← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 60

Sashe 40

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/21, 7:19 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 39_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

Al-mustapha ya jima a tsaye bayan da Habibi Talba ya fice ya barshi a tsaye... Mamaki yake Ashe habibin bai manta kalaman da yayi katobara ya faada ba akan inde yace yana son amaal to a kira shi da garanbawul wanda zaiyi reno tunda yarinya ce danya sharaf...

Ashe kuma kallon sullutu yake masa ya gano Amaal itace yarinyar da yake musu maganar ta tun suna high school..
Hannun sa ya sa ya dafe goshin sa yana dana sanin katobarar zancen da yayi musu a baya... Duk kuwa da cewa yake kanwar sa ce. Ko aina Habibi Talba ya gano da shegen binciken sa..?

Komawa yayi ya zauna akan kujerar sa ya bude wayar sa ya shiga WhatsApp yana kallon statuses... Saboda bayasan komawa gidah ma don ya tabbatar yan uwan sun sake cike gidan. Don tuni wasu daga garurwa har sun fara zuwa. Wanda ke awaje ma sunata tahowa..

Kasancewar wannan ne biki na farko da sarki Junaid zaiyi zai aurar da 'yar sa. Yar autar sa kuma autar gidan wadda Allah ya amince zata kere yayyunta ta fara yi.

Wani short clip ne ya shigo ta family group dinsu dake WhatsApp din. Tamkar bazai shiga ba saboda ta saman notification ya hango. Sai Kuma ya bude ya shiga group din yayi downloading bidiyon. Ashe katin daurin auren bikin amaal ne da Hisham..

Ya samu kansa ta tallabe haba da hannun sa daya.. dayan kuma ya dan rage sautin bidiyon da ke tashin wakar maheer zain ta aure. 'BarakAllah..."

"A madadin zuriyar Ardo kandemi... Mai martaba sarkin Nukaa, Amb. Junaidu Muhammad Mahmud Kandemi da na Dr. Abubakhar Mai dingishin kudi..Suna farin cikin gayyatar ku zuwa daurin auren 'ya'yan su...Maryam (Amaal)Junaid Muhamamd da angon ta Captain Hisham Abubakhar... Wanda zaa daura inshaa Allahu bayan sallar jumuah a masallacin masarautar kandemi.. Akwai shiryayyiyar walima bayan daurin aure. Wanda ba zai samu halarta ba dan Allah yayi addua.."

Bayan ya gama kalla.. daga kasa kuma an sake turo wasu bidiyoyin ya bude na biyu yana karantawa da ke rubuce da,

Together with their families[Maryaam-Amaaal] and [Captain. Hishaam] invite you to share in the joy and celebration of their wedding day. On Friday after jumu’ah prayer.. Venue: Kandemi central mosque.. grand reception follows immediately ....

Siririn tsaki ya sauke...Ya zura wayar a aljihun sa mikewa yayi ya fuce daga office kan sa na ta masa zugi da radadi

"Sir ka tafi kenan?" Sadya sectary dinsa ta tanbaye shi

"Na tafi... Sai da safe"
Kai ya saka ya fuce ya shige mota. Ko da ya shiga ya zauna kasa tashin motar yayi ya tafi

Ya kifa kansa akan sitiyari hannunsa dika akan satiyarin fuskar sa a kasa. Ji yake tamkar kirjin sa zai ballo kasa.

Ya zaro wayar sa ya shiga nan da nan ya cike e-ticket... Ya gama yanke hukunci a zuciyarsa tafiyar sa itace zata saka shi nutsuwa.

Ya murza key zai bar harabar ofishin nasa Habibi Talba ya bude gaban motar ya shiga. Abun ma ya bashi mamaki ya dube shi yace,

"Meye haka?"

"Lefi ne dan na shigo motar ka garanbawul?"

Al-mustapha yaja siririn tsaki yace da shi,

"Dan Allah karka karamun bacin rai akan wanda nake cikin sa.."

Habibi Talba ya kalle shi yace

"Musty fresh kenan.... Wannan abubuwan da kake idan baka sani ba sake illata kanka kake... Wallahi da ache na tabbatar Amaal itace yarinyar nan da kake dawainiya da kaunar ta a school kana gaya mana yadda kake sonta . Allah da tuni na samu manya na sanar musu dawowata da nayi. To Amma baka taba ce mana ai da aure a tsakanin ku ba nunawa kake kanwar kace ta jini"

"To ba kanwar ta bace ta jini?"

"Amma ai akwai aure a tsakanin ku... Saboda ita fa ka waiwayo Nigeria gaba daya... "

"Wai waye ya gaya maka?"

"Ya gaya mun kana son amaal? Ni makaho ne an gaya maka? Duk magangunan da kake ta fada kana baka son ta inata nazartar ka na gani kaunar ta kake fiye da kalamai. And again hotunan ta na wajen ka tun muna school plus sunan yazo mun na sake duba kamannin ma na tabbatar itace..."

Al-mustapha ya tabe baki...

"Sauka ni tafiya zanyi"

"Sai kayiwa wanda bashida mota gori. Sannan kuma ba inda zani muje gidan ku"

Al-mustapha ya dube shi ya zabga masa harara. Ya tashi motar suka bar ofishin sika dauki hanyar kandemi.

Habibi Talba sai zuba magana yake. Shi de Al-mustapha na kada kai kawai ko ya amsa masa da uhm ko uhm uhm..

Notification ne ya shigo ta wayar Al-mustapha da ke kusa da giyar motar a ajiye. Habibi Talba ya dan daga wayar ya dubu screen din.

'E-Visa notification ne' Har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalli Al-mustapha,

"E visa kuma? Wa zeyi tafiya?"

