← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 60

Sashe 55

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki dau auren mu a matsayin kaddarar da Allah ya rubuta akan mu gaba daya sai ta same mu. Maryaam inshaa Allahu ba zaki dana sanin aurena ba I assure you inshaa Allah.. kada ki manta da kaunar ki na tashi acikin rai na tun kina zanin goyo...Maryam na mallaki hankalin kai na gaba daya na gane rai na ya kamu da zazzafar son kasancewa da ke a matsayin wadda nake so muyi rayuwa ta har abada atare... Ina nufin rayuwar aure... Mukazo daga karshe Allah ya amince mana muka zama a inuwar ma'aurata... Maryaam me zanyi ki kaunace ni? Maryaam mai zance miki ki amince da kaunata? Maryaam fadi duk abunda kikeso idan har befi karfi na ba ni zanyi miki kawai don na samu ki sassauta kiyayyar da kike mun... Wallahi tallahi billahi babu macen da nake kauna a duniya bayan mahaifiyata da kanwata sai ke... Dik duniya idan kika ajiye su agefe babu macen da nake son kasancewa da ita har karshen rayuwata irin ki Maryaam.. wallahi idanu na ko kallon wasu matan su burge su basayi. Ba ma na jin kaunar wata mace a duniya sama da ke.... Maryaam ko kinsan kaunar da nake miki ce tayi sanadin samuwar depression dina a baya.? Yes ciwon damuwa kusan duka bappanin mu sun sani ma....."

Amaal tayi shiru tana sauraron sa... Tabbas ranar nan taji Bappah Abdullahi lokacin da suka zauna a parlorn hajiya baki daya sanda ana maganar auren su. Taji yana cewa Al-mustapha ba shine marar lafiyar nan ba?

"Maryaam..." Ta jiyo muryar sa ya sake kiran ta...

"Na'am..."

"Ina miki kauna tacacciya marar gauraye. Ina miki son so, Ina miki kaunar kauna... Ina kaunar ki da rai na, zuciyata da jikina gaba daya.. Maryam son ki ya mamayemun gangar jiki da ruhi gaba daya I'm not even joking. Maryaam..."

"Na'am

"I love you way too much... Maryam wata iriyar kauna nake miki..." Ya kamo hannunta ya saka akan saitin zuciyar sa ya cigaba da cewa,..

"Saurari yadda zuciyata take bugu Maryaam... Bugun adadin kaunar da nake miki ne matyaam. Zuciyata a duk inda nake inde aka kamo sunan ki saita sauya salon bugawar ta... Maryaam hear me out.. Dan Allah Dan Allah dan girman Allah ki karbi kokon barata ki kaunace ni .. ki nunamun kauna... Kaunar da nake miki ta Kai bazan iya bijerewa abunda kike kaunata ba ko menene shi. Maryaam idan ranki yafu kaunar ki rabu dani wallahi na amince zan sawwake miki din.... Maryaam me kike so.. zaki karbi soyayyata ki kin amince na rabu da ke?" Ya yago paper da sauri ya rike biro.

Take idanuwan sa suka fara zubar da ambaliyar hawaye... Kuka ya shiga yi sosai harda shessheka.. ya bude motar ya futa ya koma bangaren datake ya tsugunna da gwiwiyon sa akasa.

Ya rike paper da biro yana dubanta muryar sa da jikin sa suna rawa sosai yace,

"Wallahi kaunar da nake miki bazan iya tauye miki hakki ba.. maryaam bazan iya miki tilashe ba. Maryaam raina da zuciyata sun raja'ane da zazzafar kaunar ki. Ki dauki option daya. Ni Al-mustapha nayi alkawarin cika miki burin ki ko menene shi..." Ya karasa fada yana zubar da hawaye. Hannun sa sai rawa yake ya rike biro.

