← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 60

Sashe 27

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya zauna akan kujera ya buda laptop din dake gaban sa ya kunnata.. Nan da nan ya sassaka dukkanin abunda zai bukata take faifen bidiyon ya fara haskawa na kowanne kwanaki har ya zuwa ranar da amaal ta hadu da Bappah Nuraddeen awaje lokacin data jiyo ta Kuma gano likitocin suna yiwa Alhaji Muhamamd allura yana kuka me wahalarwa...

Da sanda taje ta curo ruwan jikin sa da allurorin nan gaba daya ta saka aleda ta futar da su.... Yana karasa kalla ya dartsane harshen sa yana ciza cike da takaici.

Ya saka hannu ya dafe kansa saboda tsananin bacin rai. Computer ya janyo ya saka kafar sa akai ya dinga takata kamar ita tayi masa lefin.ya farfasata awajen yayi 'daya daya da ita.

Ya dauki memory card din ya nannade a tissue ya shiga bandaki yajefa a masai yayi flushing ..

Dama jiokin sa ya bashi itace.... yaja tsaki yafu a kirga..wayar sa ya janyo ya rubuta sakon da zai rubuta ya mike yana cewa,

" Uba da 'ya ke hargitsa mun dik wasu lissafi...... Junaid sai kayi dana sanin waiwayowar ka kandemi...Na hane ka kaki hanuwa ko? Ka dawo har ka karbi karagar mulkin kandemi..... To ka sani ka kana gab da shiga cikin matsananciyar musiba mai wahalar fita... Mu zuba!!!!!"

Ficewa yayi daga sashen gaba daya ransa a matukar bache yana sake harzuka tamkar wani kasurgumin zaki.....

*ARDO' K UNIVERSITY NUKAA*
(A U N)

Isa direba ya zura hancin motar cikin jami'ar dataci sunan marigayi mai martaba sarkin Nukaa, Alhaji Ardo kandemi...

Jamii'a ce da ke sahun farko na jerin jam'iyoyi da ake ji da su a garin Nukaa dama najeriya gaba daya.. dalibai daga kasashe ne ke zuwa karkashin ta suyi karatu...

Su ikhram ya fara kai wa departments dinsu daga karshe ya dauki hanyar kai amaal nata department din inda zasuyi lectures

"Hajiya karama aina zan ajiye ki ne?" Isa direba ya tanbayi Hindu dake owners corner tana tauna chingam.

"Department din da zaka kai ta...." Ta bashi amsa tana nuni da amaal da yatsa..

"Toh ranki ya dade..."

Ya kai su har department din. Amaal ta sauka tana gyara zaman jilbab din dake jikin ta Kalar maroon color. Ba kadan ba tayi kyau.

Yayin da Hindu ke sanye cikin riga da skirt sun matse ta .. halittun jikin ta sun bayyana ta yafa yalolon mayafi Kalar kayan .. tayi dauri rabin gashin ta awaje . Fuskar nan tasha foundation kamar amaryar karya. Ta zuba janbaki ja daya kara haskaka ta. Gefe daya Kuma turare ne ke tashi daga jikin ta...

Amaal ta mike ta fara tafiya. Hindu ta kira ta da,

"Ke..."

Ja tayi ta tsaya... Don ta saba ji da haka take kiran ta. Hindun ta taka ta sameta tana cewa,

"Ina ne office dinsa?"

"Wa?"

"Saurayi na da kikace eh malamin ku ne"

"Wallahi bansani ba"

"Karya kike"

"Allah bansani ba... "

"To tsaya dai...." Ta fada tana janyo wayar ta a jaka

Amaal ta dubu agigon dake daure a wutsiyar hannun ta. Batasan tayi latti a lectures. Amma gudun masifa yasa ta ja ta tsaya

Kiran sa Hindu tayi a waya .. sai data kira sau uku kafin ya dauka,

"Na zo fa...."

"Kina department din?"

"Eh...."

"Okay bani minti uku... Na fita bakin gate ne taho da aboki na... Yanzu zamu dawo.. "

"Alright."

"Na tafi ne?"

"No tsaya yazo seki tafi ..."

Amaal saura kadan ta fashe da kuka har ga Allah batasan lecturer din ya rigata shiga don baya bari ashiga idan ya riga shiga.

Sai da aka debi kusan minti Sha bjyar kafin motocin biyu su danno Kai parking lodge din.

Motar Habibi Talba ce agaba sai tashi a baya... Amaal na ganin motar malamin nasu tache,

"Gashinan yazo.. Na je?"

Hindu ta daga Kai ta haska mata harara.. Ta shiga gyara mayafin ta tana mayar dashi gefe..

"Baby H?" Cewar Habib Talba daya fito daga motar yana takowa wajen su. Idanun sa akan Hindu.

"Na'am Habibi..... "

Amaal na ganin sun hadu ta sulalae zata tafi.... Ashe Habib Talba ya hango ta,

"Zo nan..."

Ta waiwayo tana nuna kanta

"Ni?"

"A'ah.... Ni"

Komawa tayi kanta a kasa tace,

"Ina kwana?"

