← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 60

Sashe 4

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakomai Hayateey zama na na gyara." Tana daga idanun ta suka hada kallo yayi mata murmushi. Domin sarai ya jiyo abunda ta fada da ma tanbayar da mahaifiyar tata ta mata.

"To ai tsautsayi ne wannan yana iya jawa kan kowa. Banga lefin sa ba ga mai lefi, wannan yarinyar fa ita da gangan fa tana sani tatafi siyayyar shago itama. "

Alhaji Abubakhar yayi murmushi jin abunda amb junaid ya fada. Ya dan juya ya kalli amaal din,

"Itama yar wajen ka ce?

"Ta karshe ce ma..."

"Auta ce kenan?"

Amb. Junaid ya daga masa kafin yace,

"Eh auta ce..... Sunan Hajiya taci ai."

"Haba?"

"Allah kuwa."

"Ma shaa ALLAHU mai babban suna... Uwata ta kai na. Me ake kiran ki da shi?"

Cikin sanyayyar muryar ta mai sanyin da dadi ga duk wanda ya saurara. Ahankali a kuma nutse cike da tarbiya ga biyayya ga wanda kanta a kasa tace,

"Maryam... Amma Amaal ake kira na da shi ...."

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[7/20, 9:32 PM] Hafsaat💞: _*BAKON MUNAFIKI!!!*_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
_👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

__AREWABOOKS:MSSXOXO_
_WATTPAD:MISSXOXO00_

_005_

  _SHAFIN KARSHE NA KYAUTA/LAST FREE PAGE_
__

   °°°Hisham ya daga kai da sauri ya kalleta, Itama wannan karon shi din take kalla. Ba wanda ya janye idanun sa. Mamaki take ashe ba balarabe bane. Yayin da shi dinma hakan take a tasa zuciyar. Yana mamakin dama ba balarabiya bace?

"Gata nan kaman Hisham itama ita kadai ce awajen mahaifiyar ta."

"Allah sarki .. Allah ya raya mana su baki daya ya musu albarka."

"Allahumma Aameen." Cewar amb. Junajd ya sake muskutawa ya gyara zaman sa. Kafin ya cigaba da cewa,

"Ga Hadiza fa ... Ko ka sheda ta?"

"Kwarai kuwa nasan hadiza ba kanwar su labbo ba?"

"Tabbas itace.... Lalle baka da mantuwa, To ga yaranta nan Abubakhar daya ci sunan marigayi yaya?"

'kwarai Yaya. Allah ya gafarta masa."

"Amin Amin, Muna ce da shi sadeeq, Daga shi sai mai bjye masa wancen safwan, Sai Na'eelah da najwa ga sunan a jere."

"Sai kuma Hindu da baka fada ba. Saboda ita agola ce? Wallahi Alhaji ka sauya halin ka. A wajen bare ma sai an raba hali. Hindu dai ko ban aure ka ba ai idan da kara kai ma yar kace. Tunda ni da kai a duk tsatso daya muka fito. Wannan 'ya tace itama Hindu amman ba shine uban ta ba kamar yadda bai lissafo da ita ba. Mahaifin ta dan uwa ne agare mu ni da shi. Mahaifin ta shine babban cousin a family din kandemi" Cewar hadiza matar sa ta fari.

Tamkar kasa ta tsage ya fada haka yake ji... Kunya duk ta dabaibaye shi. Gashi ita datai maganar ko a jikin ta tacigaba da danna wayar hannun ta.

Parlorn yayi tsit kamar ruwa ya cinye su. Chan dai Alhaji Abubakhar yayi breaking silence din yace,

"Su kuma wadannan yan biyun fa ga sunan kamar su daya baa gane su.?"

Amb junaid ya juya ya jalle su yana murmushi. Kafin ya saka yatsa yayi nuni da haj jameelah yace,

"Ga kuma jameela. Itace mai daki na ta biyu bayan hadiza. Kamar yadda na gaya maka dazu. Amaal ce kawai Allah ya albarkance ta da ita... Itama sai bayan shekaru.."

"Haka... Allah ya raya su duka Amin."

"Amin amin... Sai mai dakina ta karshe... Ruwaida.. Gata nan. Itace mahaifiyar yan biyun da kake magana yanzu. Su kadai ne yaranta."

"Ma shaa ALLAHU... Allah yayi musu albarka ya raya su duka Amin.."

"Allahumma Ameen."

Ya sake daga robar ruwa ya kafa a baki ya sha bayan ya sauke dankarereriyar ajiyar zuciya yace,

"Hadiza, Jamila, Ruwaida...." Ya kira sunayen matan nasa daya bayan daya..

Dukkanin sh suka juya suna kallon sa. Suka kuma kasa kunne don jin abunda zai ce,

Ya saka yatsa yayi nuni da Alhaji Abubakhar yace,

"Wannan shine babban aboki na da nake gaya muku. Kai ya wuce aboki ma ya zama amini. Ya kere wasu da suke ganin su yan uwan na ne na jini. Ya mun abunda a duniya bazan taba mantawa da da tarin allhairinnsa agare ni ba."

"Kabar maganar nan Junaid... Haba mana kamar wasu yara sakarkaru."