Maryaam idajuwanta suka ciko da ruwa fal. Gaba daya mamakine yasa ta kasa magana. Gege daya da tsoro mai tattare da fargaba. Ita kanta ta kasa gane irin kaunar da Al-mustapha ke mata.... Lamarin har tsoro yake bata yadda yake nuna mata kauna kamar zararre

"Maryaam kiyi magana please..... Kaunar ki ce sanadi.. and I promised you ... Na tabbatar miki bazan taba fadawa su Hajiya ai kece me son rabuwa da ni ba. Zan dorawa kai na lefi inshaa Allahu dede da kwayar zarra ba wanda zaiga lefin ki Maryaam... Kinji?"

Kuka tafashe da shi. Kalaaman sa sun mata nauyin data kasa jurewa. Cikin lallashi ya rungumeta shima yana hawayen,

"Ko mun rabu bazan taba ganin lefin ki ba Maryaam... Zan rubuta miki takarda yanzu inshaa Allah" Yana neman zare jikin sa tayi saurin rarumo shi ta kara manne shi da jikin ta tace,

"Karka sake ni....",

Ya daga da sauri yana dubanta. Murmushi ya fadada akan fuskar sa yace,

"Kin amince? Zaki dena tsanata maryaam?"

Ta share hawayen ta tana jan hancin ta tace,

"Ban tsane ka ba dama yaya Al-mustapha... Na amince "

Dadi kashe Al-mustapha ya bude gaban motar sosai ya nannade hannuwa ya dauketa charan cas ya shige cike da ita cikin gida ya ajiyeta har daki akan gado.

Ya koma mota jikinsa nata rawa ya kwaso komai ya Kai kitchen ya ajiye kowanne inda ya kamata. Ya rufe kofar sashen na su ya shiga dakin da sauri bakinsa har kunne....

"Bari nayi sauri nayi wanka don kara tabbatarwa shin da gaske kunnuwana da idanuwana sika jiye da ganemun abunda Maryamu ta ke fada? An bani dama nayi wankan? Ranki ya dade?"

Amaal ta gyada masa kai tana murmushi... Ya wuce dakinsa da sauri ya shige bandaki ya fyallo wanka ya jima agaban mudubi yana shafe shafen turaruka masu dadin kamshi. Ya taje kansa ya fesa turaren baki me kamshin vanilla ya fita yana mai yaba kyawun da shi kansa yayisa kansa.

Kofar dakin ta ya nufa ya kwankwasa . Amaal ta jiyo ana kwankwasawa tace,

"Waye?"

"Ni ne.... Gimbiya! An bani izini na shigo?"

Tayi murmushi tana daga Inda take a kwance tace,

"Ka shigo"

"Godiya nake Maryamu tahh..."

Shiga yayi bakinsa dauke da sallama,

"Assalamu Alaikum wa rahamatu Allah..."

Ta amsa shi tana dan kauda kanta gefe cike da kunya.... Ya karasa ya haye kan gadon shima ya sadaada ya kwanta a kusa da ita ya zura hannun sa ya kamo kafadar ta yayi mata pillow da kirjin sa..

"Ki cire hijabin mana... Yi hakuri"

Tunowa tayi da vest ce kawai da underwear a jikin ta ta grigiza Kai da sauri ..

"Yi hakuri bar abun ki maryamtu Tah ... Yadda kikace ai haka za'ayi.. kinci abinci?"

"Eh..."

"Ga cookies can da su kaza na sayo miki suna kitchen"

"Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya kara budi mai albarka Amin"

Da sauri ya juyo da fuskar ta yana dubanta,

"Amin... A'ina kika koyo wannan adduar haka? I'm impressed"

"Awajen Hayateey..."

"Mashaa Allah! Shi yasa akeso ka auri yar gidan mutinci da sanin yakamata. Gidan tarbiyya da dattako. Maryaam komai kin hada nayi dace sosai. Allah nagode maka. Alhamdulillah" ya daga hannu yana addua.

Ita abun ma dariya ya bata.. gefe daya bacci datake ji. Ya sake gyara mata kwanciya yana shafa bayan ta yace,

"Bacci kike ji ne?"

