← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 60

Sashe 28

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah kayi hakuri ina amfani da ita a lectures wajen browsing. Dan Allah kaban wayata"

"So kike kawai na baki kiyi waya da beloved dinki Haysam"

"Hisham.."

"Oh harda gyarawa? wato na furta sunan saurayin ki ba dai dai ba ko?"

Langabar da kai tayi... Kanta a kasa tace,

"Ka bani wayata... Please"

"Magana zaki gaya mun?"

"Ni ban isa ba"

"Gashi nan karan kada miya dan abokin bappah ma kina ce masa yaya.ban cancanci ki kirani da yayan ba sai wani ka ban waya ta.... Ko dan kinga kin fara girma? Kina shiga cikin yammata? Ko kin dauka nima Ina cikin admirers dinki kamar Aayan?"

"Kayi hakuri...." Ta shiga bashi hakuri don dik bata ga abunda yayi zafi dazai dinga ga samata maganganu ba..

"Yauwa karki dauka nima ko irin Aayan ne me rawar jiki akan ki... Ko a kafa aka dauran ke sai na kunche..You're not my type, not even close. ...... "
Kasa cewa komai tayi... Tsananin kiyayyar da yake mata yayi yawa.

"Yauwa gwara ki sani don renin na ki yayi yawa... Ko mata sun kare ni Al-mustapha ba zan taba iya soyayya da ke ba.... Baki da abunda nake so a mache ke baki ma cika macen ba. Yanzu kike tasowa. Kina Wani ji da kan ki...

Bai karasa ba still kiran Hisham ya sake shigowa.. cike da takaici ya cilla mata wayar ta dauka da sauri zata tafi ya daka mata tsawa,

"Ke..."

Tsayawa tayi. Amman zucjyar ta sai ta kasa hakuri. Hawayen data ke makalewa na cin nutincin daya ke ta mata ne suka fara zuba a kyakkywar fuskar ta.

"Dan Allah kayi hakuri .... Yaya Al-mustapha!! Zan shiga lectures." Tana karasa fada tayi gaba sam taki waiwayowa tana ji yana sake daka mata tsawa tayi banza da shi...

Yaci mata mutinci akan lefin data basan na meye ba... Ya tozarta ta akan hukuncin da shi kadai yasan kan sa.. Ya gasa mata maganganu akan fadan daya kirkire shi haka kawai ba tare dama sanjya ba...

Haka ta karasa Ardo kandemi auditorium (one thousand sitters) inda zasuyi lectures. tana tafe tana tsiyayyayar da ruwan hawaye...

Agaban auditorium din taci karo da kawayenta su biyu a tsaye da sauran yan ajin... Suna ganin ta suka tako wajen ta

"Ke meye haka....kukan me kike?" Hafsat kawarta ta tanbaye ta

"Ai shine... Babes meya faru? Ko menstrual cramps kike?" Cewar Zaarah dayar kawar ta su..

Bata amsa su ba ta dubi sauran mutanen wajen tace,

"Ya haka? Ina lectures din?"

"Ke mike jira dama... Wai baze samu zuwa ba ya bada handout aje ayi karatu zeyi open test next class din sa...."

"Alhamdulillah....." Ta sauke katuwar zuciya tana goge hawayen

"Wait..... Gurlll. Karki cemun akan lectures kike kuka?"

"Hakane ma.... Zaarah kin gano ta."

Murmushi tayi jin abunda suka fada. Maganar da Al-mustapha ya gaggaasa mata suka sake zuwa mata kai... Ta girgiza musu kai kawai tache,

"Ko daya....thou rasa lectures dinma ya dameni. Na dauka an shiga..."

"Zo nan ki wassafa mana labari... " Suka ja hannun ta suka koma wajen wasu kujeru suka zauna,

"Meya faru....?"

"Plss babes"

"Kun cika damuwa wallahi.... Allah ba komai.. Ba wani abu"

"To fada mana koma menene dai..."

"Ni da ...."