"Kyale ni sai na fada... Amini na ne... Alhaji Abubakhar mai murmushin kudi'. Ko a wani hali kuka tsinci kanku a duniya da rai na ko bayan rai na, Ku kuma godewa Allah daya azurta ku da shi. Ku kira shi a ko'ina ne zai zo yayi bakin kokarin sa. Mutumi ne da yake adali, Mai dattako, cikar kamala, alheri, Mutunci, gaskiya, Amana da rikon ta, tausayi, kawaici, kauda kai, hakuri, da Imani ga biyayya, ga ladabi ga kamewa, ga temako... Alhaji Abubakhar mutumi ne da baya gajiyawa wanda yasan halacci ba kuma ya mantawa da alkhairi komai tarin sharrin da ka bishi da shi, Yayi da jikin sa yayi da aljihun sa ...zuwan mu zuwa Nigeria ko ince dawowar mu da dik wani zuwa hutu da duk wata tafiya Dr abubakhr ya dauke mun ita ni da iyali na da ahali na gaba daya free of charge muke shiga kasashe...Allah ya saka masa da alkhairi ya biya masa dukkanin wasu bukatn sa Amin... Ga matar sa nan kuna gani sunan ta Aisha.. Ga kuma dan su da Allah ya azurta su da shi Hisham shine matukin jirgin daya kawo mu man... Bugu da kari ma jirgin mahaifin sa ne gashi a zaune na Dr abubakhr ne..

"Duk wani Hisham da kuka gani na gidan mai hotel da sauran su duk na de abubakhar ne yayi masa laqabi da sunan dan sa Hisham, kamar su: Hisham airlines,Hisham travel and tours, Hisham palace,  Hisham showroom, Hisham plaza, Hisham oil and gas ltd, Al'Hisham international university., Hisham mart, Hisham luxury. Wadannan kadan kenan daga mallakin tarin kadarorin abubakhr. Babban oil mogul ne na kasar nan. Duk samda zamuzo Nigeria idan kukaga nasa an fita da motoci an musu full tanks to shine yasa lalle na'aika a dibamun mai kyauta... Kadan kenan daga cikin temammakin da yake yi ko ince ya saba yi ya ke kuma kan yi...Na roke ku da duk wanda yayi sallah ko yake addua ya dinga kamo sunan bawan Allah nan yana masa addua. Yana kuma rokon Allah daya kara kareshi ya azurta shi ya biya masa dukkanin bukatunnsa ya kuma yaye masa damuwar sa da lefukan sa. Allah ya saka masa da alkhairi ya jikan mabaifa."

Baki daya parlorn suka shiga amsa addu'oin amb junaid.

Haka dai suka karasa yar hirar dasike yi. Kafin akai su babban masaukin baki da aka tanadar acikin gidan dake dauke da komai na more rayuwar yau da kullum. Komai yaji babuce kawai babu agidan nan.

Amaal waje daya suke da mahaifiyar ta, daki ne yana kallon daki. Bayan tayi wanka a bandakin dake cikin dakinn ta zura babban hijabin dake ajiye akan sallaya ta zura kayan bacci aciki.

"Hayateey bara naje wajen Abbiey."

"Toh."

Fita tayi daga dakin ta nufi dakin da taga an shigar da akwatin mahaifin nata aciki.

Kwankwasa kofar tayi tana daga tsaye a bakin kofar ta waje,

"Shigo..." Ya amsa ta daga cikin dakin

Ta murda kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama.

Yana daga zaune akan wata kujera. Gaban sa kuma laptop ce yana aiki acikin ta. Daga kai yayi ya kalleta yana murmushi

"Hajiyata"

"Naam Abbiey... Barkan ka da dare"

"Barkan mu dai uwata ta kai na
"

Karasa shiga tayi. Ta zube daga dan nesa da shi tana mai aika gaisuwar ta agare shi chike da biyayya,

" Abbiey  barka da dare,"

"Me sunan yan gayu... Uwata tafi ta kowa."

Nan ma murmushin tayi. Tana mai hada yatsunta wajen lankwasa su cike da maduakakiyar kunya.

"Menene uwata ?"

Nan ma.shirun tayi tana murmushi.

Ya ajiye wayar sa da ke hannun sa yana nazartar ta sosai,

"Ina jin ki..."

"Abbiey dama... Dama ... "

"Ina jin ki Hajiya ta"

,"Dama zuwa nayi wajen ka na nemi gafara abisa lefin da nayi maka ,"

Ya danyi tattausan murmushi kawai yana girgiza kai,

"Uwata ai bata lefi...... Tashi kije na yafe miki duniya da lahira duk kuwa da ban rike ki da komai ba. Da lefin da kikai da lefukan baya da ki kai dama wadanda zaki agaba. Duka na yafe miki. Allah ya miki albarka..."

Murda kofar dakin akayi aka shigo. Hajiya hadiza ce. Tana tafe da kayanta samfarin riga da skirt da daurin ture kaga tsiya

Ta dubi Amaal shekeke tana yamutsa fuska,

"Hmm an turo ki ki kasa ki tsare kenan , Kai gaskia baki saar gyatuma ba. To kije ki gaya mata idan ta isa tazo nan ba wai ta turo ki ba. ... Tashi ki fita kema chan daya munafuka,"

"Meye haka hadiza?" Cewar amb. J. yana binta da kallon bata kyauta da abunda tayi ba.

"To ai gaskia ne. Naga ba kwanan ta bane. Na wane dalili ne zata turo yar ta kawai don ta zo ta h..."

"Ya isa haka Hadiza. Ba girman ki bane."

"To tashi ta fita. Ko na fadi abunda zai fi karfin sauraron ta wallahi."

Girgiza kai kawai yayi cike da takaicin ta dama kalaman ta marasa kan gado. Ya dubi Amaal dake tsakure duk ta dubibice tanata harde yan yatsunta na hannu yace da ita,

"Je ki ki kwanta uwata... Allah ya tashe mu lafiya. Ya kuma yafe mana baki daya Amin. Ki kwanta ki huta kinji ko?"

"Tohm abbiey."

"Ki saki ranki ki sawa zuciyar ki nutsuwa kinji? "

"Tohm abbiey." Ta bashi amsa tana kokarin murda kofar zata fita
Chapter 4 · 0% Book details