi su shiga baya. Sun dauka ma abokin sa ne zai zauna a gaban kowani daban ashe amaal yayiwa tanadin wajen zama har da wani bude mata kofar mota..

"Mun gama beauty?" Ya tambayeta yana murza key

"Nagama..." ta bashi amsa tana murmushi..

"Seriously?" Ya sake tanbayar ta cikin muryar kulawa.

Ikram taja tsaki, Cike da takaicin da bata ma san ya fito ba. A kuma kufule tache,

"Muje mana... Haba!!!!"

"Me kika ce Ikram?" Ya tambaye ta yana yin baya da motar.

"Bakomai Yaa Aayaan.."

Kada kai kawai yayi... Suna tafiya yana jan Amaal da hira. Tana amsa shi da uhm da uhm uhm. Hankalin ta na kan note book da take karatun test da shi..

Ko da ya sauke su a makarantar bai tafi ba har sai ya ga shigewar su ciki. Idanun sa akan Amaal da kanta ke kan littafi tana karantawa.

Ya sauke gwauron numfashi bayan shigewar ta ciki. Ahankali yaja motar ya tafi...

----------

Kwanaki nata ja, Ranaku nata wucewa, Dare ya zama safiya .. Safiya ta yammaci, Yammaci ya zama dare.. Lalle Allah mamallakin kowa ne kuma da komai..

Abubuwa da dama sun faru a zuriyar ardo kandemi.... BAKON MUNAFIKI nata bibiyar ahalin gurin raba kawuna musanman bappah jalaludden da ke tsananin kiyayyar Amb junaidu.

Gefe daya iyalan Alhaji jalaludden dinne suka waiwayo gidah suma... Matar sa Dr. Jidda da kuma 'yar su macen Fateemah suna cewa da ita, Yusrah!!

__
_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[8/25, 10:32 PM] Hafsaat💞: _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 18_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

*KANDEM ESTATE*

  *Gaba* daya a zazzaune suke a babban dakin taron da ke cikin estate din. Kallo daya zaka yi musu ka tabbatar su din yan uwa ne kuma na jini.

Babban dakin taron ya kawaatu fiye da yadda alkalami zai rubuta... Komai samfurin royal ne kalar kasa...

Kowanne daga cikin su gaban sa dauke yake da tray an cika shi da kayan alaatu. Sai ruwa da lemo da kuma kofin tangaran an saka tissue paper a cikin sa...

Su Bappah Usayn da tagwan sa Bappah Hassan.... A zazzaune akan kujerun... Ya yin da su Amb Junaid ke daga kasan su.

Su din Bappannin mahaifin su ne ... Dattijawan kwarai matuka kowanne daga cikin su ya manyan ta.

Hakika sune masu fada aji a cikin zuriyar Ardo kandemi. Saboda ta kowane tsatso aka fito sune tushen sa. Don haka duk hukuncin da suka zartar haka ake dauka.

Bappah Hassan ya sauke gorar ruwan da ya kafa a bakin sa bayan ya sha,

"Alhamdulillah......." Yayi hamdala yana mai sauke ajiyar zuciya.

Ya daga kai ya dube su dukan su kowanen su jira kawai yake yaji maudu'in da su Bappahn suka zo da shi.

"Nurudden..."

"Na'am Bappah."

"Jalaludden.."

"Na'am..."

"Abdullahi...."

"Bappah..."

"Indo..."

"Allah ya kara maka lafiya Bappah.."

"Fateemah"

"Na'am Bappah"

"Junaidu..."

"Bappah....Barkan ku da rana.."

Bappah Hassan yayi murmushi bayan duk ya kira sunayen su daya bayan daya yace,

"To na kira register kowa ya hallara ba wanda yayi fashi.." Ya juya yana fuskantar su Bappah Usayn.

Baki daya suka saka dariya... Da ke da ma shi Bappah Hassan ya na da darakanci sosai. Shi yasa zai yi wuya bai je taro ya saka mutane dariya ba.

Bappah Imrana yayi gyaran murya yayi sallama hadi da sanya musu albarka duka.. Suka amsa cike da girmamawa,

"Kowa ni daga cikin ku yasan abunda yasa muka hada wannan taron?"

"A'a Bappah" Suka hada bakunan su wajen amsa shi.

"Toh Ma'shaa Allahu... Maganar da zamu fada ko ince hukuncin da muka yanke alkhairi ne ga ku da mu dama sauran duk wani ahali na Ardo kandemi..."

"Mashaa Allahu."

"Allah ya kara mu ku lafiya Amin."

Suka shiga amsa shi... Kowanne da abunda zuciyar sa ke saka masa. Musanman Kawu jalaludden da ke rike da wayar sa yana jujjuya taa...

Bappah imrana ya cigaba da cewa,
Chapter 16 · 0% Book details