"Eh...."

"Meye ake boye munne ta cikin hijabin?" Ya karasa fada yana zura hannunsa ta kasan hijabin ta

Ta damke hijabin tamau tana raba idanu. Murmushi yayi alokacin daya gano dalilin kin curewar hijabin nata..

Jira take ya cire hannun nasa amman yaki daga cewa zai ga meyasa sai ya zarce da taba nan taba can. Tamkar zata shide saboda yadda yake mata tafiyar tsutsa da hannun nasa cike da kwarewa da son nuna kauna ga abunda ake nunawa kaunar...

"Bac... Bacci nake ji" ta fada masa tana janye hannun sa daga cikin rigar ta

"Tohm Maryaam.... Na dena yi baccin ki kawai rage zafi zanyi dai.. amman bayaga haka ba abunda zan sake yi. Karkisa tsoro aran ki",

Ta gyara kwanciyar ta saboda baccin da take ji yacu karfin ta. Nan da nan kuwa bacci ya dauke ta. Al-mustapha kuwa tamkar ya samu baby doll yayi nan da ita yayi can da ita Yanata neman magana daga karshe shima yayi baccin bayan ya tashi yaje parlor ya hada tea ya sha... Bai ci abinci ba don bayada cin abinci shi sai hajiyan tayita takura masa wani lokacin sai idan yunwa ce ta tasoshi sosai agaba tukun sannan yake nema da kansa...

***********

Haka zaman na su ya kasance... Al-mustapha na cigaba da nunawa Amaal zallar kaunar da yake mata. Sannu ahankali kuma tana sakin jiki da shi sosai ba kamar da ba.

Sai dai fa daya fara kokarin suje su kwanta zata fara kuka tana rokon sa ya yi hakuri don tsoro da fargabar daren farkon su ya da'daa mata a zuciya.

Sai dai Al-mustapha ya dan rage zafi da Yan wasu abubuwan na jikinta har ya samu nutsuwa. Gashi yana matukar bata tausayi sam kuma baya mata dole. yadda take so din haka yake biye mata... Ta sake tabbatarwa da lalle yana kaunar ta sosai...

Rannan ya dawo daga office kamar ko da yaushe ta tare shi tayi masa sannu da zuwa ta kawo masa abinci ta tara masa ruwan wanka yayi komai.

Lokacin bacci nayi ya fita kan zai sayo maganin mura dana zazzabi. Bayan ya futa ya dawo kansa na masa ciwo.. Amaal duk ta rude ta rasa inda zata saka kansa. Tanata bashi kulawa harda hawaye.

Ganin hakan yasanya Al-mustapha sake marairaicewa kan magashiyan fa bashi da lafiya sosai a dole, kwanan sa biyu yaki zuwa ko kofar gidah.

"Ina ne kuma yake maka ciwon yanzu?" Ta tambaye shi da damuwa shimfide a fuskar ta..

"Kai na da kafafu na..." Ya sake langabewa..

Amaal duk ta gigice tace,

"Sannu Allah ya baka lafiya mai dorewa ko su Hajiya zaa gayawa ne dan Allah ?"

Ya kamo hannunta da sauri ya dora akan kirjinsa yana runtse idanu yace,

"Zan warware ba sai an kira kowa ba. Idan ma sika zo zasuce depression dina ne meye dalilin daya jawo damuwar... Kingane?"

Amaal ta daga Kai da sauri tana raba idanu... Ashe kenan tashin ciwon nasa lefin ta ne..?

"Sannu.."

"Yauwa..."

"Me kake so yanzu?"

"I want you Maryaam..... Please" Ya fada yana sauke numfashi ...

Shiru tayi.. gabanta ya tsananta bugawa. Ya saka hannun sa akan saitin zuciyar ta yana jin yadda yake bugawa da sauri..

Ya sake kankameta yana shafa kanta,
Chapter 55 · 0% Book details