"Ni ne..."

"Kai Kuma? Ina zaka?"

"Ina ruwan ka?"

"Dan wahala kawai."

Al-mustapha ya tabe baki ya cigaba da tuki har suka karasa... Sun furfuto daga cikin motar sai ga yusra kanwar Al-mustapha da Amaal..

Tun daga nesa kake jiyo kamshin turaren gyaran jikin da akeyi mata.. Suna doso su kamshin ke dada mamaye ko'ina..wani irin sanyayyen musulmin kamshi mai dadi.

Gyaran jikin da ake mata ya karbe ta. Domin fatar nan tata ta sake haske tayi santsi da laushi.. Tamkar an sake kara mata kyau. Harta gashin girar ta sun sake cika da baki. Leben nan nata ta shafa man baki sai kyalli yake da laushi..

Sanye take cikin doguwar rigar hijab bubu..Ta yane kanta da mayafin daya shiiga da kalar sa ja da ratsin baki..

"Ina wunin ku?" Yusra ta gayshe su. Suka amsa...

Amaal ma ta dan sunkuya cike da ladabi tace,

"Barkan ku da yammaci..."

"Amaal... Amarya" Habibi Talba ya fada yana murmushi

"Malam" ta fada cike da kunya

"Allah ya sanya alkhairi. Yasa gidan zamanki ne"

"Aameen" Yusra ta amsa shi. Saboda amaal din jtada dai kanta a kasa tana lankwasa hannuwan ta cike da kunya...

Tunda suka zo wajen Al-mustapha ya kasa dauke kansa daga kallon amaal da yaketa yi tamkar zai mayar da ita cikin sa..

Tana dago Kai suka hada idanu ya bata rai ya bar wajen da sauri. Habibi Talba yabu bayan sa yana cewa da shi,

"Jirani mana garanbawul.. Kai fa dan wahala ne."

Sashen Hajiya Maryam ya nufa Habibi Talba na biye da shi a baya.. suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama.. sika gaysa da hajiyan.

"Wannan aboki ka ne?"

"Eh hajia kin manta shi ko?"

"Kaman dai nasan fuskar nan tabbas"

"Habibi Talba ne.. Tun Muna kanana muke tare. Mahaifin shi abokin su Bappah ne.. yanada sarautar Talban gabas na garin Yalwanje... "

"Haka .... Ma shaa Allahu. Ya mahaifan na ka kalau?"

"Alhamdulillah Hajiya".

"Safiya kawo musu abinci" Hajiya ta dan daga murya tana kiran me aikin ta

Nan da nan me aikin ta shiga kawo musu abincin da trays tana ajiyewa da ruwa da lemuka.

"Ku zuba kuci dan Allah"

"Tohm Hajiya. Allah ya saka da alkhairi "

"Aameen Aameen Habibi"

Cikin haka Aayaan ya shiga ya same su .. suka gaysa ya zauna ya debi abincin ya fara ci,

"Hajia wannan shine malamin su Amaal fa da hindu ke magana" aaayan ya fada yana sake zura lomar abinci a bakin sa..

"Au shine.... Allah sarki"

Habibi Talba yayi murmushi yace,

"Ni ne hajiya"

"An ka samu ni da kai" Aayaan ya fada yana dariya.

Shi dai Habibi Talba murmushi kawai yayi masa. Al-mustapha kuwa kanzil bai ce ba ya cigaba da cin abinci yana korawa da ruwa.

Sun dan jima bayan sun kammala cin abincin suna ta hira daga bisani Al-mustapha da Habibi Talba suka yiwa Hajiya sallama suka fita...

"Muje ka ajiye ni a site can nabar motar"

"Nagaji maza.."

"Haba mana"

"Muje"

Motar sika koma suka shiga.. Al-mustapha ya kai Habibi Talba har site..

"Dan Allah Ina zakaje? Yaushe zaka tafi? Kuma yaushe zaka dawo"

"Meye haka? Kaman wani wanda yaci bashin gidan rediyo?"

"Dagaske nake please"

"Manchester..... "

"England dai?"

"Yes..."

"Yaushe zaka tafi? "

"Soon inshaa Allah"

"Exact date nake son sani"

"Will let you know .."

"To yaushe zaka dawo?"

"Sai na huta"

"Sai kayi healing dai... "

"Whatever... "

"Later.. will holla you"

"Alright. ka gayda su mummy"

"In shaa Allah.",

Yaja motar sa ya koma gidah ransa duk babu dadi kwata kwata.. Kai tsaye ya shige daki bayan ya shiga bangaren su.

Ko da aka tambaye shi akace akawo masa abinci ma yace a'a yaci awajen hajia. Kwana yayi bayyi bacci ba yanata sake sake sai salllar nafila da yayi ya roki Allah yasanya hakan ya zamo shine alkhairi agare shi.

A daren ya hada kayan sa a akwati da hotunan Amaal gaba daya da niyyaar idan yabar kandemi sai ya samu waje ya kona su duka..

:::::::

Shirye shiryen biki aka fara yi. Kwanakin bikin suka karaso.. Da ke Amaal din batason taro hakan yasa ba wani events za'ai ba. Akwai gagarumun Grand kamu/ royal mother's eve dai daza ayi. Sai daurin aure da walima shikenan..

Ranar Thursday yammatan gidan cousins suka hada bridal tea party. Iya su kadai ne kawai da amarya Amaal da kawayen ta. ...

Tayi shiga cikin barbie gown pink color kaman wata princess. Ta nade kanta da mayafi shima pink. Sai takalman ta silver color. Ba kadan ba tayi kyau.
Chapter 40 · 0% Book details