"Lafiya...wait tare na ganku kunsan juna ne?" Ya nuna amaal yana tanbayar Hindu..

"Step sister din sisters dina ce...."

"Omo...." Habib Talba ya fada yana smirking face

Amaal ita ko ajikin ta fatan ta su kyaleta ta tafi .

"Lecture na sai nan da one hour so kafin nan bari muje can mu zauna ko... "

"Sure... Why not?"

"Okay... Yauwa kinga ga motar aboki na can ki bashi key din nan kice ya jirani a office idan nagama zan zo sai mu wuce.."

"Okay tohm." Amaal ta saka hannu ta karbi mukullin.

Kai tsaye ta nufi motar.. Sai kallon motar take kamar akwai ire iren su a agidah. Wata zuciyar ta bata amsa da

"Ai ba dan ku kadai aka kera ba..."

Motar ta nufa ta kwankwasa ..yana danna waya ... Batare daya daga Kai ya dubi me kwankwasawar ba azaton sa habibi abokin sa ne. Ya sauke mudubin kasa,

Ta zura hannu ta mika mukullin cikin zazzakar muryar ta tache,

" Gashi inji Malam Habibi... Zan nuna maka office dinsa wai ka jira shi idan ya gama zai zo ku tafi..",

Cikin daga kai da sauri domin muryar ta na shige da wadda ke sanya shi nutsuwa ya daga kai kenan ya sauke akan kyakkywar fuskar ta.....

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/9, 12:24 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 28_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

Kanta a gefe ganin bai karbi mukullin ba wulakanci ne ko bai ji bane ga lokacin lectures dinta na kurewa.. Hakan ya sa ta juyar da kanta tache,

"Ga shi inji Malam Habibi....w...,

Ta nemi labbanta da kasa furta sauran kalmomin da zasu karashe zancen...

Sai kache ba shine ya gama kalleta ba. Yadda ya hade fuskar sa ya fuzge mukullin kamar fadaa ita lamarin nasa ma sai ya fara bata tsoro kuma ganin kamar yaga wata dodo..

Bude murfin motar yayi... Ya koma ya rufe yana wani shan kamshi. Ita dai ganin yayi kamar be santa ba yasa ta juya tayi gaba ..

"Baki iya gaisuwa bane....?"

Ta jiyo muryar sa a bayan ta... Tana cigaba da tafiyar ba tare data jiyo ba tache,

"Ina kwana...?"

"Yana gidan ku ...."

Tabe baki tayi... Dama tasan salon ya gasa mata magana ne.. Har office din ta rakashi tache,

"Gashi...."

"Zo nan...."Ya kira ta ganin ta juya zata tafi,

"Dan Allah... Zan makara a lectures ne " ta fada tanata rau rau d idanu muryar ta a sanyaye a kuma shagwabe kasancewar haka take magana amman wani sai ya dauka yanga ce...

Ya samu kansa da son sake jin muryar tata... Yana wani muzurai yache,

"Wato kula maza kike ma ko?"

"What?"

"Oh yes.... Da kawar ki Habibi yake magana right?"

Takaicin tambayoyin sa tamkar ta daka tsalle ta sharara masa mari. Kasancewar shi din dogo ne sosai ya fita tsawo. Duk kuwa da ita dinma doguwa ce... amman ya kere ta a tsawp

"Tambayar ki nake.... Ko anan ma rashin kunyar zaki mun ne?"

"Kayi hakuri... Ni ba rashin kunya nake maka na... Sauri nake zan shiga lectures dan Allah..."

Har ya zura mukulli zai bude kofar office din sai kuma ya fasa... Yana takawa wajenta tana ja baya... Har ta kai karshen bango. Gabanta na tsananta bugawa tamkar zai fado. Gashi tayi masa kyau tamkar ya rungumeta da halal dinsa ce...

Ya saka hannu daya ya tokare ta.... Ta juyar da fuskar ta gefe... Kamshin turaren jikin sa na Tom-Ford ya gauraye ta baki daya..

Kasa kasa yace,

"Baki bani amsar tanbaya ta ba.... Kula maza kike ko?"

"Dan Allah ka k.....

Bata karasa ba wayar ta tafara ringing. Tayi haka zata dauka yayi sauri ya wafce ya matsa gefe ta bi shi tana rokan sa,

"Dan Allah ka bani wayata..."

"Yaya Hisham..... Waye Yaya Hisham? Kaf zuriyar Ardo kandemi bamu da Hisham... Ohh daya daga cikin samarin ki ne ko?"

"Yaya Hisham dan.... Dan aminin abbiey ne, Dan Allah kayi hakuri kaban wayata."

"Ai dole ki so na naki wayar ki saboda samarin ki kala kala.... Waya sani ma ko habibin ma saurayin ki ne"

"Ni malami na ne... Sannan ba wata kawata da ke kula shi. Wadda kake zaton ko kawata ce suke tare ba kowa bace fache Yaya Hindu.."

"Hindu?"

"Dan Allah kaban wayata..."

"Je ki lectures din ki dawo..."
Chapter 27 · 0% Book details