"Yaya Hisham...?"

"Bassam?"

Dariya sika bata yadda suka fara fado sunaye... Ta girgiza kai kawai.

"To waye please?"

"Ni da Yaya na ne...."

"Mts... Shine kika kuka? Ai dama wasu yayyun maza haka suke sai a slow.."

"Chill babes.... Komai mai wucewa ne... Bare fadan yan uwa baya karewa idan ba aure kayi ka bar musu gidan ba."

Dariya tayi kawai tana kada musu kai alamun tohmmm...

"Muje gashassh suya muci abinci kafin next lecture din ko?" Cewar Zaarah kawar su.

"Yauwa daman Ina craving tsiren kodar nan.." Hafsat ta fada tana rataya jakarta

Amaal ta mike tsaye suka nufi gashash suya and cafe dake cikin jami'ar ta su..

  __
        __

Tana tafiya ya saka hannun sa ya naushi bango cike da jin haushi kansa da kansa...

Ya akai wadannan maganganun sika fita daga bakin sa? Babu dadi abunda ya mata gaskia..

Gashi ba zai iya bin ta yaba ta hakuri ba... Ya nufi inda yaga tayi ta bache masa da gani da alama da sauri tabar wajen..

Jikin sa a sanyaye ya saka mukulli ya bude ofishin ya shiga.. Mema kwan ya zauna sai ya nemi bango ya jingina da shi ya daga kansa yana tunanin bakaken maganganun daya gasa mata...

Abunda zuciyar sa take son fada daban .... Wanda bakinsa da labban sa suka furta daban..

Ya saka hannu ya dafe kansa yana jujjuya shi...

"Goddamn it!!!..... Kayi shirme Al-mustapha... Kayi shirme"

Knocking office din akayi sai kuma ya turo kofar ya shiga.. bakin sa dauke da sallama...

"Ahh... Guy kana Ina ne?" Ya shiga dube dube..

Ya juya zai rufe kofar ya lura da Al-mustapha ya rakube a bangon bayan kofar kansa a sama ya lula duniyar tunani....

"Maza... Meye haka?" Ya tambaye shi yana girgiza kafadar sa..

Sai a sannan Al-mustapha ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi...

"Ka dawo?"

"Inata sallama ma na dauka baka man wallahi... Da niyar zan rufe kofar kuma sai na gano ka.. meya ke faruwa ne? "

"Bakomai... Kai na ne yake ciwo amma ya dena..."

Ya samu waje ya zauna... Shima Habibi ya zauna akan kujerar dake fuskantar wadda Al-mustapha yake akai...

"Ya kan yanzu?"

"Ya dena..."

"Yauwa ma shaa Allah... Kaga yarinyar data rakoka office dinnan?"

Al-mustapha ya muskuta ya gyara zaman sa yana kallon habubi Talba sosai,

"Yeah...what about her? Menene please.. eh?"

"Omo... chill! Kaga yadda ka gigice kuwa ..."

"Aboki na get to the point please.."

"Well.... Ni fa nayi mata... I want to wife her... Long story short ba wani kwana kwana maza so na ke na auri yarinyar nan ..."

Wayar sa dake hannun sa ce ta subuce ta fadi a kasa jin abunda Habibi Talba ke fada..

Habibi Talba da sauri ya dakko wayar yana kallon screen dinta,

"Kaci screen wallahi ta fashe... Meye haka?"

Al-mustapha ya karbi wayar ya jefata a aljihu yana duban Habibi Talba

"Kace me?"

"Malam wayar ka taci screen"

"Ba damuwa ai.... Amaal... Kasan Maryam Amaal ne?"

"Sunanta kenan?"

Wani dogon tsaki Al-mustapha yaja ya dankara masa lafiyayyar harara yace,

"Kaketa wannan dogon turancin da ko saninta bakai ba? That aside naga budurwar kache tazo kuna zance amma bata gaban ka kana planning auren wadda baka ma san sunan ta ba... Banza mahaukaci. Ka cika yaudara wallahi ", Ya karasa fada yana mai jan dogon tsaki..

"Look.... Naji kache sunan ta Maryam Amaal... A'ina ka santa?"

"Kai a'ina ka santa?"

"Student dina ce mana..."

"Ni kuma cousin dina ce... First cousin ma kuwa"

"Shikenan... Yaya Al-mustapha... In-law... Dan Allah kabani ita"

Al-mustapha ya daga kai ya sake hararar sa yana girgiza kai,

"Kacika kule kulen yammata"

"Wai waccen yarinyar nacacciya datayita kirana har yau na amince muka hadu? Maza wallahi bata gabana.. tun a Instagram take bibiyata kasan tsawon shekarun da take nace mun kuwa? Bamu taba haduwa ba sai yau shima gajiya nayi da nacaccen nacinta tacika stalking yau dai na ce sai dai tazo my hadu ni bazan samu zuwa ba.. tana ta roko na shine fa tazo..."

Al-mustapha ya taba baki yana yamutsa fuska,

"Ka yarda dani mana... Yauwa sannan tare suke ma da ita Maryam Amaal din"

"Kawarta ce ko?"

"No... Not really... Baby H din tace amaal kanwar kannenta ne da suke uba daya...yadda na lura kaman amaal din agidan su baby H din take a zaune ko? I dunno dai...cuz inata tanbayarta akan Amaal din taki bani amsa kaman basa good terms haka.. kasan mata one can't tell... "

Al-mustapha yayi shiru yana jujjuya sunan wai baby H...

"Wai Hindu?"

"Exactly... Amma dai da baby H na santa"

"Okay...."

"Kasanta?"

"Well... Yar uwata ce dai itama... Amma ba kaman yadda muke da amaal ba... Duka dai agidah daya ake under same roof.. Amma dai ita Hindu din itace ke agidan su Amaal din"

"Woah.... Amma ita meyasa take haka?

"Bangame take ba? Me kake nufi.. oho dai matsalar ku ce kai da ita... "

"Ni fa kade na hadani da ita wallahi bana son ta."

"Amma kai banza ne wallahi . Baka santafa kache.. akan wane dalilin tataso tazo har wajen ka?"

"Daya daga cikin abunda yasa bana son ta kenan ma... Batada kamun Kai... Kicewa saurayi ko'ina yake zaki zo ki same shi bakya jin fargaba? Na biyu kizo da wata iriyar shiga dake nuna tsiraicin ki awaje? Na uku tasaka wani seductive turare saura kadan nayi aika aika Allah yatemaka wallahi korarta fa nayi... Could you imagine.... Tana saka hannu tana wani tattaba ni... Tana macen? Ina martaba da kimar ta suke? Wai ahaka kake tunanin zan zabeta komai awaje ga Amaal dake killace jikinta da komai nata yarinya me nutsuwa da hankali? Kai nifa nayi mata wallahi.... Ka gayawa su Bappah zan aiko manya gaskia... Aurenta kawai nakeson yi ba sai an dau wani lokaci ba..

Al-mustapha ya mike bayan ya girgiza masa kai kawai,

"Meye haka muna magana?"

"Office zan tafi mana..."

"Magana mike fa akan Amaal kanwar ka . Da nake so da aure"

"An bada ita tuntuni...."

"Bangane ba...?"

"Ina nufin an bawa wani auren ta tun tuni..." Yana karasa bashi amsa yayi gaba abinsa

Habibi Talba yabi bayan sa yanata kiran sunan sa..

"Aboki na sai mun sake magana... " Al-mustapha ya fada yana mai bashi hannu sukayi musabaha

Wani malami da zai zarta su a shekaru yazo wucewa suka tsaya suna gaysawa...habjbi talba ya nuna Al-mustapha yana cewa da dayan malamin,

"Shine amini na da nake gaya maka fa... Architect Al-mustapha jalaludden........

...
_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
Chapter 28 · 0% Book details